NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 259 of 323

nyi rashin kunya, ke fa uwar ɗakin mu ce". ta gyaɗa kanta kawai ba tare da tace komai ba, Hannatu ta ce,"jiya na zo ɗakin naki da daddare na tarar kin rufe ƙofa, kin manta ba ki faɗi abin da za'a dafa da safe ba, sai Sakina ta ce taji kamar kince a soya dankali da ƙwai". ta ce,"in dai zaku ci dankalin ku dafa kawai, amma karku sa da mu". Hannatu ta dinƙa kallonta, so take ta fahimci wani abu, don kwana biyun nan ma sai gulma suke na rashin saukowar da bata yi, shi ma kuma me gidan baya fita, in sun ga ya sauko to masallaci zai wuce, har Sakina na cewa ta rasa uwar da suke yi a saman sai su wani koma kamar matattu, in banda ranar nan ma da akai baƙi taga sun sauko, har Fillon ta yini a ƙasa, sai shi da yake saukowa daukar abincin da ake kawo masa ya koma, wanda hakan ke ƙona musu rai, ba su san me ake nufi da su ba, ba su taɓa yin girki sun ci ba sai dai su dafa suci au kaɗai. Tunanin Hannatu ya tsaya cak sanda taga Fillo ta fito daga store hannunta ɗauke creat na ƙwai, ta tafi da sauri zata karɓa Fillo ta hanata tana faɗin,"bar shi Hannatu, kici gaba da aikinki". ta ce,"ai Anty da kin bari munyi aikinmu, ke da ba ki jima da tashi daga rashin lafiya ba". Fillo tayi murmushi kawai bata ce ma ta komai ba, ta ajiye ƙwan ta koma ta ɗauko semovita, shi ma ta ajiye sannan ta nufi friedge ta buɗe ta ɗauko ingrediant ɗin da zata yi amfani da su, butter, shredded coconut, youghurt, lemon juice syrup da almond seed. su ma duk ta ajiye su wuri ɗaya kana ta buɗe drower ta ɗauko baking powder, sugar da veg oil. semolina Cake take so tayi, wanda larabawa suke cewa Basboussa, tana sonsa sosai, dan lokacin da suka je umara yawancin kullum sai taci, hakan ne ma yasa ta zage ta koya a wajen kukun da ke dafa musu abinci, kuma yau tana so tayi shi ko don Turaki yaci yaji daɗi, ya san ta iya girkin ƴan gayu itama, so take ya koma cin girkinta kawai, ta yanda ko gida yaje ba zai ci ba sai ya dawo zai ci na ta, ita bata son yake cin abin hannun kowa, nata kawai. duk ingredient ɗin ta haɗe wuri ɗaya, tasa mixer tai mixing sosai, ta ɗauko pan ta shafa butter ta juye kwaɓin kana ta yaryaɗa pealed almond seed, ta kunna oven tayi heating na ta for 1minutes sannan ta saka aciki in 180 degree. tana nata aikin Hannatu da Sakina suna yin na su, sai dai su na hira tare, musamman da taji su na hirar ƙauyen su Maijidda, ta dinƙa tambayarsa wasu wurare da ta sa ni lokacin da suka je suka kwana biyu acan. 30minutes na cika ta ciro Basboussa ɗin, ta nemi flask da zai riƙe zafinsa, tana tuna yanda Zaytun ke yi idan zata saka kayan baking acikin flask sai ta saka tissue saboda kar gumi ya jiƙa sama da ƙasansa. ta dafa herbal tea shi ma sai tashin ƙamshi yake yi, in 45minutes ta kammala haɗa break fast ɗin da take ganin idan Turaki yaci sai kunnensa ya kusa tsinkewa, har hango shi take yi tana murmushi, suka gama aikin kusan a tare da su Sakina, lokacin har 8 ta kusa, su ma ta basu Basboussa ɗin sukai ta godiya, sannan ta saka wani a ƙaramin bowl ta bawa Hannatu tace ta haɗa a breakfast ɗin Baba me gadi ta kai masa. babban tray ta ɗauka ta jera breakfast ɗin su ta wuce da shi upstairs, dan ba ma ta so su zauna cin abinci a parlo su Sakina su shigo, ita yanzu duk ji take yi da ma ba'a kawo ma ta su ba, da ma can ɗin da take yin murnar zuwansu zaman kaɗaici ne yasa, har da Bello ya tambayeta a kawo su tace masa ehh. akan table ta ajiye, ta kunna turaren wuta a ɗakin, ta ƙarasa bakin window ta haɗe cuttons da suka rabu hasken ya ratso ta ciki yana haske fuskar Turaki, ɗakin sai ya koma deep. bakin gadon ta zauna tana kallonsa, da alamu ko motsawa bai yi ba tun da ta fita, dan yacca ta fita ta bar shi haka yake, sai taji tausayinsa ya kamata, cikin kwana ukun nan raba dare yake yana aiki a computer, jiya ma ƙarfe goma na dare Bello da Khaleel suka zo suka ɗauke shi suka je company, sun sami matsala da wani companny na lemu da suka haɗa partnership da su, su na neman su yi musu asarar over 10millions, ga shi basu sanar da Baffa ba gaban kansu kawai suka yi, dan ya hana su haɗa hannun jari, ita ba ta san ma lokacin da ya dawo gidan ba, duk da har 12 tana zaune tana kallo a laptop ɗinsa da ya tafi ya bar ma ta. fasa tashinsa tayi, ta fita ta koma kitchen, ta buɗe drower ta ɗauko ƙaton plastic bucket, ta buɗe shi ta ɗebi garin ciki. garin kunu ne na haɗin su alkama da gyaɗa da sauransu, wanda yake gyara jiki yasa kumari, shekaranjiya da Nuratu matar Dr Yusuf suka zo ta kawo ma ta shi, ta ce ta dinƙa damawa tana sha safe da yamma, kuma babu ranar fashi, ta gargaɗeta akan karta kuskura tayi wasa da shansa yana da amfani sosai ajikinta, dan akwai wasu sinadarai ma da aka ƙara ma ta akai. tai murmushi da tuna tsiyar da suka dinƙa yi ma ta, wai in taci gaba da zama haka ƴar duma dumar amaryarsa na dawowa zai mance da ita, sai kuma suka shiga faɗa ma ta abubuwan da taji duk sunwa kanta girma, Nuratu har da cewa tace ya siya ma ta waya domin akwai zafafan abubu
🏠