NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 240 of 323

da Hajiya Madina tayi, karaf idonta ya fara sauka akan hannun Fillo da ke zubar da jini, ta zaro ido waje tana ambaton,"subhanallahi". sai kuma ta kalli Fillon ta ga tana hawaye ga shi kamar ba ta cikin hayyacinta, tai saurin kamota ganin tana neman faɗuwa. "Daughter lafiya?, wannan jinin fa da ga ina?". Fillo ba ta iya ba ta amsa ba, haka ba ta iya kallonta ba, Hajiya Madina ta riƙeta suka yo waje tana cewa da Nihal,"ko ma ki tayar da mota". sannan ta ƙara ce wa da Fillo,"ina me babban sunan?". sai a sannan ta iya buɗe baki ta ce,"ya fita". san da motar Maama ta fita da ga gidan Baba me gadi ya girgiza kansa cike da tausayin Fillo, yarinya ƙarama ana neman a ɗora ma ta hawan jini, tun ranar da aka kawota ya fuskanci ba auren soyayya akayi ba, dan shi dai bai taɓa ganin Turakin ya shiga part ɗin ba sai ɗazu da ya fito a fusace kamar macijin da aka dannewa kai. direct asibiti mafi kusa suka wuce, tun tahowarsu Maama da Nihal ke jera ma ta sannu, su na zuwa cikin gaggawa Dr yay ma ta treatment ɗin wajen, ya cicciro pieces na glass yafi biyar a tafin hannunta, aikuwa tasha azaba dan jini kamar ana tatsarsa hannun duk ya caɓe, akai ma ta allurai, Nihal taje pharmacy ta karɓo maganunguna, lokacin da ta dawo an naɗe hannun Fillon da uban bandage. da ga fitowarsu zuwa yanzu kuwa Maama ta kira wayar Turaki yafi sau bakwai duk ba ta shiga, kuma duka lines ɗin nasa, hankalinta duk a tashe yake da ciwon Fillon, ta kira wayar Mum ta tambaya ko Turaki ya zo gida ta ce ma ta a'a, Bello ma yace ba sa tare. kan hanyarsu ta dawowa Maama ta matsa ma ta da tambaya akan yacca akayi taji ciwon, ta kasa haɗa ƙaryar da zata faɗawa Maama ɗin, tai shiru ita dai sai rera kuka takeyi a hankali, har sai da taji ɓacin rai a muryar Maama tukunna ta ce,"wayarsa na fasa masa ban sa ni ba". Maama na kallonta ido buɗe ta ce,"fasa waya kuma sai kiji ciwo haka?". tayi shiru tana daɗa yin ƙasa da kanta, Maama ta dinƙa kallonta tana so ta nazarci yanayinta, uwar ramar kaɗai da yarinyar tayi ya isa ya shaida maka hankalinta ba'a kwance yake ba sam, dole akwai wata matsalar a ƙasa, dole da akwai abin da yake faruwa wanda basu san da shi ba, tun da me gadi yace ma ta Turaki ya fita babu jimawa ta san akwai matsalar da ke faruwa musamman da taga Fillo a wannan yanayin, babu tantama saɓani suka samu duba da yanda duk Fillon take a tsorace. _me ce matsalar?._ tambayar da ta yiwa kanta kenan, sai dai babu amsarta. hakan ya sa ta kamo hannun Fillo tana kallonta ta ce,"ɗago ki kalle ni a matsayin Umminki wacce ba za ki taɓa iya ɓoyewa damuwarki ba". idanuwanta suka kawo sabon ruwa sanda ƙwayar idonta ke shiga cikin ta Maaman, tausayin Maaman shi ya fara kamata ganin duk ta damu, kafin girma da kwarjinin Maaman su mamayeta gaba ɗaya, ba zata iya yi ma ta ƙarya ba sam saboda ta kare kanta ko kuma ta kare shi, ta sauke kanta ƙasa muryarya a hankali ta ce,"da wayar ta fashe ne shi ne ransa ya ɓaci ya ce sai na kwashe glass ɗin da hannuna". da tsananin mamaki Maama ta ce,"me babban sunan da kansa?, ya ce ki kwashe glass da hannunki?, cikin hankalinsa yake kuwa?". wannan furucin kaɗai ya shaidawa Fillo ran Maama ya ɓaci sosai. Maaman tai shiru ba ta ƙara magana ba sai faman jijjiga kai da takeyi, idanunta na kan waya tana ƙara trying lamar Turaki, cikin sa'a kuwa yanzu ta shiga sai dai har ta gama ringing bai ɗaga ba, ta ƙara kira nan ma bai ɗaga ba, sai da ta kira har sau uku sannan ta haƙura ta jefa wayar a jaka, cikin zuciyarta sai jinjina abin da Turaki ya aikata takeyi, ko da yake da ma ba'a sanin wani mugun halin namijin sai bayan ya yi aure. Fillo dai idonta na kan hanya, tunaninta ɗaya ta yanda zata faɗawa Hajiya Madina a sauketa a hanya, ta ga motar ta tsaya bakin wani islamic chemist, Maama ta buɗe ta fita ba tare da tace da su komai ba, ta bi ta da kallo ta glass har ta shiga kantin. a lokacin ta buɗi baki ta cewa da Nihal,"Adda don Allah ina ne hanyar tashar barin gari?". Nihal ta waigo tana kallonta ta ce,"me za ki yi acan?". tai shiru ba ta ce komai ba, lokacin Maama ta buɗe motar ta shigo, sanda ta rufo ƙofa Nihal ta ce ma ta,"Maama wai tambayar tashar da za'a bar gari take yi". Maama ta waiga taita kallon Fillo, wacce idonta ke kan hannun ciwon nata, tana nufin gidan su zata tafi kenan?, ta san ba komai bane ke damunta fa ce yarinta, bata ce komai ba tayi ƙwafa me ƙarfin gaske tana ɓallo maganin da ta siyo a islamic chemist ta bawa Fillo. Nihal ta kashe sautin waƙar da ke tashi, saboda ta san idan ran Maama ya ɓaci ba ta son jin komai na shiga cikin kunnenta. bayan doguwar tafiya Fillo taji motar ta tsaya, ta ɗago kanta tana kallon gate ɗin gidan, gabanta taji ya faɗi hakan yasa babu shiri ta juya tana kallon gefen da Maama take tace,"Maama ya ce na bar masa gida". "ki bar masa gida?". ta ɗaga kanta tabbacin hakan. "saboda kawai kin fasa masa shegiya waya ya buɗi baki ya ce ki bar masa gida?". sai kuma ta bar kallon Fillo ta koma kan Nihal ta ce,"
🏠