ta karatun ƙur'ani, ya durƙusa ya gaishe da ita, tayi ta saka masa albarka kuwa tana jadadda masa akan ya gaida iyali.
ya ce,"Umma Bello ya dawo ne?, na kira wayarsa ban samu ba".
ta ce masa,"yana ciki bai jima da shigowa ba ma".
ya wuce ɗakin Bello, kuma yana zuwa ya tarar da shi kwance rungume da pillow yana waya, Turaki yaja dogon tsaki na takaici, ya jefa masa flash ya juya ya fice ba tare da yace masa komai ba.
bai koma gida ba sai bayan sallar magrib, yana shigowa parlo Sakina da Hannatu suka yi saurin durƙusawa su ka gaida shi, bai amsa musu ba illa bin parlon da yayi da kallo, ganin babu Fillo sai ya haye upstairs ɗin, yana buɗe ɗakinta ya ganta shame-shame a ƙasa sai murƙususu take yi, ya wuce ya dire ledar drugs ɗin akan stool, har ya juya zai fita sai kuma shashsheƙar kukan da ke fita a hankali ya dakatar da shi.
dawowa yayi ya durƙusa a gabanta, ya tsayar da ƙwayar idonsa akan fuskarta da hawaye ke ta zuba, ga uban gumi ta haɗa kamar an watsa ma ta ruwa, ga wani irin nishi kamar me naƙuda, sai ka kasa kunnenka sosai tukunna zaka ji kiran sunan Kaka da Ummi da take yi a wahalce.
ya ɗan taɓa hannunta yana cewa,"ke".
ta damƙo hannunsa ba tare da ta sani ba ta murgina tare fashewa da kuka sosai.
"wayyo Allah nah, wayyo Ummi nah, wayyo zan mutu".
ya sa hannu ya taɓa jikinta yaji zafi rau, sai kawai yaji ta ɗan ba shi tausayi, ya kamota zai ɗagota da ga kannanaɗewar da takeyi kamar miciji tace,"a'a".
muryarsa a hankali ya ce,"me yake damunki?".
sai a sannan ta iya buɗe idonta a wahale tana kallonsa a disashe saboda ruwan hawayen da ya cika ma ta ido.
shi kuma ganin tana kallonsa ya tamke fuska yana haɗe gira sama da ƙasa ya ce,"me?".
ta mayar da idon ta rufe tare da kamo hannunsa ta ɗora akan cikinta, ya kalli cikin ya ƙara cewa,"me ya sami cikin?".
cikin kuka ta ce,"don Allah ka kira min Kaka mutuwa zanyi, ko kuma ka kaini asibiti su cire min cikina don Allah".
yay shiru for some minutes sannan ya ce,"me kika ci?".
tai shiru ta kasa ce masa komai sai burgima take yi tana kuka sosai.
ya miƙa yaje ya ɗauko ledar drugs ɗin da ya shigo da su, ya fita ya ɗauko ruwa a ɗakinsa ya dawo, ya durƙusa yana ce ma ta,"tashi ki sha magani".
ta girgiza ma sa kai, ya ɗaga murya sosai,"na ce ki tashi ko".
ta ce,"Kaka ta hanani shan magani".
haushi ya kama shi ya miƙe zai fita karaf idonsa ya sauka akan tiles inda take kwance, wajen duk ya ɓaci da jini, yay saurin rufe ido yana girgiza kansa, lokaci ɗaya amai ya taso masa babu shiri yay hanzarin ficewa, amai sosai ya yi da ya shiga toilet, bayan ya fito ya tsaya yana tunani, yana jin zuciyarsa duk babu daɗi.
yay ta so ya tuna sunan abin da ya gani a ƙasa, ya dai san Nihal ma na irin haka wanda har suma take yi ita, sai kawai ya ɗauki wayarsa yay dialling lambar Zaytuna, tana ɗagawa ko sallamar bai amsa ba ya ce,"mene ma sunan wannan abun da kuke yi every month?".
ta ji yay tambayar kamar a rikice, ba ta fuskance shi ba sai daga baya sannan tace,"oh menstruation". yay ɗan jim sannan ya ce,"wanne irin magani ake sha?". ta ce,"zan maka text ɗin su yanzu".
yay ɗan guntun tsaki ya ce,"babu a gida?".
ta ce,"akwai".
ya ce,"to ki kawo yanzu, idan ana allura ma ki taho da ita".
ya koma bakin gado ya zauna ya kulle idonsa yanata girgiza kansa, yana da ƙyanƙyami sosai fiye da tunani, ko Zaytuna da yake cin abincinta idan tana period ko ruwan hannunta ba ya sha, har yanzu zuciyarsa ba ta bar tashi ba, so kawai yake ya ƙara yin wani aman ko zai ji daɗi, kansa har wani ciwo yake yi.
ya na nan zaune yana ta aikin jera tsaki kamar aikin farilla, wayarsa ta yi ringing, yana ɗagawa bai ko jira abin da Zaytuna zata ce masa ba ya ce,"ki sameta a ɗakinta".
"Hammah ai ban san ɗakin nata ba, ban taɓa shigowa ba".
a daƙile ya ce,"zan kashe fitilar ɗakina".
ta ce,"tom".
Sanda Zaytuna ta shiga ɗakin, samu tayi ta kyala amai yafi guda huɗu duk wuri daban daban, sai dukan tiles take yi tana ambaton innalillahi, tana faɗin azo a taimaka ma ta, ta kira sunan Kaka ta kira na Yami.
Zaytuna ta ƙarasa da sauri, ta ɗauki jarkar ruwan da ke wajen ta buɗe ta tuttula a cup ta bata magani ta sha, sannan tayi ma ta allura, tsabar wahala ma bata san wa ke kanta ba, a hankali a hankali kuma taji ciwon yana ɗan sauƙi.
sai lokacin da iya buɗe ido ta kalli Zaytuna ta ce,"Adda".
ta amsa ma ta tana cewa,"sannu".
Zaytuna ta riƙeta ta kaita toilet ta ce ta daure ko ba tayi wanka ba ta ɗauraye jikinta, haka tayi wanka a daddafe ta fito, zata kuma kwanciya a ƙasan tiles ɗin Zaytuna ta hanata, ta buɗe wadrobe ta ɗauko ma ta riga ne ɗan kauri iyaka gwiwa ta bata, sannan ta kwanta akan gado, tana kwanciya baccin wahala ya ɗauketa.
Zaytuna da kanta ta gyara wajen tas, har kayan da ta cire ta wanke su a machine, ta kunna turaren wuta sannan ta kira Turaki a waya tace masa zata tafi, toh kawai yace ma ta, before ya kashe wayar tayi saurin ce masa,"kar ta sha ruwan sanyi, da abu me zaƙi, da cocumber".