NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 236 of 323

ya cikin biyun. a kullum babu abin da take kira face mutuwa, ta gaji da wannan wahalar da take sha, jikinta ya fara addababben ƙaiƙayin da shi kaɗai taƙi jin ya tasar mata, ta ɗago hannunta guda ɗaya da ya shanye ya koma tamkar ba'a taɓa halittar tsoka ba ajikinsa, karkarwa kawai yake yi yama ƙi kaiwa inda take so ta sosa ɗin. ta fara rera kuka a hankali, kukan babu daɗin ji, shi ba na mutane ba kuma shi bana dabbobi ba. Ilham ta ɗago ido tana kallonta, ta miƙe tana jin duk duniyar ta isheta, ta sani mahaifiya ta wuce duk inda ake zato, babu me so ya rabu da mahaifiyarsa a kowanne irin hali kuwa, amma ita dai a yanzu zata ce gwara mahaifiyarta ta mutu, ba wai zata ce ta gaji da zaman jinyarta ba ne, but cutuwar da take yi a zamanta tare da ita shi tagaji da shi, a kullum ba tayi amai ba tayi sama da sau biyar. ta ɗauki facemask ta saka sannan ta ɗauki sandar share yana, ta isa gaban gadon tasa sandar tana sosa mata jikinta da ita, saboda ba'a saka hannu wajen sosa ma ta gudun kamuwa da cutar da likitoci suka faɗa, sun tabbatar da cewa duk ranar ruwan ƙurjin ya taɓa jikin wani to shi ma yana iya kamuwa da wanannan cuta ta ƙuraje wadda har yanzu suke bincike akan su. wahaltaccen amai ya tahowa Ilham babu shiri ta jefar da sanda ta fita a ɗakin da gudu ta shiga toilet, amai sosai tayi kamar wacca zata amayar da kayan cikinta, ban da haki babu abin da take yi idanuwanta duk sun yo waje saboda galabaita. ta wanko bakinta ta fito ta tsaya a ƙofar wajen tana sauke numfashi, wucewar daƙiƙa ta fita ta zagayo ta window inda me martaba yake tsayawa duk sanda zai ga Fulani Azima, a yanzu ban da shi da ƴarta babu wanda yake iya zuwa wurinta hatta kuwa da mahaifiyarta, suma ɗin da suke zuwo roƙar ma ta mutuwa suke yi a wajen ubangiji kamar yanda take roƙawa kanta itama. cikin muryar me rauni Ilham ta ce,"Mami don Allah kiyi haƙuri, zan je inci abinci sai in dawo, banda ƙarfi a jikina yanzu duk abin da naci ya dawo". ta faɗa tana kuka. Fulani Azima ta bi ta da kallo hawaye na biyo gefen fuskarta, kullum roƙon Allah take yi ya bata aron dama ko da na lokaci ɗaya ne tayi magana da bakinta ta sawa Ilham albarka ta kuma yi ma ta godiya. su kai ta kallon junansu duk su na tausayin kowannensu, Ilham ta share hawayenta ta bar wajen ta tafi ɓangaren Boɗejo, in da ta dawo da zama gaba ɗaya tun ranar da aka yi sakin Ilham, ta ɗau fushi da Baffa da Hakimi ta ce duk Me martaba shi ya fi son ta da ƙaunarta, kwanciyar Turaki a asibiti ma sai da ta taushi zuciyarta ta iya zuwa, shi ma dan taji ance ya na can rai a hannun Allah. ta shiga parlon da sallama, kana ganin yanda take tafiya kasan damuwa tayi ma ta ƙatutu, ta zauna kusa da Boɗejo wacca ke shan kayan marmari da aka ajiye ma ta a faranti, ta cire hand gloves ɗin da ke hannunta ta wanke acikin ruwan da wata baiwa ta kawo yanzu. sannan ta shiga cin fruites ɗin da Boɗejo ta dawo da shi gabanta. "Sannu Ilham Allah ya yi miki albarka ya ba ki ladan ɗawainiya da mahaifiyarki, ita kuma ya kawo ma ta hanyar hutu, wannan ciwo na ta gwara mutuwa da jinyarsa, shiyasa akace kullum ka roƙo Allah ya rabaka da doguwar jinya". cewar Boɗejo. hawaye na bin kumatun Ilham ta ce,"amin". sannan ta karɓi plate ɗin alkubus da miyar taushe da Boɗejon ta miƙo ma ta. tana ci tana zubar hawaye na tsananin tausayin mahaifiyarta. **** bayan sati ɗaya Fillo ce zaune a parlo tana kallo, tv ɗin da tun da ta tare sai jiya da Bello ya shigo ya sa aka haɗa ma ta ita. kuma sai yanzu ta fara jin daɗin zaman tun da tana ɗebe ma ta kewa, jiya ma tana kallon tayi bacci ba ta sa ni ba sai wajen 12 ta farka ta kashe tv ɗin ta haye sama, tsoron ma da take ji ya fara raguwa, da zarar ta kunna karatun qur'ani shikenan sai tayi baccinta lafiya lau. cikin sati ɗayan nan banda zaman kaɗaici babu abin da ta ke yi, kewar Umminta da Kaka kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, kullum sai taji kamar ta fita ta roƙi me gadi ya ara ma ta wayarsa, sai kuma ta tuna idan ta karɓo babu lambar wanda ta riƙe akanta, lambar Yami ma ta mance balle ta ce zata kira Maijidda ta kawo ma ta lambar Kaka, ita kanta Maijiddar kewarta take yi. babu wani wanda yake leƙo ma ta, ko da ga gidansu Turaki kuwa, tayi tsammanin ganin su Maama ma amma shiru ba su babu su Zaytun, hatta shi Turaki rabonta da ganin inuwarsa ma tun washegari, sau tari tana jin dawowarsa da daddare in an zuge gate ba ta ko leƙan windon balle ta kalli takaici, dan Allah ɗaya ya san adadin haushinsa da take ji a yanzu, kwatakwata bata ƙaunar ma wani abu da zai haɗata da shi, lokaci kawai take jira ta bar masa gidansa. kullum iyakarta da ga sallah sai bacci sai cin abinci haka take fama, fatar nan tata kam ta ƙara yin fresh saboda hutu, kuma duk ta gaji da hakan, sai uwar rama da take yi saboda damuwa da ta sakawa ranta da kuma rashin cin wadataccen abinci. ta ɗau remote ta sauya tasha zuwa africa tv, daidai lokacin da aka hasko marigayi Shaik Albani Zariya yana amsa tambayar wata mat
🏠