NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 252 of 323

ta baya, taji yana waya yana cewa,"oak gani nan, ki ajiye ki wuce, na bawa Samha saƙonki". ta ɗago kanta lokacin da yake sakkowa akan gadon yana barin ɗakin, ta bi bayansa da kallo, after few minutes sai ga shi ya dawo ɗauke da basket ɗin abinci, ya wuce ya ɗora akan table, sannan ya zauna akan kujera ya shiga zuba abincin da ke cikin flask, duk tana kallonsa yadda yake yi tamkar bai san da halittarta a ɗakin ba, ita kuma tana yi ana yana shareta shi yake daɗa tunzurata, hakan na ɓata ranta, har ya kammala cin abincin bayan ya tsarga masa ya taso ya dawo kan gadon, yay kwanciyarsa kamar mai bacci. can yaji ta riƙo hannunsa, ya juyo yana kallonta, ta kifa goshinta akan hannun nasa, hawayen idonta ya sauka akan fatarsa, ɗumin hawayen ya wuce ta cikin jijiyoyinsa har zuwa ƙirjinsa, tausayinta ya wanzu a zuciyarsa, gaba ɗaya jikinsa sai yay sanyi, Allah ma ya sa ni yana tsananin tausayinta, basarwa kawai yake yi, ko shi da yake namiji ba ya jin zai iya ɗaukar 2days bai ji muryar Mum da Maama ba, balle har akai ga kwanaki tara, ai sai rashin lafiya ta kama shi. but sai ya ƙara ɗauke kansa akanta, ya tamke murya ya doka ma ta tsawa yace ta fitar masa a ɗaki, ta miƙe jiki a sanyaye kamar wacca ƙwai ya fashewa a ciki ta fita, kai tsaye ƙasa ta koma wajen su Yami fuskarta duk caɓe caɓe da hawaye, sai da taje ta tarar su har sun wuce, sai ta dawo ta koma ɗaki ta rufo ƙofa, ta hau gado taci gaba da kukan gado. sai bayan fitarta Turaki yaji gaba ɗaya bai kyauta da abin da yay ma ta ba, ko babu komai mahaifiyarta take ta roƙon ya kira ma ta, duk sai yaji ransa babu daɗi, kasa daurewa yayi ya ta shi ya bi bayanta, a dunƙule ya ganta a tsakiyar gado, ya girgiza kai ya ƙarasa ya hau kan gadon gaba ɗaya. ya ɗagota zuwa jikinsa ya kewaye yana ɗora haɓarsa a saman kanta, yasa hannu yana goge ma ta hawayen fuskarta, ya shiga hura ma ta iska a kunne yana faɗin,"cry cry Baby what the cry for umm?". cikin kukan ta ce,"ba kai ba ne". ya ce,"OMG! laifin me nayi da har ya sa kike kuka?". tana motsi a jikinsa kamar zata shige jikinsa gaba ɗaya ta ce,"ba kai bane sai kake yi min tsawa bayan ka san bana so". yaja dogon numfashi ya sauke sannan yace,"to ai kece Fulani nah ba kya ji, duk yanda na so nai controlling anger na akanki sai kinja na ɗaga miki murya, phone ɗina fa kika fasa min da abubuwa masu muhimmanci a cikinta, but shikenan daga yau insha'Allah ba zan ƙara ba in dai tsawa ce". ya faɗa yana ɗago kanta daga ƙirjinsa ya ɗora goshinsa akan nata, ya hura iska a idonta suka lumshe yace,"shikenan?". kamar jiran tambayar takeyi ta girgiza masa kai da sauri tana cewa,"a'a". ya buɗe ido yana kallonta da shirin jin abin da yake tsammani, but sai yaji saɓanin haka. "ka bani haƙurin kukan da kake ta saka ni to, har ma da ciwon da kaji min". ba shiri ya tsura mata ido yana kallonta, sai yau ya ƙara ganin yarinyartarta ta fito sosai, ya ƙara tabbatar da muguwar rigimammiya ce, bakinsa yaƙi rufuwa da murshin da yake me haɗe da mamakin halin rigimarta. tana buɗe ido suka sarƙe a nasa, sai kawai ta tsuke fuska ta kai masa duka a ƙirji tana mayar da kanta ta kwantar, ya shafo gashinta yana cewa,"ni ne zan baki haƙuri ko da wani daban kike?". "kai ne mana, ai kaine kaji min ciwo, kuma kake min tsawa, kuma kake sa ni kuka, kuma kake share ni". ya ƙara ɗago kanta yana kallonta ya ce,"duk ni ɗaya!, to yanzu tsakani da Allah baki ji kunyar cewa in baki haƙuri?, ke fa kika fasa min waya me tsada, ni bance ki ban haƙuri ba sai ke". ta zumɓura baki ta ce,"to ai kaine ka janyo na fasa ban sa ni ba". "ni kuma?". ta ɗaga masa kai kawai. "to da nayi mene na janyo?, sharri kika fara?". sai kawai ta ƙura masa ido, kukan da ya tsaya ya dawo sabo, ya kwanto kanta jikinsa yana faɗin,"subhanallah!, ni kam naga ta kaina, Fulani wai me yasa kuka ba ya miki wahala?, wallahi Allah bana son hawayenki its hurts me alots amma kinƙi ganewa. kin ga ni dai yanzu mu bar ma zancen in dai kuka za kiyi, kin min laifi na miki laifi kowa ya rama anyi 1-1, yanzu dai mu shirya don ranar yau ba zata wuce ba sai anyi sulhu". ta kamo gaban rigarsa ta riƙe har sai da maɓallin ya cire, a hankali tace,"ni ba zan shirya da kai ba sai ka bani haƙuri". ya shafo wuyansa ya ce,"ya zanyi, bada haƙuri ai ba zai sa na ragu da komai ba, kiyi haƙuri". ta ɗauke hannunsa daga bayanta ta ɗago tana kallonsa, a shagwaɓe ta ce,"ba'a haka ba". sai ya lanƙwasar da kai yana kwaikwayon shagwaɓarta ya ce,"to a ya ya?". "ka kama kunnenka sai ka sakko ƙasa ka tsuguna". ganin bai da niyyar yi yasa ta juya masa baya tana faɗin,"to kayi tafiyanka kawai". ta faɗa tana sakin kuka kaɗan. wannan kukan ya sa shi saukowa ƙasa ya durƙusa, ya kama kunnensa da hannu ɗaya sannan ya kamo ɗayan hannunta ya ce,"to look at me mana". ko da ta juyo ta gan shi sai ya kusa bata dariya ganinsa ya koma kamar ɗan yaro. ya sarƙe yatsunsu wuri ɗaya wanda hakan yasa ta jin wani abu ya tsarga ma ta, shi
🏠