NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 25 of 323

tsinke masa, kuma before he notice anything stearing ya ƙwace daga hannunsa, kamin ganinsa ya ɗauke gaba ɗaya yana tunawa da motarsa ce ɗaya akan titin sai farar motar da ta duki tashi ya ƙarasa gangarawa bakin bishiya, wanda sanadin buguwar kansa da glass kenan kuma sai farkawa yay ya gansa a hospital. Fatansa ɗaya Allah yasa motar da ta buge shi mutanen ciki basu sami matsala ba, saboda ba laifinsu ba ne, shine wajen yayi ƙoƙarin kama stearing ya shiga gaban motar ita kuma tayi saurin kaucewa. Amma Maama ta dage kan motar na sa ne ta hankaɗa shi. yamma liƙis Boɗejo ta shigo parlon, babu kowa a parlon, tai tsaki ta nufi hanyar stairs tana mita. Akan wanne dalili ne ma su duka zasu yashe su wani haura sama after all sun san hawa saman wahala yake yi ma ta. Ƙofar bedroom nasa a buɗe yake, daga bakin ƙofar ta tsaya tana kallon ikon Allah, sai kace wani gwal ko tauraro, yana zaune kan gado sun wani baibaye shi, basu san da zuwanta bama sai da ta shiga ta zauna kan stool ɗin dake fuskantarsa. tace,"wai baka ji sauƙi ba ne har yanzu?, mutum sai kace mace". murmushi yayi bai ce mata komai ba. ta ɗan harare shi tace,"ashe an kwance maka ƙaton rawanin?". Samha tace,"rawani kuma?". tace,"ehh ko za kice min ba haka bane, wadda ba zan faɗi ra'ayina ba sai dai nata". Samha tace,"yo ni wani abu nace Boɗejo, gyara ne fa kawai nake miki...idan wani yaji sai yay zaton rawanin sarauta kike nufi, alhalin ba haka bane...mene haɗin bandage da rawani fisabilillah?". Boɗejo tace,"to banga damar cewa bandage ɗin ba...ina ce ba dake nake maganata ba". Samha bata ce komai ba, Turaki yace,"wai babu wani maganin da akeyi ne irin wannan ciwon ya warke kusa?". Boɗejo tace,"lokacin da muka sameka a asibiti rai a hannun Allah ban bada shawara ba ne?, kaje ka tambayi ita Madinar, sai da nace a kira Waziri ya saka maka hannu a gocewar ƙashin nan sai ce tai inaa ita ba haka ba, gwara asibiti suyi hoto su gano matsalar, yo ni kuwa me zan ƙara cewa wanda ya wuce nayi shiru tunda bani na haifa ba". Turaki yay shiru, ta ƙara cewa,"ƙarafun da asibitin suka danneka da su ba suyi tasiri ba ne da kake neman wani magani na daban?". Yace,"sunyi mana, naji sauƙi fa kawai dai ba yanda ya kamata ba...kafaɗar ce bana iya motsata". tace,"ba sauƙin kenan, ni ai sai dai nace Allah baka lafiya, amma ba dai bada shawarar inda ya kamata akai ka a sama maka lafiya ba, ko kuma maganin da zaka sha...tunda ita Madinar ta ɗauki dukkan yardarta ta ɗora akan bature, yo bature ko gaibu". Zaytuna tace,"Boɗejo asibiti ai ba gaibu bane, yama fi saurin taimakawa lalura". Boɗejo tace,"to ko na asibitin ko na gidan duk wanda akayi ni dai fatana Allah ya ba shi lafiya". Sai kuma ta kalli Turaki tace,"yo kai me ka yiwa mutane suke neman rayuwarka?, gaka dai da kyan hali kuma ni ban san dalili ba, Muhammadu ka faɗa min gaskiya ko dai kana aikata wani mugun abun a ɓoye bamu sa ni ba?". Ya ɗago ido ya kalleta zai yi magana Hajiya Madina ta shigo ɗakin, acikin wayar dake kare a kunnenta cikin tsawa tace,"just do as i said! thats all, i don't want that your blabaring". ta ƙarasa bedside drower ta zauna tana dire wayar da ta katse a gefen Turaki, tasa hannu ta ɗan matsa kafaɗar Turakin, yay saurin rumtse ido tare da yin,"ashhhh". Ya faɗa cikin dauriyar zafin ciwon da yaji. "still dai?". ta tambaya. Shi kuma ya ɗaga ma ta kai. Hajiya Madina tace da Boɗejo,"babu wani mugun abu da yake aikatawa, gaskiyarsa ce tayi yawa, saboda yaƙi bada haɗin kai akan wani cuta da mutanen dake son haɗa partner ship da company nasu, bcox hakan zai jawa company ɗin asara babba. shine yasa suke so su kashe shi dan samun biyan buƙatarsu". Baki buɗe Boɗejo ke sauraronta, tana yin shiru tace,"yo ina dalili anan, wallahi sai ya bar musu aikinsu babu dole, dama kai ka ɗorawa kanka ba ce akayi dan kayi karatu dole kaci ribarsa ba, an tara an ajiye muku, ba ku kaɗai ba har ƴan gabanku, to mene kuma na cewar sai anyi aiki a ƙarƙashin wani?, ina su waye masu bibiyar rayuwar taka?". "Boɗejo ai zar...". Hajiya Madina ta dakar da shi daga abunda zai ce. tace da Boɗejo,"zasu shigo hannu ne tunda ƴan sanda na kan bincikensu". Boɗejon tace,"dole ma a binciko ko su waye, dan babu wanda zai yi kasadar shiga rayuwar jinin Sarki Sulaiman Dukko bai fuskanci tsatstsauran hukunci ba...ɗan babban alƙali kuma jikan sarki, a nemi aga bayanka sannan a zuba ido, hakan ba mai yiwuwa bane...aiki kuma ka barshi har gaban abadan". Hajiya Madina tace,"abunda nace nima kenan, to matsalar yana jin sauƙi abinda ya faɗawa uban akai za'a zauna". Baɗejo ta muskuta tace,"ina ce ai na isa ko?, to bari Dukkon ya dawo ya sameni...wallahi sai dai idan bana numfashi amma wannan aiki dai ba zaka koma shi ba, can suje su ƙarata da duk irin asaran da zasu yi, ai ma'aikatar bata ubanka bace balle asarar ta shafeka". Hajiya Madina ta jinjina da kai da jin daɗin hukuncin Boɗejon. sai dai jin sabon furucinta sh
🏠