NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 248 of 323

hi zata yi magana sai ta fasa ganin irin kallon da yake watsa ma ta, tai saurin hayewa ta ƙudundune a tsakiya, yace,"matsa can". ta matsa inda ya nuna ma ta, sannan shi ma ya hau ya kwanta bayan ya kunna karatun alƙur'ani. yana kwanciya yaji ta kamo hannunsa ta riƙe, ya ce,"what?". ta ce,"don Allah ka barni a haka". "to yi bacci kar in ƙara jin motsinki". ta ce,"to". har tsawon wani lokaci yaji alamun dai ta kasa baccin, kawai tayi shiru ne kamar tana baccin, zai zare hannunsa a nata tayi mugun firgita ta ƙwalla ƙara tana yowa kansa gaba ɗaya. yay saurin tattarota jikinsa ya kewayeta da duka hannunsa yana cewa,"shhhh ba ihu ba adu'a za kiyi kinji". ya ƙara maimaitawa,"kin ji". ta fizgi numfashi ta ce,"wani abu ne yake bin jikina yana kuka". ya ɗora hannunsa a gashin kanta yace,"ta ina kike jinsa?". a hankali ta ce,"a ƙafata". ya miƙa hannu ya daɗa ƙaro hasken lamp, ya ɗaga blanket ɗin yana bin ƙafarta da kallo, yau da yaga duka ƙafarta a zahiri sai yaji ya tsorata da irin sirantarta, ya sauke numfashi yana tunanin anya ba sai ya kaita anyi ma ta general check up ba kuwa?, shi idan ma ana ƙara nama a jikin mutum tsab zai kashe ko nawa ne a saka mata, sirantar tayi yawa sosai. ya sunyo da kansa yana kallon fuskartata, ta rumtse idanuwanta gam kamar ko ance ta buɗe ba zata buɗe ba. a hankali in a cool voice ya ce,"za ki ci abinci?". ta ce,"a'a". ya hurar da iska a bakinsa ya ce,"cikin ya daina ciwon?". ta ɗaga masa kawai. ya ƙara cewa,"me kike so yanzu?". ta ce,"babu komai". "har yanzu kina jin motsin abun?". ta girgiza ma sa kai kawai tana ƙara ƙanƙame shi. a kunnenta ya ce,"ki yita ayatul kursiyyu". ta ce,"ina yi". "to yi bacci". ta knodding kanta kawai. ya girgiza kansa yana jin tsananin tausayinta, a hankali yaji ta sauke numfashi hakan ya shaida masa tayi bacci, sai ya kwantar da ita kusa da shi sosai, duk yanda ya so ya zare hannunsa daga riƙon da tayi masa ya rasa yanda zai yi, saboda ba ya so yay ƙwaƙwƙwaran motsin da zata farka. kuma baccin da bai iya yi ba kenan, yay tayi ma ta karatu a cikin kunneta, har aka kira sallar asuba, sai lokacin ya zareta daga jikinsa ya rufeta gaba ɗaya ya shiga toilet yay alwala, sai da ya yi raka'atanul fajr sannan ya wuce masallaci bayan yasa key ya rufeta a ɗakin. *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Kar mu manta da karanta suratul kahf tare da yawaita salatin manzon Allah(SAW), a cikin wannan rana me albarka ta juma'a🙏🏽. Allah ya sadamu da alkhairan da ke cikinta._ *50* sai ƙarfe goma sha ɗaya Turaki ya farka da ga baccin bayan asuba da ya kwanta, lokacin da ya tashi bai ga Fullo a ɗakin ba, bai yi mamaki ba ya san da ma tsoro ya kawota, ba don haka ba ya san ba zata taɓa zuwa ba. yana kunna wayarsa ya ci karo da messege ɗin Sectery na sa, da yake tuna masa appointment din da yake da shi da wani company na lemu by 3pm. saukowa yayi akan gadon ya shiga toilet yayi wanka, bayan ya fito ya shirya cikin shigar manyan kaya na kufta black colour da tayi masa masifar kyau. yana cikin fesa turare yaji cikinsa yayi ƙugi sosai alamar yunwa, dan daren jiya ma bai ci komai ba, yay gajeran tsaki na ƙorafi da takaici, ga shi da aure amma bai da matar da zata dafa masa abincin da zai ci, shin wai sai yaushe zai san yayi aure ne?, when zai fara jin wannan daɗin da ake cewa akwai shi a gidan aure?, wannan farin cikin sai yaushe?, ga shi ta bakin Bello da gaske rainon Fillo zai yi, rainon da baya jin cewar zai iya, ya ƙara yin tsaki yana dire perfume da ke hannunsa, yanzu ba abin yaje gida ba da sunan zai ci abinci a fara yi masa tambayar ƙwaƙwaf. jakar laptop ɗin sa ya ɗauka ya fita a room ɗin, daidai bakin ƙofar room ɗin Fillo ya tsaya, ƙofar a buɗe take, ya tsaya yana tunanin ya shiga ko kar ya shiga, a ƙarshe zuciyarsa ta yanke masa yay tafiyarsa kawai, tun da har ta iya barin ɗakin nasa taji sauƙi kenan. yana saukowa parlo ƴan aiki suka fito da sauri da ga kitchen, suka durƙusa suka gaida shi, hannu ya ɗaga musu ba tare da ya amsa da fatar baki ba, har ya kai bakin ƙofa idonsa ya sauka akan dining, flask ne guda biyu a ajiye sai na tea flask, ya kalli Sakina da ba ta koma kitchen ɗin ba ya ce,"ta sakko ne?". kanta a ƙasa ta ce,"a'a ranka ya daɗe bata sakko ba kwatakwata". yay ɗan jimm sai kuma ya ce,"ita tace kuke yin girki?". ta ce,"a'a ranka ya daɗe, mun ga dai hakan na cikin aikin mu ne". ƙaramin tsaki kawai ya yi ya zuge glass ya fi ce, Sakina ta bi shi da kallo tana riƙe haɓa da jinjina kai. Hannatu na ganinta ta ce,"lafiya?, me kika guntso?". "uhmm ke wannan me gidan bai da sauƙi ko kaɗan, babu ma alamar mutunci a tare da shi, ni da ma tun ranar farko naji bai yi min ba sam, gaskiya matarsa na haƙuri da shi, irin mazan nan masu shegen girman kai da izza, fuska gaba ɗaya babu annuri". Hannatu ta ce,"wani abu kika gani hala". tayi maganar da irin suffa ta ƙwanƙwararrun munafukai. "ke kin ji yacca yake tambayar wa ya saka mu yin gi
🏠