NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 247 of 323

bai ko ce ma ta ƙala ba ya kashe wayar kawai. tafiyar Zaytuna babu jimawa ya fito a ɗakinsa ya tafi ɗakin Fillo, fitila ya kunna ya hangeta kan gado, yanayin yacca tayi kwanciyar kaɗai zai shaida maka kwanciya ce ta wahala, dan hatta yanda numfashinta ke fita ma ba ta daɗi ba ne, hasken fitilar yasa ta yin juyi tana sa hannu ta kare idonta duk cikin baccin, lura da hakan ya sa ya kashe light ɗin ɗakin ya kunna ta wayarsa, ya mayar da ƙofa ya rufe sannan ya ƙarasa ciki, a bakin gadon ya zauna ya kai hannu ya taɓa wuyanta da kanta yaji still jikinta da zafi. wayarsa ya ɗauko ya kira Zaytuna, ta ɗaga tana sallama da alama ma ta fara bacci, yace da ita,"zazzaɓin bai sauka ba fa". ta ce,"da ma akwai zazzaɓi ne Hammah?". bai amsa ma ta ba kawai yaja tsaki ya kashe wayar, ya haska torch ɗin wayarsa ya ɗauko ledar maganin ɗazu yaga bata sha ba, ya zazzage ledar ya ɓallo adadin yacca zata sha, ya zuba ruwa a cup sannan ya ɗago Fillo zuwa jikinsa, ba tare da yay magana ba ko ya tasheta ya kafa cup ɗin a bakinta ya zuba ruwa sannan ya tusa ma ta drugs ɗin duka, ya ƙara zuba ruwa tare da toshe hancinta, take drugs da ruwan suka wuce maƙogoronta. tsabagen baccin na cin sosai buɗe ido kawai tayi ta mayar ta rufe tana gyara kanta a ƙirjinsa, ajiye cup ɗin ruwan yay tare da mayar da ita ya kwantar, yasa hannunsa ciki nata mara ciwon ya haɗe da nasa, yay ta kallonta wucewar wasu ɗaƙiƙu tukunna ya buɗe blanket ya rufeta, yana me kamo ɗayan hannun dake da ciwo, ya kalli ciwon ya kalli fuskarta, ya tuna jiya haɗe da yin ɗan guntun tsakin da shi ɗaya ya san dalilin yinsa. ya ƙara ɗaukar waya ya kira Zaytuna, sai da ya kira sau uku sannan ta ɗaga, lokacin bacci yaci ƙarfinta sosai, dan kamar zata yi kuka ta ambaci sunansa. ya ce,"wannan ciwon na ta when suka ce za'a kunce?". ta ce,"Hammah ai ba da ni aka je hospital ɗin ba". sai ya hauta da faɗa yana cewa,"kuma ke ba ki san yanda za'ai masa ba za ki ce wani ba da ke aka je ba. mene amfanin karatun da kika yi?, ko haka kike yiwa patients ɗin da su ke asibiti?". faɗan ya fara hawan ma ta kai ta tari numfashinsa,"a bar shi ya ƙara kwana biyu tukunna". yaja tsaki yace,"ki fita ki bawa me gadi first aid". yana faɗa ya kashe waya ba tare da yace komai ba, ya fita da ga ɗakin cikin sauri, zuwansa gidan yay daidai ya isowar Zaytuna bakin gate ɗin sai tangaɗin bacci take yi. kusan fizgar firstaid ɗin yay daga hannun na ta ya juya ya tafi bai ko tanka mata ba, abun da bata taɓa yi masa ba kawai ta harari bayansa ta koma sai masifa takeyi. yana komawa ya tarar Fillo har ta tashi ta shiga toilet, zama yay bakin gadon yana jiran fitowarta, can sai ga ta ta fito tana jan ƙafa ɗaya, ya bita da kallo ta ƙasan ido, ita kuma ganinsa sai tai saurin juyawa zata koma toilet ɗin saboda rigar da ke jikinta, ƙafafunta tun daga gwiwa duk a waje, ga shi babu brazier a jikinta kuma ana hango shatin breast ɗinta. muryarsa a sama yace,"wallahi kika koma sai naji miki ciwon da yafi na jiya". cak ta tsaya ta manne a jikin bangon tana sakin kuka, ya taso ransa a ɓace ya figeta suka wuce, yana kallonta fuska ɗaure ya ce,"ban hannunki". za ta tsaya gardama ya bige hannunta daga kan fuskarta da take goge hawaye, ya kamo me ciwon ya shiga warware bandage ɗin, ya jawo stool ya zauna ya shiga ƙara dressing ciwon. tana kallonsa murya gwanin ban tausayi ta ce,"don Allah ka kira min Ummi". shiru kamar bai ji me ta ce ba, ta ƙara maimaita masa ya ce,"kin gyaro wayar ne?". tana kallon saman kansa da ke duƙe tace,"wacca wayar?". ya ce,"wadda kika fasa". a shagwaɓe ta ce,"to ai bana sa ne". ya ce,"to sai ki jira sai randa kika gyara". kukan da ya tsaya ma ta ya dawo, ta dinga roƙonsa akan ya kira ma ta Ummi ko Kaka, bai ko bi ta kanta ba yana gama naɗa bandage ɗin ya ɗauki first aid ɗin yay ficewarsa. around biyu na dare Fillo ta kasa bacci saboda tsoro, duk yanda ta so ta dake tai bacci ta kasa, sai tayi ta jin kamar ana motsi a ɗakin, a imagination ɗinta ma kamar kukan wani abun take ji, ta buɗe ido a hankali ta diro akan gadon tana tafiya saɗaf saɗaf sai adu'a takeyi ta fita daga ɗakin, da gudu kuwa ta kwasa ta ƙarasa ɗakin Turaki, tana shiga ta tura ƙofa ta jingina da ƙofa tana sauke a jiyar zuciya. motsinta ya sa Turaki buɗe ido ya ƙaro hasken bedside lamp, ta kusa ba shi tsoro ganin gashin kanta duk a barbaje, takaici ya cika shi ya buga mata tsawa lokaci ɗaya kamar wadda aka ɗauko sai gata a bakin gadon tana kyarmar jiki. "don Allah ka yi haƙuri, wallah tsoro nake ji ɗakin sai kuka ake yi a cikinsa". ta faɗa a cikin muryar kuka me tattare da rauni, har ya ƙara haɗe rai zai korata sai kuma ya tuna matsalar da ke tare da ita ta aljanu, saboda haka ya fasa ya kamo hannunta ya zaunar da ita a bakin gadon kusa da shi. calmly ya ce,"idan ba ki daina kukan ba sai na kore ki". ɗiff tayi shiru tana ƙanƙame jikinta. tausayinta ya kama shi sosai, ya sauko yace ta haye kan gadon, ta kalle s
🏠