a da ta aiko akan bambancin iddah da kuma Takaba, hakan yasa ta dire remote ta tattara hankalinta gaba ɗaya tana sauraron bayaninsa.
_"Takaba shi ne zaman da mace za tayi na tsawon wata 4 da kwana 10 bayan mutuwar mijinta. Ita kuma Iddah ita ce zaman da mace za ta yi idan mijinta ya saketa har sai ta yi jinin al'ada sau 3. Iddah mace za ta iya yin kwalliya da sauransu, amma ba zata iya yin maganar aure da wani ba har ta fita daga iddar. Ita kuma takaba mace ba zata iya yin kwalliya ba amma za ta iya yin tsafta, banda sanya duk kayan da suke ɗauke da ado na kwalliya.
Amma dukkanninsu idan mace ta na da ciki to dole ne idan aka haife cikin nan to iddar ko takabar ta yanke, Idan ma aka saketa yau kuma ta haihu Yau to iddar ta ƙare. Idan ma mijinta ya mutu a yau kuma ta haihu anjima to ta gama takaba.
sai dai kuma idan akayi aure miji bai tare da mace ba, ko ya tare da ita amma bai taɓa kusantarta ba, to ba zata yi masa iddah ba duk tsayin lokacin kuwa da suka ɗauka tare, da zarar ya bayyana sakin tana iya yin aurenta ko da ace a daidai wannan gaɓar wani ya zo ya bayyana cewar zai aureta to ana iya ɗaura aurensu anan take insha'Allahu...wannan shi ne taƙaitaccen ba yani a game da tambayar da kika yi, wallahu ta'Ala a'alam"._
gama bayanin nasa yay haɗe da taruwar ruwan hawaye a idon Fillo, a hankali kuma sai taji hawayen su na sakkowa saman kuncinta, ta rumtse ido tare da cije leɓenta na ƙasa ta kifa kanta akan cinyarta, haka ɗaya ba tare da sanin dalili ba taji tana so tayi kuka, irin kukan da zata yi ya isheta, taji zuciyarta na matsewa da wani irin zafi tamkar ana hura wuta, ciwon kan da ta kwana biyu ba ta yi ba ta ziyarce ta, ta kasa danne kukan da ke neman ƴancin fita a bakinta kawai sai ta sake shi, ta miƙe da sauri ta haye upstairs tana jin wani irin wahaltaccen yanayi a tare da ita, tana shiga ɗaki ta faɗa kan gado ruff da ciki, kuka sosai take yi ta rasa ta ɓangaren da zata lallashi kanta.
sai da ta kusa rabin awa tana kukan sannan ta daina, ai kuwa kanta yayi ma ta wani uban nauyi kamar zai faɗo, ta miƙe ta shiga toilet ta yi wanka a daddafe ta fito, ta buɗe wadrobe ta ɗauko doguwar riga ta atamfa ta saka, ta taka stool ta ɗaga ƙasan trolly ta ɗauko takardar sakin, ta zura hijab ɗinta tare da buɗe drower ta ɗebi kuɗi ta saka a jaka, abu biyun nan su kawai take buƙatar tafiya da su, takardar sakinta da zata zama shaida da kuma kuɗin da za su kaita Taraba.
ta zauna bakin gado zuciyarta na karanto ma ta kuskurenta, ita ai duk ɗan guntun ilimin da take da shi ce take sai tayi masa iddah shiyasa har ta yarda ta zo gidansa, ashe yanzu ita kwata-kwata ma ba ta da wata alaƙa da shi, zaman haukarta na rashin iliminta kawai take yi.
abun da ta kasa ganewa shi ne; me yasa ta damu da sakin nan?, me ya sa take jin kamar rabuwa da cikin gidan nan tamkar rabuwa da wani ɓangare ne na jikinta?, abu ɗaya kawai ta san yana rubuce a tafin hannunta, babu wani abu da zai hanata barin gidan nan ayau tun da har ba ta da wata alaƙa da shi, za ta tafi tabarsa nisan tafiya kuwa ta har mutuwa.
sabbin hawaye suka shiga sauko ma ta, taji kamar hayaniya da ga downstairs, bata ta shi ba taci gaba da zamanta tana tunanin ta yanda za'ai ta tafi, ita ba sanin hanya tayi ba, ita ba lambar wayar kowa ba, ba ta taɓa sanin ina ne tasha ba balle ta kai kanta, anya ba zata nemi taimakon Baba me gadi ba?, dan ba zata iya zuwa gidan su Turaki ba.
zuciyarta ta yarje ma ta hakan, dan haka ta miƙe tana ƙara goge hawayen fuskarta ta fita da ga ɗakin tana jin wani baƙin ɗaci a zuciyarta, tana fara sakkowa da ga steps ta hangi Nihal da wasu yara da za su yi sa'anni da ita, kuma kallo ɗaya ta yi musu ta tuna maganar Bello da yayi mata jiya cewar za'a kawo ma ta ƴan aiki, tai saurin komawa yanda ba za su jita ba, ta cire hijab ɗin jikinta ta ajiye tai saurin shiga toilet ta wanke fuskarta da sabulu, tana fitowa taga Nihal a tsaye tana ƙarewa ɗakin kallo.
tayi ƙarfin halin ƙaƙalo murmushi kamar yanda Nihal ɗin ke yi ma ta. cike da zolaya Nihal ta ce da ita,"kai Antynmu ai sai muyi zaton ko honey moon ku ka wuce babu sallama, 1week ba ku leƙa mu ba".
Fillo tai murmushin yaƙe ta tsuguna tana gaida ita.
Nihal ta ce,"kar ki ban kunya don Allah tashi mana, ni ya kamata na tsuguna miki yanzu ai ba ke ba, matar babbar Yaya".
Fillo taja yatsun hannunta ta ce,"Adda Nihal ina Maama da Mum?".
ta ce,"su na kan hanyar zuwa ai, ashe ba ki da lafiya shi Hammah kwata-kwata bai faɗa ba sai yau. ya sauƙin jikin naki?".
Fillo ta ɗago tana kallonta sai kuma ta ce,"naji sauƙi ai".
Nihal ta ce,"kin ga ma yanda ki ka rame kuwa".
buɗar bakin Fillo zata yi magana suka ji shigowar mutum, Nihal ta gaida Turaki tana yi masa sannu da zuwa, bai ko amsa ma ta ba yayi ma ta nuni da hanyar fita ta zo ta wuce tana ɓata fuska, tun da Baffa yay masa gate da gida shikenan ya sauya musu ko magana ba yay musu up to now, sai kace su ne suka hana shi zuwa gidan.
sai da Nihal ta fita tukunna Fillo ta