fa normal take, me ya sami taka ɗin da ma?"
Turaki ya ɗan kalle shi sannan ya ce,"fasata ta yi, gaba ɗaya ta tarwatsata ta koma fanko".
"ban gane ba, da ma ka haihu ne da har yara su ka fara yi maka babban ta'adi haka?".
"nop ban haihun ba dai tukunna, fitowa tayi da ga cikin ta fasa sai ta koma".
ya kalli Bello da kyau ya ce,"ka daina tambayar rainin hankali Bello, wataran sai ka haɗu da wanda zai rufeka da duka".
ya maida hankalinsa ga abin da yake yi, Bello dai sai cika shi da tambayoyin rainin wayo yake yi amma sam yaƙi responding nasa, da ya gaji kawai ya miƙe ya tattara komatsansa ya fice ya bar masa part ɗin gaba ɗaya.
part ɗin Fillo ya koma, lokacin tana kitchen su na aiki da yaran da aka aiko ma ta yau da safe, jiyo motsin shigowa parlon yasa tai saurin wanke hannu a sink ta fito, ganinsa ta yi zaune ya ɗora ƙafa ɗaya kan table ɗin, yatsansa ɗaya cikin baki ya kafawa laptop ɗin ido da alama nazarin wani abu yake yi, kafin ta ɗauke ido akansa taga ya miƙe da kayansa a hannu ya wuce upstairs, ta bi shi da kallo tana hararsa, sannan ta juyo ta mayar da idonta wurin da ya tashi tana faman ɓata fuska, haka kawai ya zo ya ɓata ma ta wuri, ya ɗauko table daga in da yake amma mayarwa ta gagara.
ta wuce tana ƙunƙuni ta ɗauke table ɗin ta mayar da shi ainihin in da yake, sai maganganunta take yi ita ɗaya har Bello ya shiga ma bata sa ni ba, sai da ta baro wajen zata koma kitchen sannan ta lura da shi. tai murmushi tana gaida shi, ya amsa ma ta yana tambayarta ya lafiyarta, ta ce,"Alhamdulillah".
yana kallon bandage na hannunta ya ce,"subhanallah ciwo kika ji haka?".
ta ce,"ehh jiya ne na yanke, amma da sauƙi".
ya ce,"ya salam to Allah ya sauƙe".
"amin na gode". sai kuma ta ce,"ka zauna mana".
ya ce,"nop ina sauri ne, MT fa yana nan ko yana ɗaya part ɗin?".
ta ce,"na ga ya hau sama".
Bello ya fito da flash da ga aljihunsa ya ce,"please ki ba shi wannan".
tana tsaye da ga in da take tace,"ka hau ka same shi mana".
ya ce,"no anata min waya daga office ne, ki ba shi yanzu please kice masa yay calling ɗi na".
ta wuce taje ta amsa, shi kuma yay ma ta sallama ya tafi.
kamar ta hau saman taje ta kai masa sai ta fasa tai wucewarta kitchen suka ci gaba da aikinsu, haka kawai yau ta tashi da kwaɗayin dambun gero, sanda ta shiga kitchen taga hannu ɗaya gareta har ƙwalla sai da tayi, kuma sai Allah ya taimaketa yaran suka zo a lokacin, nan da nan kuwa suka shiga kitchen ɗin tare.
kuma sai da suka kamma dambun kawai taji gaba ɗaya bata son cinsa, tun safe da ta tashi take jin mararta na murɗa mata kaɗan kaɗan, yanzu kuma ciwon ya ƙaru sosai, ta san ba komai ba ne illa period ɗinta, haka yake yi mata da ma, da zarar yazo kuma duk sai ya cika mata ciki taji bata son cin komai, fatanta ɗaya ne kar tayi wahalallan ciwon da ta saba.
ta kalli ɗaya cikin yara me suna Sakina ta ce ma ta,"kinga ɗauko wancan flask ɗin ki cika shi sai ki kaiwa Baba me gadi, idan kuma ba zaku iya cinyewa ba ki bawa Baban kice dan Allah ko da wanda zai bawa".
ɗayar me suna Hannatu ta ce,"Anty ke ba za ki ci ba?".
Fillo tai ma ta wani kallo ta ce,"na ce miki sunana Halima, bana son wani Anty. na ƙoshi naji ya fita a raina".
ta juya ta fita, Sakina da Hannatu suka shiga gulman wai ciki ne da ita, su na cikin ƙusƙus ɗin su sai gata ta dawo, ta ce da su,"yauwa yanda ma za'ayi, dan Allah ku kaiwa Kakata, ai kun san ɓangaren masu aiki ko?".
Hannatu ta ce,"anan gidan?".
ta ce,"no can gidan su me gidan nan".
Sakina tace,"ehh mun sani, kwananmu biyu ma a can".
haka kawai taji wani daɗi tace,"kun san Yami?".
suka haɗa baki wajen cewa,"ai a wajenta ma muka kwana".
"yauwa to ita zaku kaiwa, kuce ina gaisheta kuma don Allah ta sa Maijidda ta zo".
ta faɗi hakan ta fita a gaggauce saboda ciwon marar da ya fara tsananta ma ta.
tana hawa upstairs taji karatun qur'ani na tashi a room ɗin da ke kusa da nata, ta yi wucewarta ɗakinta sai faman yamutsa fuska take tana danne mararta.
har ta kwanta akan gado sai ta tuna da saƙon Bello, hakan yasa ta miƙe ta fito cikin ƙarfin hali ta wuce ɗakinsa, ta tura ƙofar tana sallama aciki-ciki, shi kuwa kamar bai ji sallamar ba dan bata ji ya amsa ba.
ganinsa babu riga yasa tai saurin rufe idonta, ta shiga ciki tana lalube kamar makauniya har ta isa inda taji kamar mudubi ta taɓa, ta ɗora flash ɗin da Bello ya bata akai sannan tai saurin ficewa ta bar ɗakin.
around 5 kiran wayar Maama ya shigo wayar Turaki, lokacin ya rufe laptop kenan, ya ɗaga da ga can ɓangaren Maaman ta ce masa,"ka na office ko gida?".
"ina gida Maama".
ta ce,"jiya Daughter ta manta magungunanta sai yanzu nake ganinsu, ka zo yanzun nan ka amsar ma ta dont waste time, ya hannun na ta?".
ya ce,"da sauƙi".
ba tare da tace masa komai ba ta kashe wayar, ba'a son ransa ba haka ya shirya, ba ya son wani faɗan dan haka bai tsaya ɓata lokaci ba, kuma ko da ya karɓo direct gidan su Bello ya wuce, Umma ya gani zaune a falo tana yiwa ƴan jikokin