i idan ita take buƙatar hakan shiyasa ta faɗa".
Mum na ta kallonsa ta kasa cewa komai dan kallon typical mahaukaci take yi masa, Hajiya Madina ta kira Zaytuna a waya ta ce taje part ɗinta ta ta zo ma ta da Fillo.
wucewar minti uku sai gasu tare, Fillo ta rakuɓe waje ɗaya tana rarraba idanu akan carpet, Turaki ya dinƙa kallonta yana ganin yanda fuskarta tayi jawur, da kuma uban bandage ɗin da ke hannunta.
Mum ta ce da ita,"karki ji tsoronsa ki saɓa shari'ar musulunci, faɗi ya sakeki ko bai sakeki ba?".
cikin dusashewar muryar kuka ta ce,"ya sakeni".
Maama ta ɗauki remote a kusa da ita ta jefawa Turaki sai ga shi a goshinsa, ya dafe wajen da lokaci ɗaya yayi malolo yana,"shhhh, Maama ni wallahi ban saketa ba ƙarya take yi".
Fillo ta ɗago ido ta kalle shi ta ce,"wallahi fa kake cewa?".
yanda tayi maganar dariya ta kusa fito masa amma sai ya dake ya zabga ma ta uwar harara ta yanda su Maama ba su lura ba, itama ta murguɗa masa baki tare da ɗauke idonta akansa ta kalli Mum ta ce,"tun a ranar da muka je asibiti duba shi ya sakeni, ni kuma na kasa faɗawa kowa, shi ne yau yace in dai ban bar masa gida ba sai na ƙwammace da ban taɓa saninsa ba har ma da ku".
ya kalli su Mum da duk idanuwansu ke kansa, da sauri ya ce,"Allah ban saketa ba". sai kuma ya juya ya kalli Fillon ya ce,"ni da bakina na furta miki hakan?".
ta harare shi tana fito da ɗayan hannunta da ga hijabi ta miƙawa Maama takardar hannunta.
ganin takardar idanuwansa suka fito waje da sauri ya kai hannu zai ƙwace a harzuƙe Mum ta sa masa ƙafa ta hamɓarar da shi gefe. ya ɗago da ga kifewar da yay yana ɗora hannu aka yana ambaton innalillahi da ƙarfi har sai da kowa ya kalle shi.
sanda Maama ta gama karanta takardar sai ta kalli Mum, ta miƙa ma ta Mum ta kau da kai tana girgiza kanta alamar ba zata karɓa ba.
Maama ta ce ma ta,"dan Allah ki karɓa your excellency, zuciyata zata fashe".
Mum ta juyo da sauri ta karɓa, ta kifar da takardar a cinyarta da ƙyar ta yarda da roƙon Maama ta karanta.
ta kalli Fillo a sanda ta gama karantawar ta ce,"yaushe ya ba ki wannan takardar?".
ta tsagaita kukanta ta ce,"ranar da muka je asibiti duba shi".
Mum ta ƙara cewa,"ruwan hawayenki ya shanye wajen adadin sakin, nawa ya rubuta?".
furucin Mum ɗin yasa idanuwan Turaki suka ƙawalalo waje fiye da ɗazu, ƙirjinsa ya ce taratsatsa.
Fillo ta buɗe baki wani sabon kukan na tahowa ta ce,"ai ban karanta ba".
Mum ta miƙa ma ta takardar tana cewa,"to karɓi".
Fillo ta karɓi takardar zata cusa a hijab Mum ta ce,"karantawa za ki yi ai, idan ba ki karanta ba sakin ai bai tabbata akanki ba, ki karanta sai ki nuna masa kuskurensa ki ɗau duk kalar matakin da kika ga ya dace da shi".
tana gama faɗa ta miƙe ta bar wajen, Maama ma ta fi ce, Zaytun ta haye Uptairs tabi bayan Mum, aka bar Fillo da Turaki kawai, ta ɗago kumburarrun idanuwanta ta kalle shi taga fuskarsa kamar baƙin hadari, hawaye na sakko ma ta ta ɗora ido akan takardar, sai taji fargabar yau tafi ta ko yaushe, ba ta san me yasa ba ko kaɗan ba ta ƙaunar adadin sakin da yay ma ta, sai dai kuma a sanda ta shiga karanta rubutun da ke ji sai taga saɓanin abin da zuciyarta ta faɗa ma ta tun ranar da ya bata takardar, idanuwanta suka karanta abin da yake daban da wanda take ta haskowa yana rubuce a jikin takardar.
wannan wani rubutu ne na daban, rubutun da ko kusa bai da alaƙa da abin da sakin da ta gama yankewa kanta anyi ma ta, rubutu ne take kallonsa da handwriting ɗin da ya burgeta, haka kuma taji kalaman da ke jiki na tafiya su na haɗewa da jinin jikinta, taji tana sha'awar da a karanta ma ta su a kunnenta.
ta karanta sau ɗaya ta kuma gane ma'anar but haka kawai sai taji tana ƙara buƙatar ta ƙara karantawa.
_my life depends only on you, i love you Fulani Nah, i love you up to the square of infinity, i promise you that i will take care of you morethan i will take care of my self, trust me when i say i can't do without you, Fulani Nah love me even just a bit._
ta rufe ido a sanda ta gama karantawa, taji bugun zuciyarta na sauyawa zuwa wani yanayi da bata taɓa riskar kanta a ciki ba a dai ga me da Turaki, ta sauke numfashi ta buɗe idon tana sauke akan Turaki.
tuni ya miƙe tsaye hannayensa na zube cikin aljihu, ta bi shi da kallo sanda ya wuce ta gabanta, sai da yaje bakin ƙofa sannan ya dakata ya juyo yana kallonta rai a haɗe murya a tamke ya ce,"kin taso ko kuwa".
ta ɗauke idonta da ga kansa ta mayar gefe, ya ƙara cewa,"ba za ki taso ba".
ta kumbura baki ta ce,"ai ka ce kar na koma maka gida".
Turaki ya saki baki yana kallonta, zai sake magana sai ga Mum nan ta sakko, ta yi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta ta isa kujera ta ɗauki wayarta, har ta juya sai kuma ta waigo ta kalli Fillo dake zaune ta ce,"tashi ki bi mijinki".
Fillo ta miƙe ta bi bayansa lokacin har ya kai bakin mota, ta buɗe baya ta shiga, ya kalleta ta mirrow ya ce,"do i look like your driver?".
ta hankaɗo laɓɓa gaba ta sunkuyar da kanta ƙasa tana sh