NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 254 of 323

y wasa da rayuwarta haka?, duk yacca ta ke ɓoyewa da ma sai da hakan ya bayyana ta wani ɓangaren bata sani ba, sai ta tura baki gaba zata kau da fuska yay saurin saka hannu ya tare hakan, ya marairace yana kama kunnensa ɗaya kamar a ɗazu ya ce,"am so sorry ƴar lelen gidan su Zaytun, ki ce kin haƙura kar Hajiyoyin gidan Alƙali su ƙara min tsinin goshi da remote". daga ita har shi murmushi suke son yi but kowanne sai ya cije, ta kai yatsanta kan goshinsa tana shafa ƙullutun wajen da bai baje ba har yanzu, sai kawai ta ƙyalƙyale da dariya, wanda hakan shi ma ya sa shi dariya, yana kama hancinta yaja. "kayi sabon ido a goshi". yasa haƙori ya ciji hancinta,"zan rama ne akanki". sai kuma ya kwanta itama ya kwantar da ita a jikinsa yace,"shikenan mun shirya?, an daina kukan?, an daina min tsiwa an daina share ni?, an mayar da aurena?". ba tayi magana ba kawai ta ɗaga masa gira, yace,"thank you". ya faɗa yana shafa sajenta ita kuma tana so ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa. bakinsa a saitin kunnenta yace,"to sai yaushe kuma". a hankali ta ce,"what?". ta faɗa yana jin saukar ɗumin iskar bakinta akan ƙirjinsa, wanda ya nemi ya haifar masa da kasala, jin yay shiru ta ƙara tambayarsa, sai ya sosa gefen fuskarsa yana faɗin,"just forget, not now". ya mirgina yana riƙe da ita a jiki yace,"ke yanzu da na baki takarda kawai sai kika ɗauketa as divorce paper?". kunya ta kamata ta ce,"to ai na ɗauka idan aka bawa mace farar takarda sakinta aka yi". yana wasa da hancinta ya ce,"tunda kin ɗauka ai sai ki sauke...oya bani labarin kukan da ki kai tayi, duk da na san rabi kukan shagwaɓa ne, to sauran rabin na mene?, na son Turaki da kishinsa ko na mene?". tasa tafin hannu ta rufe masa baki da ido, sannan ta ce,"i want sleep". ya sauke hannun da yake kan idonsa sannan ya ɗora nasa hannun akan nata da ke bakinsa yace,"its after 4 babu kyau baccin yamma". ta shagwaɓe tana cewa,"ɗan kaɗan zanyi". bai ce komai ba ya ɗora kanta a ƙirjinsa, take kuma bacci ya ɗauketa, da kukanta da baccinta su na ba shi mamaki, abu ne da duk basa yi ma ta wahala, ita dai shekarun ne kawai da ita but komai da take yi na ƴan 4-5years ne. ya kamo hannun da ke da ciwo zai warware bandage ɗin sai yaji ta motsa, hakan yasa ya ƙyale yaci gaba da looking at her innocent cute face. *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *51* sai da aka fara kiran sallar magriba tukunna Turaki ya iya zame Fillo daga jikinsa, sanin cewa ba sallah zata yi ba kawai yaja blanket ya rufeta, yay kissing forehead nata sannan ya fita, yana zuwa ɗakinsa yay alwala ya wuce masallaci. a masallaci ya zauna har sai da akayi sallar isha'i tukunna ya dawo, for the first dawowarsa gida bai wuce ɗakinsa ba kai tsaye, bedroom ɗin Fillo ya wuce, yana shiga ya tarar har yanzu bacci take yi, ya girgiza kansa yana mamakin irin baccinta. durƙusawa yayi a gaban gadon yana yaye blanket ɗin ya kamo hannunta, ɗayan kuma yana shafa fuskarta sai kallonta yake yana murmushi, fuskar baccin nata kaɗai ya isa ya shaida maka rigimammiya ce, haɗe gefen fuskarsa da tata yayi, ya lumshe idonsa for some minutes ya buɗe, yasa hannu yana jan hancinta yace,"Fulani nah baccin ya isa haka". ta buɗe idonta a hankali, cikin baccin da yake cinta ta dube shi ta mayar da murfin idon ta rufe tana juya masa baya. murmushi yay ya miƙe tare da hawa gadon ya cicciɓeta ya fita da ita zuwa ɗakinsa. direta yay a ƙasa yana kama hannayenta ya ɗaga sama, sak irin yacca akewa ƙanan yara idan za'a tashe su, ta buɗe lumsassun idanuwanta ta kalle shi tana sakin kukan shagwaɓa,"ni fa bacci nake ji". ya rumgumeta yana kwaikwayon muryarta shi ma yace,"ni kuma i want you to wake up, kin barni ni ɗaya i feel lonely, ki tashi ko rigima ce muyi". haka yay ta damunta har sai da ta wartsake tukunna ya ƙyaleta, ya kama hannunta suka isa wajen gado, ya zauna a gefe yana ƙoƙarin ɗorata a saman cinyarsa sai taƙi, taƙi zaman becose she is not feeling comportable saboda period ɗin da take ciki, tana jin ma kamar tayi staining. "mene amfanin ƙafafun nawa idan ba ki zauna akai ba?". ta ɗan kauda fuska tace,"ɗaki zanje". yaja hannunta har sai da ta juyo ta kalle shi yace,"nan ba ɗaki ba ne?". "to ai toilet zan shiga". ya miƙe tsaye yana faɗin,"nan ma ai akwai toilet ɗin, muje let me escort you". ya faɗa yana kama hannunta zuwa toilet, sai ta maƙale a bayansa taƙi shiga, ya janyota zuwa gabansa yana kallonta, ta kifa kai akan cikinsa tana cewa,"ni toilet ɗina ba wannan ba, ina so zanyi wanka". ya ce,"nan ma ai ana wankan". tasa taɓara,"ni ba wannan ba to, nawa zanje please leave me". ta faɗa tana ta maƙalewa a bayansa, bai kulata ba ya buɗe toilet ɗin suka shiga ciki duk da faman tirjewan da take yi, tana kallo ya kunna ruwa a bathtube har sai da ya cika sannan ya dawo da idonsa kanta, su na haɗa ido ta ɓoye fuska a bayansa, ya juyo da fuskartata yana cewa,"kiyi wankan anan". sai ta shiga dukan ƙafafu a ƙasa cike da kukan shagwaɓ
🏠