Fillo damar ‘kara fashewa da wani matsanancin kuka cike da shagwab’a da iya shege gami da zallar wawta.
Sakina dai na laɓe bakin ƙofa ta kasa kai da kunne, ta rufe baki tana fito da idanu waje.
Maijidda tayi saurin kai hannu ta janyo Fillo jikinta, da tsantsar kulawa da damuwa irin ta ƴan'uwantaka take fad’in,“wai don Allah me aka yi maki?, don Allah ki sanar da ni meye wai ni don Allah?”.
Da k’yar Fullo ta bud’e baki ta fara magana, leb’en sama da na k’asa su na had’uwa su na faman luguden kuka,“wai wai ni fisabilillah haka kawai..”.
Maijidda ta zabura tana k’ara fad’in, “wai Ke me?, don Allah ki min bayani inji?, kin san kuwa duk yanda gabana ke faɗuwa?".
“to wai ba Turaki ba ne haka kawai shi kullum ya gagara ya fahimce ni sam, sai yay ta faman ji da kansa, kullum sai yay ta ƙin kula ni yana share ni, ko kallona ma ba yayi, sai dai fa yay ta hararata, kuma idan nayi magana sai yay ta min tsawa yana ɗaga hannu zai mareni, ni sai yay ta min abu kamar ba mijina ba, da ma sai da na faɗa muku ba ya so na, ni kawai gida zan koma, ki kira min Ummi a waya please".
kukanta ya ƙaru a san da take ƙarasa maganar.
damuwa ta bayyana fal a fuskar Maijidda, cikin sanyin jiki da murya ta ce da ita,"kuma kina yi masa biyayya?, kina sauke duk hakkinsa da ke kanki?, kuma ba laifi kika yi masa ba?".
tasa hannu tana goge hawayenta ta ce,"ai ni bana kula shi ma".
Maijidda ta ware ido,"ba kya me?, kwatakwata ba kya kula shi kike nu fi ko kuwa da ku ka yi faɗan ne?, ni ban gane rashin kulawar ba".
"ni kawai ba na kula shi ai baya so na?".
Maijidda ta raɗa ma ta abu a kunne, Fillo ta ɗago daga jikinta tana faman ɓata rai,"ni nace miki komai ma bana kula shi, sai jiya ma na fara ganinsa a gidan, ni dan Allah ki kira min Ummi a waya azo a tafi da ni".
"Allah me girma da ɗaukaka, yau ina ganin iya shege, da ma Fillo har haka kika kai ba kiyi hankali ba?, mijin naki za ki ce sai jiya kika gansa bayan sati guda da aure?, kuna cikin gida ɗayan?, to wa kika barwa shi?, ɗaya matar tasa ko kuma ƴan aikin?".
kuka ya ƙara zuwar ma ta,"to ai shi ne baya zuwa inda nake, kuma da yazo sai ya fara min tsawa alhalin ya san bana so".
Maijidda ta ce,"tabɗijam, to wallah sai yau na tabbatar da ke ɗin nan dai ba ki da wayo sam, a iya ɗauke asiri kawai kika fi wayo. yarinya Allah ya tausaya miki ya ba ki miji kamar Turaki, mijin kece raini, mijin wuce sa'a, amma ki gantalar da shi da lamarinsa saboda shegen taurin kai da miskilanci irin naki. to ai ni dai a iya nasiha da faɗan da naji an miki ba'a ce sai ya zo inda kike tukunna za ki saurare shi ba, kuma ba'a ce lallai sai ya zo inda kike ba sannan kema za ki je inda yake, yo to da ma wanne miji ne zai kula matarsa alhalin ita ba ta kula shi?, da kike batun ma ba ya sonki, ai ko jikina duka kunnuwa ba zan yarda da wannan zancen ba, dan idan ba ya sonki babu abin da zai sa ya aureki, don billahi irin waɗannan mazan masu aji da ilimi ya ratsasu ta ko'ina ba sa auren macen da basa so, haba Fillo ki yiwa bawan Allahn nan adalci mana, wannan mutumin dai zuciyarsa babu mugun nufi ballantana kice saboda ya wulaƙantaki ya aureki, kuma da ma akan mene ba zai ke shareki ba, shariya ma ai dole dan wallah me iyawa da halinki sai me kai zuciya nesa, in wani ɗan wiwin ma kika aura Allah da tuni kin sha kutufo, to da yake ma kin samu wuri ne shiyasa kike abin da kika ga da ma. kuma idan gidan za ki tafi da gaske ai haɗa kaya za kiyi kibi hanya ba sai kin kira waya anzo an tafi da ke ba".
sai kuma ta kwantar da murya ta shiga ba wa Fillo shawarwari masu kyau a matsayinta na aminiya kuma ƴar'uwa, tare da ƴan nasihohi wanda ta san idan har ta ɗauka tayi amfani da su ba zata yi danasani ba.
kusan minti biyar sannan ta miƙe tana cewa,"wanko fuskarki tare da Yami muke, saura idan munje kiyi wawtar gaya ma ta abin da kika faɗa min, dan naga kamar hankali ya bar jikinki, wallahi kici uban faɗa in ta kama ma a haɗa miki har da duka, ki ce ma ta kawai ba ki da lafiya, in ya so ma ai tsammanin ciki kika ɗauka da wuri haka". ta ƙarashe maganar cike da tsokana tana ƴar dariya, Fillo ta harareta ta nufi toilet, ita dai dariya take tana ƙara faɗin,"Allah kina cewa ba ki da lafiya abin da za'a fara tunani kenan, nan kuwa ba'a san ko shimfiɗa baku taɓa haɗawa ba, balle ayi me kankat".
su na sakkowa da ga step Maijidda na ƙara faɗin,"ni dai gaskiya nake faɗa miki kuma shawara nake baki, ki ajiye shegen taurin kanki da tsinannan miskilanci a gefe ki kama mijinki, billahillazi tsiwa da rashin mutunci ba naki ba ne a gidan nan, ki nutsu ki yiwa kanki karatun ta natsu, in kuwa ba haka ba na rantse da Allah sai kin yi kukan da yaci uwar wanda kike yi, sarai kin san dai ba ke ɗaya ba ce, matarsa na dawowa zai jefa ki a kwandon shara, ya mance da ke da batunki, ba kowanne kalar iskanci namiji ke ɗauka ba a wajen mace komin son da yake yi ma ta kuwa, yanda kishiyarki take wayayyiya sai ki zama ke da bola ɗaya acikin gidan nan in k