rki, kamar fa zai kawo min duka, babu wani irin taushi girmamawa ta ɗan adam acikin muryarsa".
sai kuma ta taɓe baki,"ni da ma na faɗa miki tun ranar da muka zo na san ba zaman lafiya ake a gidan nan ba, ba ki ga ita kanta kamar ba ta da miji ba, sai dai ta sauko tayi kallo taci abinci ita ɗaya ta koma, tabɗijam ni kuwa dai duk kuɗin namiji wallahi ba zan yarda da rashin mutuncinsa ba, ke ni ba zan ma yarda da wani auren dole ba, ba zan iya namiji ya takani ba gaskiya".
"ke ma dai Sakina ai da ma da gani ba auren soyayya akai ba, ni itace ma ta ke bani tausayi tun da naji ance tayi aiki a gidansu, wataƙila ƙarfi aka nuna musu aka aura ma ta shi dan anga ba su da hali, ni tausayi ma take bani kina kallonta kin san bata jin daɗin zaman, ko da yake babu komai zamu ɗaurata a hanya, naga ba ta da girman kai za ta sake da mu, zamu ba ta shawarwarin da zata saita mishi zama".
Sakina ta nufi cooker gas tana faɗin,"ke yanzu dai buɗe firinjin nan ki ɗauko mana kazar nan da naji ta ɗan fara yami, mu gyara muci abarmu in ba haka ba a banza za'a barta ta lalace, naga matar gidan ba wani wayewa tayi da cin kayan daɗi ba, duk gata nan a ƙanjame ai. Allah na tuba ni ina da wannan uban kayan daɗin ma me zai sa in damu da takaicin ɗa namiji, ai ɗaukarka zanyi in bawa banza ajiyarka, kai ita ma dai wallahi anyi lusara, ko da yake wasu sun ɗaukaki soyayyar namiji fiye da jin daɗi, kuma kin san Allah duk yanda akayi ganinta ƙashi da rai yasa yake ma ta wulaƙanci, babu gaba babu baya kyace me cutar S, kai Allah dai mun gode maka, kuma banza da ita ma kawai ta jefa shi a kwandon shawara ta bawa jikinta ingantattun kayan da zasu farfaɗo da ita, ba dai gidan jin daɗi da hutu ta zo ba, wallah wata guda yay ma ta yawa ta murmure".
Hannatu tai ƴar dariya tana fito da gasashshiyar kaza a freezer,"Sakina ko dai ko dai, kawai...".
bata ƙarasa ba Sakina ta juyo tana yi ma ta wani kallo,"ko me?, ni da wannan miskilin mijin?, ba dariya ba murmushi babu fara'a?, azaba!, Allah ya kiyaye wallahi, ai ranar farko zan bakawa gidan nan wuta dan ba zan iya da mugun halinsa ba, dukanta fa yake yi".
Hannatu ta riƙe baki,"kai don manzon Allah?".
"mtswww ke sai shegiyar gulma ba kya sa ido a abu, jiya baki ganta tana kuka ba?, to da daddare ma lokacin da ya shigo na hau saman ina jinsa a ɗakinta yana zazzaga ma ta masifa ita kuma sai kuka takeyi, ke Allah yasa ma ba sakinta yay ba dan naga yau gaba ɗaya fa ba ta sakko ba".
Hannatu tayi dariya,"wallahi yana sakinta zan shiga da ga ciki, wa ye zai so rabuwa da wannan gidan da aka aje daula, aljannar duniya, ita ma ɗin dai shashasha ce kawai, ni fa yana burge ni sosai saboda yana da kyau kamar ka sace shi ka gudu, kuma da yardar Allah sai ya zama rabona". ta faɗa tana jujjuyawa,"kalle ni fa da kyau, kissar ƴan aiki zanyi kawai a wuce wurin".
buɗar bakin Sakina za ta yi magana suka ji sallama a parlo, da sauri suka fita a tare, ganin Yami yasa suka ƙarasa da sauri su na yi ma ta sannu da zuwa, Yami na yi musu fara'a ta amsa musu, ta zauna akan kujera tana tambayarsu ya aiki.
"ina matar gidan fa?". Yami ta tambaye su.
Sakina ta yi saurin cewa,"bari a hau a kirawota yau ba ta sakko ba gaba ɗaya, ƙila ba ta tashi ba".
Maijidda ta cire hijab ɗinta ta ajiye tana cewa,"ƙyale ta bari na hau na sakko da ita".
ta faɗa tana nufar upstairs, kuma duk da haka Sakina sai da ta bi ta saboda taje ta yo munafurci.
“Aa lafiya dai?” Maijidda ta tambaya lokacin da take ɗora ƙafafunta akan steps.
Sakina ta ɗan sosa gefen fuskarta ta ce,“Aa da ma wai...”. dakatar da ita Maijidda ta yi kana ta ce,“Aa Kika ce bata sakko ba ko, na ce miki to zan je na gani ko lafiya, ina ga ai babu kuma buƙatar sai kin biyo baya na ko kuwa?. Kije kiyi aikin gaban ki”.
Haka kawai ta tsinci kanta da fad’a mata wad’annan maganganun ba tare da sanin dalili ba.
but still sai da Sakina ta bi ta ɗin bayan ta haye, kuma tana hawa ɗakin Turaki ta buɗe a hankali ta shiga, tai tsaye daga bakin ƙofa tana yi masa kallon tsab, ganin kan gadon ba'a gyare ba yasa ta riƙe baki tana jijjiga kai, ko me ta saƙa a ranta oho, da sauri kuma ta fito tana barin wajen ta nu fi ɗakin Fillo.
Maijidda kuwa tana isa ta ga ƙofar d’akin Fillo a bud’e, bata yi mamaki ba sanin cewar Turakin baya nan, kai tsaye ta saka kanta ciki d’auke da sallama. Bata ji alamun za'a amsa ma ta ba don haka kawai ta kutsa kanta ciki, a karo na biyu ta ƙara yin sallama saboda son ta samu izini kamar yadda Manzon Allah (SAW) yay mana umarni da mu yi.
Sai da tayi sallama uku babu amsa hakan ya sa ta ƙarasa ciki tana kuma ƙara yin sallama, rufe bakinta ke da wuya sai ta jiyo kamar shesshek’ar kuka, hakan ya bata damar yin sauri ta isa bakin gadon tana fad’in,“hasbunallah wa ni’imal wakil, na shiga uku ni Hauwa, Ke! Meye ka faruwa meye damuwan?, Wani ya mutu bani da labari ne?.”.
kawai sai itama ta fashe da kukan, da ma itama gwanar hawaye kamar Fillon, ganin hakan Kuwa ya ba ma