NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 251 of 323

ika yi wasa. ke idan ma ita ba ta dawo ba ga ƴan aiki nan an ajiye miki cikakkakun ƴan mata masu buɗaɗɗan ido, inda rabon sun ƙwace miki miji sun barki da sakakken baki ne ke kika jiyo, dan wallahi ni ban wani yarda da ƴan aikin nan ba, son samu ma duk ki saita musu hanya kiyi aikinki ke ɗaya, mene abin wahala anan, haka kawai ƴan aikin yanzu da suke ƙwace maka miji". ita dai Fillo jinta kawai take bata ce mta komai ba, tun sakkowarsu Yami ke bin su da kallo har suka ƙaraso suka zauna kan kujera, Fillo ta sauko ta gaishe da Yami, ita dai Yami sai kallonta take yi cike da nazari da son gano wani abu, kuma cikin hikima ta iyaye manya ta fahimci abin da yake faruwa ba tare da ko ta tambayi Fillo ɗin ba, ai kuwa nan da nan Yami ta shiga yi ma ta nasiha sosai, da ƙara koya ma ta dabarun riƙe miji gam a tafin hannu, ita dai Fillo ji kawai take yi, don ba ta tunanin zata aiki ko da abu guda indai akan Turaki ne. lokaci ɗaya Fillo ta sake, su Yami su ka ɗebe ma ta kewar da take ciki, hira sosai kamar sun shekara ba su haɗu ba, tana ta zumuɗin za ta ji muryar Ummi ta tambayi Yami wayarta tace ai ta lalace, ɗoki da murnar da take ciki duk sai taji sun gushe, har la'asar su Yami su na nan ba su tafi ba. su na cikin kallo Turaki ya shigo, ita ta fara kai kallonta kansa, haka kawai sai taji gabanta ya faɗi, tayi saurin ɗauke idonta a kansa ganin wani kallo da ya yi ma ta fuskarsa a tamke. ya shigo ya zo ya gaida Yami, suka gaisa sosai tana sanya masa albarka tare da yi musu adu'a sannan ya wuce sama. bayan tafiyarsa Yami ta kalli Fillo ta ce da ita,"ban ji kin yi masa sannu da zuwa ba, ba ki tashi kin karɓi jakar hannunsa ba, duk lafiya?". ta turo baki gaba tana faman ɓata fuska, ai kuwa Yami ta shiga yi ma ta faɗa sosai kamar zata duketa. "ta shi ki bi bayan mijinki". murya a kumbure ta ce,"ai sai kun tafi zanje Yami". tai maganar alamarta na shaida ko sun tafi ɗin ba zuwa zata yi ba. Yami ta taso mata da faɗan da yafi na ɗazu, ba shiri ta miƙe kamar zata yi kuka ta wuce sama fuuu, tana hawa ta shige ɗakinta, sai kuma taji kamar Yami zata hawo saman, hakan yasa tai saurin fitowa ta wuce ɗakinsa. ta buɗe ƙofar ta shiga babu ko sallama, ta nemi bakin ƙofa ta maƙale tana jan yatsu sai kace munafuka, Turaki ya buɗe idanuwansa da ke rufe ya bi ta da kallo, ƙwayar idonsa kawai za ka kalla kasan akwai abin da ke damunsa, akwai abin da yake buƙata sosai, ta ɗago ido karaf suka haɗa ido da shi, sai ta saurin juya masa baya, ya miƙe zaune da ga kishingiɗen da yake ya ce,"is there anything?". ta juyo tana turo ba ki gaba cike da zallar yarinta tace masa,"Yami ce ta ce na biyo bayan ka". babu shiri murmushi me kama da dariya ya suɓuce a leɓensa, sai ya tallafi haɓa yana kallonta kawai, ganin hakan yasa ta ɗan duki ƙafafu a ƙasa ta ce,"ce tayi ka kira min Ummi a waya". sai ya ɓata fuska ya mayar da kansa jikin pillow yace,"ba ki faɗa ma ta kin tarwatsa wayar ba?". kamar zata yi kuka ta ce,"ai na faɗa maka bana sa ne". "to sai ki jira sai kin gyaro sai kiyi kiran". kawai sai ta saka kuka tana faɗin,"to wayan naka ai ba guda ɗaya ba ne, dan Allah ka bani in kira Ummina, yau kwanana 9 banji muryarta ba fa". ya galla ma ta harara, banda tana kuka tsab sai tayi dariya saboda yacca idanunsa suka yi a hararar, ta ƙara dukan ƙafafu a ƙasa da shagwaɓa sosai tace,"don Allah ka ba ni kaji, to ni ka bani lambar sai inje wajen Baba me gadi ya ara min tasa". ya kasa ɗauke ido akanta, sai yaji tana cewa,"kuma kai fa kace za ka zame min kamar Abba nah". sai ya sauke numfashi ya ce,"zo ki ɗauka". ta taho kamar wadda ta yiwa ƙasa laifi, tana zuwa bakin gadon taga duka wayoyi biyun akan bedside locker har ma da keypad, tana kallon wacca ta fasa ta gane ta, kenan an gyara ma shi ne yake ta yi ma ta ciwon baki, ta ɗan waigo kaɗan ta kalle shi taga hankalinsa bai kanta, sai ta kai hannu zata ɗauki wayar, caraf taji ya riƙo hannunta ya janyota jikinsa ya zaunar da ita kan ƙafafunsa da ke tankwashe. "da kika fasa ai ba ki iya ba da haƙuri ba, shi ne saboda rashin kunya yanzu an gyara za ki zo ki ɗauka, to ba ni sai kije can wajen me gadi ya ara miki". ta shiga kokawar ƙwace hannunta tana faɗin,"to ai kaine kace in zo in ɗauka". "ehh ai ƙarshen rashin kunyarki zan gani kuma na gani, ba ni wayata ba zan bayar ba, kije shi me gadin ya ara miki tunda dama wajensa kike zuwa aron abu". ta ce,"to ka ban lambar". kawai ya fizge wayarsa sannan ya ɗauketa da ga kan ƙafar tasa ya dire a ƙasa, yasa wayoyinsa a aljihu yay shigewarsa toilet, after 3 minutes ya fito yana goge hannu da ƙaramin towel, mamaki yasa shi tsayawa yana kallon Fillo da ke durƙushe ta kifa kai akan gadon tana kuka bilhaƙƙi, yau rana ɗaya da ya tambayi kansa shin hawaye basa ƙarewa ne?, ko da yake in su na ƙarewa ai da tuni ya sami salama da wannan kukan, ya girgiza kai ya koma toilet ya mayar da towel ɗin sannan ya fito. ya dawo ya koma kan gadon yay kwanciyarsa ya juya ma
🏠