sallamar cike da kewar junansu.
ta riƙe wayar a hannunta tana ta kallon hotonta, so take alallai sai ta tuna ranar da yay hoton, iyakar fuskarta ne kawai da wuyan balle idan taga kayan jikin nata ta iya tuna ranar.
but kan gadon yay ma ta kama da ɗakinsa na can gida, its like kamar ma ranar da ta kwana a ɗakinsa ne.
a hankali ta juyar da kanta tana kallonsa, zatonta ko bai bacci ba, sai taga yana sauke numfashi alamu ma ya jima da yin baccin. hannu ta miƙa ta ajiye wayar a inda taga ya ɗauko, sannan ta kwanta tana barin tazarar 4inches a tsakaninsu, taji ta kasa rufe ido tayi bacci, taji kamar tana buƙatar wani abu daga gare shi, ganin da alama yay nisa a baccin ta sami damar ƙarewa kyakykyawar fuskarsa kallo, tana jin wani abu me kama da sonsa tsantsa na taɓa zuciyarta.
laɓɓanta suka tale da wani kyakykyawan murmushi, abu ɗaya ta sani yanzu shi ne tana sonsa, idan tace ba haka ba tayi ƙarya, and ta yaudari kanta, but ba zata iya cewa ga rana ko kuma lokacin da ta fara sonsa ba, idan har ma ta faɗi hakan to tayi ƙarya.
kallon fuskarsa kawai take yi tana jin tamkar kar ta daina, tamkar yay ta baccin ita kuma tai ta kallonsa babu ƙifcen ido, ta tuna wata rana, ranar da ta fara tambayar Maijidda, _kin san wani Turaki a gidan nan?._, kuma amsar da Maijiddan ta fara ba ta ita ce,_ wani kyakkyawa ne ajin farko, in kyawun kowa na fasaltuwa nasa ba zai fasaltu ba, don ko kyau da kansa yay ƙaryar yace zai iya faɗin kyan Turaki._
amsar da Maijiddan ta bata kenan, kuma haka kawai sai taji haushin maganar a yanzu, wanda ta san ba komai ba ne face kishi, sai ta yamutsa fuska tana ɓata ranta, haka kawai duk ya bari kowa ya gama kalle kyansa ita an bar ma ta saura.
ta rufe ido tana so ta sami sassaucin zafin da taji zuciyarta nayi ma ta, kafin ta buɗe ƙwayar idonta ta sauka akan gashin kansa, baƙi wuluk da shi, kwantacce kamar na larabawa, cikin ɗan hasken ɗakin sai sheƙi yake yi, sai taji tana sha'awar ta taɓa taji kalar sulɓinsa, ta ɗaga hannunta a hankali zata taɓa sai ta fasa, gudun kar taje ta taɓa ya buɗe ido ya kamata.
ta mayar da kallonta kan pink lips ɗinsa, ƴan daidai da su masu ɗaukar hankali, a iya kallon kawai ta shaida masu taushi ne.
ta rufe ido ta kai yatsanta ta taɓo lips ɗin a hankali, tana taɓawa tayi saurin ɗaukewa tana rufe fuskarta kamar wadda ya kamata tana taɓawar.
sai da ta ɗauki kusan 3mints idonta a rufe, tana jin kamar ta kuma taɓawa taita shafawa lips ɗin, tana buɗe idon kallonta na sauka akan ƙirjinsa da ya wadatu da kwantacciyar gargasa me kyan naɗewa.
sai taji tana buƙatar ta taɓata itama, tayi nisa a kallon chest ɗinsa, ba tayi aune ba taji muryarsa yana faɗin,"you want to hug me right?".
ba ta san lokacin da ta waro idanu waje ba, ta kalle shi tai saurin kulle ido tana ɓoye fuska ajikin pillo, yay murmushi yasa hannu ya matso da ita kusa da shi a kunnenta ya ce,"stop being shy, hug me the way you want, i am all yours".
ta tura baki tana jin kamar tayi kuka tsabagen kunya, ya sa hannunta a bayansa but ta kasa rungume shi ɗin duk da tana so tayi hakan, sai kawai ya ƙara matso da ita sosai ya ɗora kansa saman shoulde ɗinta, in a cool voice yace,"lets sleep".
ta ce,"ai bana jin baccin".
"but yo want to touch this right?". ya faɗa yana kamo hannunta ya ɗora akan ƙirjinsa, da sauri ta rumtse idonta jin wani abu ya ratso tun daga babban yatsanta har tsakiyar kanta.
"oya ki ta shafawa baccin zai zo, or should i bring cumb kiyi masa kitso?".
zata juya masa baya ya hana hakan, sai ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa, har yay bacci bata yi ba, sai da yay nisa sosai sannan ta shiga wasa da gashin ƙirjin nasa tana kuma shafa lips ɗinsa.
*After 3Days.*
ƙarfe shida da rabi a lokacin, Fillo ta sauko daga upstairs, english wears ne a jikinta, riga white sai skirt baby pink, sai hular chantaly itama pink colour, tayi kyau sosai acikin shigar.
ta dubi parlon taga an gyara shi sai ƙyalli yake yi, duk da cewar da ma ba wai da datti yake ba, but ko ya wuri dai ya samu gyara kyau yake ƙara yi.
wucewa tayi ta kunna burner ta zuba turaren wuta, nan da nan kuwa parlon ya karaɗe da ƙamshi, ta kunna tv tasa karatun ƙur'ani sannan ta wuce kitchen, tana tafiya kamar ba zata taka ba.
yau da kanta take so tayi girki, kullum sai dai yasa Zaytuna ta dafa ta kawo musu, ta san akwai gajiyawa kawai dan ma dai ya haɗu da ƙanwa me biyayya ne, and kamar yanda ba zai iya cin abincin ƴan aiki ba haka ita bata tunanin zata barsa ci, ba ma ta fatan Allah ya kawo ranar da zai ci abincinsu.
a kitchen ɗin ta sami Hannatu na feraye dankali, ta amsa gaisuwar da take yi ma ta da murmushi. "har kun tashi da wuri haka?, sannunku da aiki".
Hannatu ta amsa ma ta da yauwa tana barin ferayar ta miƙe,"Anty akwai wani abu ne?".
Fillo tayi ma ta wani kallo ta ce,"ni kam wai ba zaku bar faɗa min wannan sunan ba?".
Hannatu ta ce,"ai Anty sai dai kiyi haƙuri gaskiya, amma ba zamu iya faɗin sunanki ba gatsal, ai in muka yi haka mu