NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 257 of 323

tayi shiru bai yi magana ba, jin shirunsa yasa ta juyowa tana kallonsa ta ce,"Allah na iya girki". ya rufe ido ya buɗe ya ce,"ai tun kina ƙarama kika ce". tai saurin cewa,"a'a nufina tun ina ƴar ƙarama nake yi, ko time ɗin ma da muna masarauta ina yi". "ohhh yanzu kenan ke babba ce?". kamar jiran tambayar take yi ta ɗaga masa kai, murmushinsa me sauti ya fito yana cewa,"to ni ban ga girman ba, you are still a Baby in my eyes, dan haka ni ba zan ci abinci ƴar ƙarama ba babu daɗi, rabi ya dahu rabi bai dahu ba, ko yay ta ƙauri, ko a cika gishiri". su ka haɗa ido ta haɗe gira waje ɗaya ta murguɗa masa baki, yasa yatsa ya ɗalle bakin nata. "oya ba rigima na ce ba, abincin za'a ci, buɗe bakin". saboda yunwar da take ji ta buɗe bakin tana karɓa, sai da ya gama bata sannan ya matso kusa da ita sosai, ya ce shi ma ta ba shi hannunsa ya gaji zai karye, yay ta narke ma ta yana koma ma ta ƙaramin yaro, da taƙi ya ta shi zai bar wajen yana cewa ya fasa kira ma ta Ummi ɗin, babu shiri ta ɗauka plate ta kamo hannunsa ya dawo ya zauna ta shiga ba shi, kuma yaƙi yarda ta ba shi da spoon dole sai hannu ta saka, duk kaiwa ɗaya sai ya cije hannun nata, har ta gama ba shi bata yarda sun haɗa ido ba kanta na ƙasa, sai dai tana ta murmushin da ta rasa dalilinsa. duk yanda Fillo ta cije ta noƙe akan ba zata bi shi toilet ba sai da yaja ta suka tafi tare, da kansa yay ma ta brush, sannan shi ma yay nasa, su ka fito yana ɗauke da ita rungume ajikinsa, ita kuma tayi laƙwas ta lafe a jikin nasa kamar mage, ya wuce yay switching light off sannan ya kunna deem light, tukunna ya wuce kan gadon, ita dai duk sai kunyarsa take ji. ko a kan gadon ma a jikinsa ya kwantar da ita, murya can ƙasa ya ce,"Fulani nah". ta ce,"uhmm". ya shafo gashin kanta da yake jin laushinsa da santsinsa na shiga jikinsa ya ce,"mu bari sai Allah ya kaimu gobe sai a kira Ummi ko?". ta girgiza kai da sauri,"a'a yanzu dai". "to ai dare yayi, kar tayi tsammanin wani abu ne ya faru". kamar zata yi kuka ta ce,"ni dai don Allah yanzu". ya sauke numfashi ya ɗauko wayarsa ya bata, ta miƙe daga jikinsa tana cewa,"remove the password". looking at her eyes da suka koma sexy ya ce,"your name". ta tsaya kallonsa kafin ta ce,"Halima?". ya girgiza kai,"no, the other one". "Fillo?". nan ma girgiza ma ta kai yay, ta shagwaɓe ta ce,"to which one?". daidai kunnenta ya ce,"cry cry Baby". fuska a tsuke zata yi magana yasa hannu ya rufe bakin, ita kuma taƙi saka sunan da ya faɗa, ai ta san bata kai wannan matsayin ba, dan haka sai ta saka sunayensa duka biyun bai yi ba, ta sa na Mum da na Maama duk bai yi ba, tasa na Zaytun shi ma bai yi ba, da ga ƙarshe kawai tasa yanda ya faɗa ma ta ɗin shi ma ta ga bai yi ba, tana sa Fulani Nah taga ya buɗe, kuma da tsantsar mamaki sai taga hotonta akan wallpeper, hoton da ba ta san da shi ba, kuma ba ta san lokacin da ya ɗauke shi ba, dan bacci take yi ya ɗauka, mutum dai in yana bacci muni yake yi amma ita kanta ta san tayi kyau, sai kawai fuskarta ta washe da murmushin da ya bayyana haƙoranta. ta kalle shi ta ga idanuwansa a rufe kamar ya yi bacci, a hankali ta ce,"ai ban san lambar Ummin ba". ya buɗe idonsa da bacci ya fara fizgarsa ya ce,"Ummi nah". yana faɗa ya mayar da idonsa ya rufe, kamar kuwa yanda ya faɗa ɗin gaban Ummi sai da ya faɗi da taga shigowar kiran, ta ɗaga wayar tana karawa a kunnenta cike da jin nauyi na sirikinta da kuma fargabar abin da zata ji, duk da cewa duk bayan kwana biyu yana kiranta su gaisa, but ba'a irin wannan lokacin ba, ta ƙara duba agogo taga ƙarfe goma har da ƴan mintuna. "Ummina". "na'am Autata". Ummin ta amsa tana sauke numfashi, sai yanzu taji ta samu natsuwa. da murna sosai haɗe da farin cikin jin muryar mahaifiyartata ta ce,"Ummi nayi kewar ki sosai". "ni ma haka Autata, ya kuke?, ina fatan duk kuna lafiya?". sai kawai Fillo ta saka kuka tana faɗa ma ta ita dai tana so ta ganta, haka Ummin tai ta fama da ita tana lallashinta, sun jima su na wayar, dan hira sosai suka yi, har Kaka ma sai da suka gaisa da ita, tace akai wa Dada su gaisa, Ummi ta ce ai tayi bacci yanzu. "Ummi to yaushe za ki zo?". ta ce,"yau kwananki nawa Autata?, ko 2weeks fa ba ki yi ba, ki bari sai an kwana biyu zan zo in ganku kinji, hope babu wata matsala ko?". ta girgiza kanta kamar tana ganinta ta ce,"to Ummi ba za ki dawo nan ɗin ba?". ta ce ma ta,"su Dada sun hana, muna nan sun riƙe mu ni da Dadana, an bar mana ɓangaren Kakarki, ba ki ga ba an gyara mana shi sosai yayi kyau, har ƙaton enlargement ma akayi mana aka kafe a parlon, da hotona da na Abbanku da naki da na Hamid, duka aka haɗa yayi kyau sosai". Fillo ta sauke numfashi tana jin soyayyar Umminta da kuma kewar Abbanta ta ce,"Ummi ina zuwa zan ɗauke shi Allah". Ummi ta ce,"ba zan bari ki ɗaukar min nawa ba, sai dai ki roƙi Hamid ya ba ki nasa, shi ma ya saka a ɗakinsu". da haka suka ci gaba da wayar har sai wajen sha ɗaya saura sannan suka yi sallama, sukai
🏠