NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 238 of 323

ɗago ta yi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta, yana tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba ma ta ido, kamar me son karanto wani abu a tare da ita, jin idonsa a kanta yasa ta haɗe gira sama da ƙasa ta juya masa baya. wucewar daƙiƙa biyu wayarsa da ke aljihu ta shiga ringing, ya sa hannu ya ɗauko yana picking tare da cewa Hajiya Madina,"Maama ba ta fito ba ne idan ta fito zan kira ki". muryar Hajiya Madina na bayyana damuwar rashin lafiyar da yace musu Fillo na yi ta ce,"to da ta fito ka kirani kaji ko?, nima gamu nan muna kan hanyar dawowa na tsaya her excellency ne za ta shiga office ta fito, ka dai ce kunje hospital ko?". ya shafo wuyansa ya ce,"ehh Maama ta ji ma fa sauƙi, na faɗa miki ma zatona ko Baffa ya dawo ne shiyasa bamu zo ba". ba ta ce da shi komai ba ta kashe wayar tana shaida Mum batun rashin lafiyar. "da me babban suna mu ka gama waya, ashe rashin zuwan na su ba ta da lafiya ne, ni dama dai ince cin amarci ai ba zai hana su zuwa su gaisar da mu ba muna kusa da su. yanzu kawai mu tafi gidan na su ko? duk da naji yace ai jikin da sauƙi". Mum ta ce,"ni kam ba zan iya zuwa gidan su ba, tun da taji sauƙi shikenan, ki kwantar da hankalinki please". Maama ta ce,"ni kam gaskiya sai naje na dubo su hankalina zai kwanta, sati guda ban saka me babban suna a idona ba". Fillo na murguɗe murguɗe da harare harare ta nufi hanyar toilet za ta shiga, yay amfani da sautin muryarsa wajen buga ma ta tsawa akan ta tsaya, duk ta yanda taso ta dake ta nuna rashin firgitarta sai da ta tsorata ta ƙame a wuri ɗaya jikinta na kyarma. ya ƙarasa shigowa ciki ya ja stool ya zauna akai, ya saita kira akan lambar Maama, sannan ya ɗago yana kallonta yaga har yanzu rawar jiki kawai take kamar me jin sanyi tama ƙi buɗe idanuwanta, hawaye na sauka a kuncinta. yay tsaki na ban haushi da takaici, ya miƙa hannunsa ya fizgota sai ga ta ta wancakalo bakin gado kamar sandar da aka janyo, abunka da mara ƙiba sam sam. "buɗe idonki". yanda ya yi amfani da sautin muryarsa abin ya bata tsoro, kuma da ta buɗe ido ta kalle shi tsoron sai ya ƙaru fiye da misali, dan rikiɗewa ya ke yana komawa kamar ba mutum ba. muryarta na breaking ta ce,"tafiya zan yi". ya danna kiran Maama ya jefa ma ta wayar a jiki, niyyarta ta miƙe wayar ta tarwatse a ƙasa, amma sai taji Maama na magana, sannan ne ta ɗauka tana magana ta yanda Maama ba zata fahimci kukan da take yi ba a muryarta. *comment, share and vote.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *48* "Daughter nah". Hajiya Madina ta kirata da sabon sunan da ta raɗa ma ta tun a ranar da aka kawo musu ita. "na'am Maama". with much care Maama ta ce ma ta,"ya jikin naki?, da sauƙi ko kuwa?, kina shan magani?, yanzu ya kike ji?, mene yake ya damunki?". waɗannann tarin tambayoyin yasa ta kallon Turaki ta gefen ido, idonsa na kan ɗaya wayar da ke hannunsa, fuskarsa kamar baƙin hadarin da ya haɗo, ta rufe ido ta ce,"Maama lafiyata lau, shi ne kawai ya ce miki ban da lafiya". ta faɗa kamar zata sa ki kuka. furucin na ta yasa Hajiya Madina murmushi, ko ba komai ta san da gaske jikin na ta da sauƙi kamar yan da ya ce, ta furta alhamdullahi sannan ta ƙara cewa,"kina cin abinci sosai ko?". ta ce,"ina ci". "to Allah ya ba ki lafiya Daughter, Allah ya sa kaffara, ki daure ki dinƙa shan magani kinji, becx bana so na ji wani abu yana taɓa min ke, zan zo anjima na duba ku, Allah ya yi muku albarka". a hankali Fillo ta ce,"Maama Ummina fa?". ta faɗa muryarta na ɓallewa da kuka. zaton Hajiya Madina ko tana so ta ganta hakan yasa ta ce ma ta,"za ki je kiga Ummin ki very soon, ni da kaina ma zan kai ki". kamar ta faɗawa Maama komai sai kuma tayi shiru, ita tambayar da tayi saboda Maama ta ce zata haɗa su a waya ne, in yaso sai ta ce da Ummi azo a ɗauketa dan ba ta fatan ta ƙara kwana acikin gidan da ba zaman aure take yi ba. ta sauke wayar da ga kunnenta bayan Hajiya Madina ta kashe, ta waiga tana kallon Turaki ta ce,"ka ba ni lambar Kaka ko Ummi please". maganar tata sai ya zama tamkar da dutse tayi, yay banza da ita ban da ma waya da ya kara a kunnensa yana amsa sallama, ba ta ɗauke idonta akansa ba taci gaba da kallonsa, hotunan kasadar da ta dinƙa yi wurin ceto rayuwarsa yana haska ma ta a ido, sai a yanzu ne ta yarda da cewa ɗan adam butulu ne, ita ba wai don ya saketa ba, a'a irin wulaƙanci ma da yake ma ta na nuna da ita da banza da wofi ɗaya, kuma ƙila duk yana ma ta haka ne saboda sanin mahaifinta da yay, da ma sai da ta faɗawa Ummi cewa wallahi bai aureta ba saboda abubuwan da ya faɗa sai don ya wulaƙantata, a lokacin Ummin ba ta yarda da ita ba hasalima faɗa suka haɗu suka dinƙa yi ma ta ita da Kaka, but yanzu ta san dole za su yarda da abin da ta ce, kuma ko ba komai ta san Turaki zai ga ishara akan aurenta da yay ba don komai ba sai domin ya tozartata. maganar da yake yi a cikin wayar ta shiga kunnenta. "no ba haka ba ne Faruq, bana fatan na ƙara maimaita kuskure, this time around ba zan yi ga
🏠