a bar wajen ya isa gado ya ɗauko babban kwalban humra ya jiye a saman mirriow ɗin, tafin hannunsa a saman haɓarta ya juyo da fuskarta yana ma ta nuni da kan gado ya ce,"your dress".
sai kawai ta bi kayan da ido kafin ta gyaɗa masa kai, ba tare da ce komai ba, kuma ba tare da ta kalle shi ba.
tana kallonsa ya fice daga ɗakin jiki a saɓule kamar mara lafiya ko wanda aka yo aiken mutuwa, duk sai taji kamar yana neman bata tausayi, ko me akayi masa oho?.
sai da ya fita sannan ta iya ɗaukar man ta shafa, tana mita ƙasa-ƙasa ta ɗauki humrar ta shafa, kawai yaje ya ɗauko mata sabuwa alhalin ga buɗaɗɗu nan har guda uku a ajiye, tana gama shafawa ta wuce kan gado, tunaninta ɗaya pant da pad, kuma da mamakinta tana ɗaga kayan sai ga pad ɗin haɗe da sabon pant, wata uwar kunya ta lulluɓeta, yaushe ma ya san tana period ɗin?.
tana murguɗa baki ta shiga toilet ta saka, garin ɗauko brezier ɗinta ta zame ta faɗa cikin bathtube ɗin ta jiƙe, ta rumtse ido kawai ta fito bayan ta shanya, cikin sauri ta ɗauki kayan ta saka gudun kar ya dawo.
tana saka rigar taji kamar ta kurma ihu, ya san kuwa kayan da ya ɗauko ma ta?, ita kam bata jin zata iya saka kayan nan alhalin yana nan, duk rigar tayi transparent, kuma iyakar gwiwarta fa, hannun ma irin na vest, kuma ma ko ya haɗo ma ta da brezier, sai kawai ta doki ƙafafu a ƙasa da ƙarfi kamar tiles ɗin sun ma ta laifi.
ƙofa ta nufa zata fita sai dai tana zuwa taji ƙofar a rufe ya saka key ta waje, ta cije leɓen ƙasa ta juya ta koma toilet ɗin, ta ɗauko brezier ɗin sai dai ba zata saku ba don sosai ta jiƙe.
fitowa tayi tana hawaye, gado ta nufa ta durƙushe a wajen ta kifa kai tana kuka, can jimawa taji an buɗe ƙofar, bata ko ɗago ba dan ita haushinsa take ji, shi ma kuma da ya shigo ɗin kallo ɗaya yay ma ta ya ɗauke kansa, ya wuce ya ajiye basket ɗin abincin dake hannunsa, ya fito da cooler ɗin ciki ya ajiye akan table.
bakin gadon ya dawo ya zauna, ya ɗagota ya ɗaurata saman cinyarsa tare da zagayeta da hannayensa ya ce,"kukan na menene?, me Fulanin Turaki ke so?".
ta ɗago da kanta, tana matse idanu tamkar baby ƴar 2years ta ce,"ni ɗakina zan tafi".
ɗan murmushi ya yi yace,"naji to za ki koma can ɗin but tare zamu tafi ko?".
tai saurin girgiza masa kai, ya ƙara cewa,"why?".
"to ai kaima ga naka, kowa ya zauna a nasa ai".
ya buɗe ido yana kallonta sosai kafin ya kwantar da kansa a kafaɗarta yana shaƙar ƙamshin humrar da ke fita a jikinta.
da wani irin murya yace,"to ni yau tsoro nake ji, ba zan iya kwana ni ɗaya ba, in kin yarda na bi ki ɗakinki, na yarda ko a ƙasa ne zan yi shimfiɗa, but please karki tafi ki barni ni ɗaya bana so wani abun yazo ya kamani, ba zan iya ƙwatar kaina ba".
Fillo ta dinƙa kallonsa kafin ta ce,"kai ne ɗin kake jin tsoro?".
ba tare da ya ɗago kansa dake kafaɗarta ba ya ɗaga ma ta kai kawai. sai kawai ta tsinci kanta da kama hannunsa ta ce,"to amma jiyan nan ai kaine ka kori abun da yake biyo ni".
"to ai jiya kika ce, yau indai yazo to sai dai ya cinyemu dukanmu, kuma da ma jiyan ma ai ƙarfin hali nayi na zama jarumi saboda bana so wani abu ya taɓa ki".
tayi shiru ba ta ce masa komai ba, ya ɗago kansa ya kalleta ya ce,"shikenan ma kawai, zan tafi gidan su Bello".
ta kalle shi suka haɗa ido ta girgiza masa kai da sauri, sai kuma ta sauke idonta ƙasa tana jan yatsunta.
"ai dare yayi yanzu".
hannu yasa ya ɗago haɓarta ya ce,"look in to my eyes".
sam taƙi sai ma ido da ta daɗa rumtsewa. idanuwansa na neman lumshewa ya zura hannunsa cikin rigarta, tana jin hannunsa a ciki tayi saurin buɗe ido ta zabura zata miƙe ya riƙeta, flat tommy ɗinta ya shiga shafawa yana faɗin,"na san wannan shafaffan cikin na buƙatar abinci ko?".
magana yake yi duk yay wani collapse.
ta ɗaga rigar ta fito da hannunsa tana cewa,"ni ka bari".
yay knooding ma ta kansa, ɗaukarta yay zuwa kan kujera ya ajiyeta, ya buɗe cooler ɗin abincin, nan da nan ɗakin ya karaɗe da ƙamshin ƙwai. ta bisa da kallo a sanda yake ɗauko plate ya zuba soyayyar doya da ƙwai da kuma miyar souse, bayan ya gama zubawa ya juyo ya fuskanceta, da hannunsa ya ɗauki doyan ya kai bakinta.
"wa ye ya dafa abincin?". taji bakinta ya suɓece da yi masa tambayar.
"Zaytun nasa ta kawo mana, i know ba ki da lafiya, and ba ki iya girki ba, so na roƙeta alfarmar take dafa abinci tana kawo mana before na kai ki catering school ki koya".
ta tsuke fuska tana kallonsa ta ce,"ni ce ban iya girki ba?, wancan ranar da na dafa indomie ai kace na iya dafawa".
ya ce,"amma ai bance yayi daɗi ba ko?".
ta turo baki gaba ta kauda fuska gefe,"Allah na iya girki nima, kuma ka tambayi Maama kaji, Baffa ma da yaci wainar masar da nayi sai da yace yayi daɗi Allah yay min albarka, Adda Zaytuna ma indai zata yi baƙo in tana asibiti tana sawa nayi ma ta, kuma ka tambayi abokinka ɗin kaji, kuma ma ka tambayi Kaka kaji tun ina ƴar ƙarama nake yin girki".
ya dinƙa kallon bakinta yana murmushi, har