kurɓa kamin tace da shi,"application for annual leave, ina ce ka miƙa musu ko?".
Yace,"ehh Maama na miƙa tun a washe garin ranar da yay accident ɗin".
Tace,"good, how many months kasa?".
yace,"munyi waya da shi yace na saka just 1 week".
ta ɗago ido ta yiwa Turaki wani kallo na ashe baka da hankali, hakan kuma yasa yay saurin sauke idonsa ƙasa, duk da bai san akan mene kallon ba tunda ba jin abinda Bello yace yake ba, amma wannan kallon yasan ba a banza ba.
Ta kalla goshinsa da ƙaton plaster ke manne a wajen, sannan ta tsurawa kafaɗarsa ido, tana hasko yanda wajen ke nannaɗe da bandage kwanaki biyar da suka wuce kamin jiya a kwance, ai har yanzu hannunsa na hagu baya moving sosai, amma shine saboda bai da cikakken saiti, yay wannan mummunan accident ɗin sannan yace wai hutun just 7days ya ɗauka, which means monday zai koma aiki.
Tai gajeren tsaki, ta lura Turaki nema yake ya kashe kansa a bautar company kawai, yafi damuwa da aikinsa akan lafiyarsa da rayuwarsa, to ita ba ƴar iskar uwa ba ce. Ko da yake shima Bello ba shi da hankalin ai, yana kallo har kusan fitar da rai sukai da Turaki, basu taɓa zaton zai farka ba saboda mugun ciwukan daya ji, amma shine har yake biye masa da ɗaukan hutu na kwana bakwai kawai.
Daga ɓangaren Bello so yake yay magana amma yana gudun faɗan da zai biyo baya, dan shima sai bayan daya kai takardar yaga yayi rashin tunani. ta katse tunaninsa da cewan,"then write a resignation letter ka ƙara kaiwa".
Turaki da Zaytuna duka a lokaci guda suka ɗago ido suna kallonta da mamaki tsantsa, hatta Bello daga inda yake bai san lokacin daya miƙe daga zaune ba, yana daɗa tambayarta abunda tace.
"ehh resignation letter nace, takardan barin aiki ba, And if you can't tell me sai na saka Khalil ya rubuta ya kai".
Bello ya haɗiye wani yawu yace,"amma Maama hakan sai nake ganin will not be the best solution, we should just add him a days more off...idan ya dawo sai a san zaman da za'ai da Manager to let him know what is going on".
a fusace tace,"karka rubuta ka bari zan rubuta sai na bawa wanda na isa da shi ya kawo, kuma ai dama ban kira na faɗa maka don neman shawaranka bane, umarni nake baka tunanina cewar na isa matsayin mahaifiyar amininka".
In calm voice yace,"kiyi haƙuri Maama".
Bata ko ba shi amsa ba ta kashe wayar, tana kallon yanda idanuwan Turaki suke kallonta kamar zasu fito waje, amma sai tayi kamar bata san yana yi ba, taci gaba da shafa wayarta har sanda ta nemo lambar Khalil ta kira shi, ringing biyu ya ɗaga. a taƙaice ta amsa sallamarsa ta ɗora da cewa.
"You have Bello Ƙaraye's number right?, Anyway if you don't have i will send it to you now, call him and ask abunda na karanta masa, as early as tomorrow morning ka fara aiwatar da abinda nace before you leave to koma ina ne zaka je".
Bai tsaya yin wani tambaya ba, haka itama bata jira cewarsa ba ta katse wayar ta ajiyeta gefenta.
Ba tare da ta kalli Turaki ba tace,"mun gama magana da Baffa, shima ya amince da hakan, so i do not want to hear anything different... ina ce dama saboda kuɗi kake musu aikin ko?, to mahaifinka ya tara maka arziƙin da har jikokinka ba zasu yi talauci ba, so no need of any job, ka zauna a gida kamar mace, kaci ka sha ka kwanta...bautar company ta ƙare, dan ba zan yarda kaci gaba da yi musu aiki ba suna neman hanyar da zasu kashe min kai saboda kawai kana da gaskiya, ba zan lamunta ba...i won't let anyone kill my son come what may!, aikin ai ba dole ba ne, ko da ace bamu da cin yau balle na gobe, rayuwarka da lafiyarka ta fiye min wannan tsinannan company ɗin".
Ba shi da ta cewa a yanzu, dole ne zai yi shiru har zuwa sanda zata sakko ta huce before yay Comprehending nata. bai san reason ɗin daya sa ta ke tunanin accident ɗinsa yana da alaƙa da wasu ke son ganin bayansa ba.
"hannun da sauƙi?". Ta tambaye shi tana kallonsa with so much Sympathising na uwa.
Ya amsa,"ehh sosai ma".
"Allah ya ƙara maka lafiya...tsakanina da wanda ya nemi ya cutar da kai kuma Allah ya isa ban yafe ba, tunda ba wani ya haifa min kai ba".
Shi dai bai ce komai ba, ta kalli dining ta kalli Nihal dake shigowa tace,"ki zubo pepper soup".
ta wuce dining ta zubo ta kawo mata, ta karɓa sannan ta miƙe ta isa kujerar da Turaki yake, ta kalli mug ɗin da yake aje kan table ɗin dake gabansa tace,"yaushe kasha wannan?".
Yace,"ina gama sha kina shigowa". bata ce komai ba ta ɗebo ppper soup acikin spoon ta kai bakinsa, ba son ci yake ba sam amma babu yanda ya iya haka yay ta karɓa har sai daya cinye tas, tana tambayarsa ko zai ƙara yay saurin cewa,"a'a".
kansa ya kwantar jikin kujerar ya lumshe ido, Hajiya Madina na waya da wani Asp akan Case ɗin accident da Turaki yayi har 2times, cikin idanuwan Turaki kuwa hoton yanda yay accident ɗin ke haska masa, abunda ya ɗaure masa kai, the samething da wancan, ko da yake gwara wancan yaga motar dake binsa a baya wadda ya tabbatar da attacking nasa ta ke son yi, Amma wannan kam kawai ji yayi burki ya