NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 242 of 323

r ɗakinta, haka kawai yaji gabansa ya faɗi duk da bai san abun da ke faruwa ba, Hajiya Madina ta waigo dan ganin mai shigowa, tana ganinsa ta miƙe ba tare da ta shirya ba ta fuskance shi. murya a sama ta nuna masa hanyar fita ta ce,"fita, fitar min da ga ɗaki kafin na sa ƙafa na take in take banza". muryarta ta fita da tsananin ɓacin rai. yay tsuru tsuru ya buɗe baki zai yi magana ta ɗaga hannu ta wanka masa wari, ta shiga nuna shi da yatsa tana faman huci tace masa,"da ga ranar yau zuwa ranar da za'a busa ƙaho babu ni babu kai, in har ka ƙara shiga sabgata tabbas hukuma ce zata rabani da kai, ma za juya ka bar min ɗaki". ganin ba zai fita ba ta rarumo ƙaramar kujerar da take zama zata buga masa, babu shiri ya juya cikin sauri ya fi ce. yana zuwa part ɗin Mum ya tarar da ita zaune a parlo ta zabga uban tagumi, zuciyarsa ta shiga lugude, ya tafi kamar munafiki ya tsuguna a gefen ƙafarta, bai san dai laifin da yay ba amma saƙon da Khalil ya ba shi ya san akwai laifin da ya aikata. muryarsa a hankali ya ce,"Mum lafiya?". ya tambayeta yana ƙoƙarin cire hannun da tayi tagumin da shi, sai dai tun kan ya kai ga taɓata ta make shi da mugun zafi. "matsa da ga kusa da ni". ta faɗa tana sauke masa rikitattun idanuwanta da ke nuna zallar ɓacin rai, nan da nan hankalinsa ya tashi ya shiga tambayar laifin da yayi. "wallahi tallahi idan har baka matsa da ga kusa da ni ba ko me na ɗauka sai na buga maka in yaso ka mutu in huta da baƙin ciki da takaicin rashin dacen haihuwarka da nayi". ya buɗe baki ya furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yana kallonta zai ƙara yin magana a mugun tsawace ta dakatar da shi,"na rantse da Allah ka ƙara min magana a wurin nan sai na fiddo maka da nonona ka biya ni wanda na sha, banza mara mutunci shashasha butulu kawai wada bai saka halacci da halacci sai dai ya saka halacci da sharri, da ga ranar yau ina me tabbatar maka da babu ni babu kai har abada kuwa". ta sauke yatsanta da ga kansa, ta ɗau wayar da ke kusa da ita ta kira Khalil, cikin mintina kaɗan sai ga shi ya shigo, tai masa nuni da kujera ya zauna a ɗarɗarce, ta ɗauki takarda da biron da ke kusa da ita ta wurgawa Turaki wanda ke dafe da kansa yana ta amabaton kalmar innalillahi a zuciya da fili, magana yake so yayi amma babu dama saboda rantsuwar da Mum tayi. "mu ba matsiyata ba ne, kai tsiya ta yiwa ƙatutu, Allah ya hore mana yay mana arziƙin da zamu iya siye duk abin da ka mallaka har kake taƙama da shi, ka rubuta kuɗin matsiyaciyar wayar da kashe hannun ƴar mutane saboda ita, ko nawa ne za'a biyaka dan kai ne faqararre". ta ƙyasta yatsunta biyu ta ce,"kuma ka sa ni, duk illar da hannun ƴar mutane yayi wallahi sai mun shiga kotu da kai". ganin zai yi magana ta kuma doka masa tsawa,"kuɗinka nace ka rubuta". yay taking deep breeth yana kulle idanuwansa yay rubutu ajikin takardar, da ido Mum taiwa Khalil nuni da ya karɓa, ya karɓa yana kallon abun da ya rubuta, Galaxy fold Z2 1.3ML tare da kuɗin gyara 700k. ya kalli Mum zai ma ta magana ta ce,"tura masa kayansa". Khalil ya ɗau wayarsa in few minutes ya turawa Turaki kuɗin, seconds kaɗan sai ga ƙarar shigowar alert a wayar Turaki. "Mum sun shiga". Khaleel ɗin ya faɗa yana dubanta. ba tare da ta kalle shi ba ta ce,"ka kira min Madam". ya tashi ya fita, babu jimawa sai ga Hajiya Madina ta shigo fuskarta sam babu annuri babu walwala, ta tsaya cak da ga baya tana cewa da Mum,"ya za'ai ki kirani alhalin wannan ɗan banzan yaron yana zaune anan, ko kaɗan yanzu bana son ganinsa, zan dawo in sameki after ya fita". ta faɗa tana juyawa Mum ta dakatar da ita da cewa,"so nake ki zame min shaida dalilin da yasa na kiraki kenan". hakan yasa Maama dawowa tazo ta nemi kujera ta zauna, ta juyar da fuska yacca ko kaɗan ba zata fuskanci Turaki ba. Mum tace,"ko bayan raina ban amince ba wannan ɗan banzan yaron yay aure, ina so ki zamar min shaida". da sauri Turaki ya ɗago ido yana dubanta, me ya yi zafi shi ba wuta ba?, laifin me ya yi har haka?, yaji duniyar gaba ɗaya tayi masa zafi kansa na neman tarwatsewa, da ƙyar ya iya tattaro yawun bakinsa ya ce,"Mum me ya yi zafi haka?, wanne irin laifi na aikata muku?, idan abin da naiwa ƴarku ne na roƙeku don Allah kuyi haƙuri ni kaina na san nayi kus....". maganar tasa ta yanke lokacin da yaji saukar jotter da biro a fuskarsa. ya kalla Maama da ke kallonsa da tsananin ɓacin rai tace da shi,"ka rubuto min sauran sakinta shi ne zaka tabbatar min da kai isashshe ne, dan ba zan karɓi saki ɗaya ba domin kuwa Fillo ta gama aurenka har a naɗe duniya". ya kulle ido yana sauke numfashi, sannan ya buɗe yace,"Maama ce muku tayi na saketa?". "ba ka saketa ɗin ba ne?". ya shiga girgiza kansa yana faɗin,"ni ban saketa ba Maama, idan ma haka ta faɗa muku to ƙarya take yi". Maama ta dinƙa kallonsa babu ko ƙifce, kafin tace,"kai ko dai kayi hauka ne?, ko kuma shaye-shaye ka ke yi a ɓoye?". ya ce,"Allah ni Maama ban san da wani batun saki ba a tsakaninmu, sai da
🏠