shiga ciki ki gano min ko ya dawo".
a tsure Fillo ta ce,"Maama ai...".
kuka ya kubce ma ta ta kasa cewa komai.
Maama na kallonta ta ce,"ai me?".
ta buɗe baki tana jin kamar yawun bakinta yayi kaɗan su yi maganar da zata yi, tace,"he divorce me".
da wani mugun shock Maama ta ce,"what?, divorce!, ƙalu innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, ya sake ki fa kika ce?".
tayi maganar tana jin kanta na mugun sara ma ta, tai saurin dafe shi tana rumtse ido ta jinginar da kanta jikin kujera.
Fillo ta fashe da kuka, Nihal ta shigo motar tana cewa,"bai dawo ba Maam...".
maganartata ta tsinke jiyo numfashin Maama na fita da ƙyar, a ruɗe ta ce,"innalillahi, Maama".
ta faɗa tana fitowa ta zagayo ta buɗe side ɗin da take, "Maama". ta faɗa tana kamota.
Hajiya Madina na dafe da ƙirjinta da ƙyar ta iya cewa,"mu je gida da sauri".
tun kamin su ƙarasa gidan Nihal ta kira Mum a waya ta sanar ma ta cewa BP ɗin Maama ya tashi, kafin su ƙaraso tana tsaye a compoud hankalinta a tashe sai safa da marwa takeyi.
ko parking Nihal ba ta ƙarasa ba Mum ta buɗe, ita ta kama Hajiya Madina suka wuce, ko lura da Fillo ma bata yi ba, sai bayan ta kai Hajiya Madina bedroom ne ma taji tana ce mata,"ina amanar da mu ka karɓa?"
Mum ta ce,"wacce amana?".
Maama na magana da ƙyar ta ce,"Fillo". sai kuma muryarta ta karye tana cewa,"your excellency me babban suna ya cuce mu, sati ɗaya da aure ya saki yarinyar mutane".
Mum ta zabga wani salati tana waro ido waje ta kalli Nihal da Fillo da ke shigowa ɗakin. sannan kuma ta juya tana ƙara kallon Maama wacca taga kamar ba'a hayyacinta tayi maganar ba, ta ce,"wai saki kamar ya ya dai Madam?, saki na aure? ko wanne kalar saki ban gane ba?".
cikin ƙarfin hali na irin zafin da Maama ke ji a ƙirjinta ta ce,"divorce dai da kika sa ni, kawai saboda ta fasa masa waya ba ta sani ba, ki duba hannunta ma ki gani ciwon da yaji ma ta".
farat ɗaya ran Mum ya kai ƙololuwar ɓacin da bai taɓa yi ba, ta ce,"ba shi da hankali ko kuwa shaye-shaye ya fara bamu sani ba?".
ta kalli Nihal ta ce,"kirawo min shi dan ubansa".
sannan ta kalli Fillo tace,"laifin me kika yi masa da har zai sake ki?".
ta zube gwiwoyinta a ƙasa tace,"ai dama tuntuni na ya sake ni".
Maama ba ta san lokacin da ta miƙe zaune ba tayi warkewar lokaci ɗaya, Mum ta nemi wuri ta zauna, a tare suka jefa mata tambayar,"wacce tuntunin Fillo?".
"tun before na tare, na kasa faɗawa kowa ne...". kuka yaci ƙarfinta tayi shiru tana rumtse ido.
Maama ta saki baki kamar yanda Mum tayi duk suka kasa cewa komai, wucewar daƙiƙu muryar Nihal ta kutsa cikin shirun na su da cewa,"Mum bai ɗaga ba".
ba tare da tace ma ta komai ba ta miƙa ma ta hannu Nihal ta ɗora ma ta wayar, ta lalubo lambar Bello ta kira, bugu uku ya ɗaga, a fusace tace da shi,"da kai da shi kunci kutumar ubanku, kuna ina?". tayi tambayar a tsawace.
zagin da tsawar suka daki kan Bello yayi zillo akan kujerar da yake, ya haɗiye yawu da ƙyar ya ce,"Mum". tai saurin katse shi,"zanci ubanka idan ka ƙara kiran sunana, na ce kuna ina?".
cikin ƙinƙina Bello yace,"ni ina office shi kuma ban san inda yake ba".
"ƙarya kake yi munafiki".
yace,"wallahi Mum rabona da shi tun last week, ko haɗuwa bama yi a office".
tai shiru kafin tace,"to ka kira kirasa ka faɗa masa minti ashirin na ba shi yazo ya sameni".
ta katse wayar, Nihal tayi saurin karɓa ganin tana ƙoƙarin jefar da ita a ƙasa.
bayan minti biyu kiran Bello ya shigo, ganin Mum bata da niyyar ɗagawa Nihal ta ɗaga yace ma ta,"ki faɗawa Mum wallahi ina ta kiransa bai yi picking ba for morethan 4times, kuma ni ban san inda yake ba".
Nihal ta faɗawa Mum, sai tace ta kira ma ta Khalil, yana ɗagawa Mum ta ce da shi,"ka kira min ɗan banzan Hamma'nku ka faɗa masa tun banyi masa baki ba ya sameni a gida cikin gaggawa".
ba tare da jiran cewarsa ba ta kashe wayar.
ɗaki dai yay shiru tamkar babu wata halitta acikinsa, ran kowa a cunkushe, zuciyoyin kowa da abunda take saƙawa.
minti goma minti ashirin suka wuce, rabin awa ma haka, aka cika awa guda ma, duk su na zazzaune jungum jugum, Hajiya Madina ma ta kasa shan magungunan da aka ajiye ma ta.
can suka ji buɗewar ƙofa an shigo, Zaytuna ta shigo tana ajiye jakarta, ta cire labcourt ɗin jikinta tana zazzare idanu wajen kallon kowa kafin ta buɗi baki tace,"Mum, Maama lafiya?".
babu wanda ya kalleta balle ya amsa ma ta, sai tayi tsuru-tsuru ta kalli Nihal suka yi magana da ido ta nuna ma ta Fillo dake durƙushe a ƙasa.
sai taja bakinta tayi shiru ta fasa sanar da saƙon Turaki da ya faɗa ma ta cewa tace da Mum yaje kano ne after magrib zai dawo, wayar da take kira ba ta ɗaguwa.
shirun da yay yawa yasa Mum miƙewa ta fita, aka bar Maama da Fillo har sai da akayi sallar la'asar tukunna tace da ita ta tashi tayi sallah.
gida dai sai yay ɗiff kamar gidan mutuwa, ran iyaye babu daɗi yara kuma duk sun shiga damuwa saboda yanayin da iyayensu suke ciki, bayan sallar magriba Hajiya Madina tana lazimi Turaki ya tura ƙofa