NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 235 of 323

a tana barin wajen tare da goge ƙwallar idonta, shi kuma ya bita da kallo yana ta zazzaga ma ta adu'a yana sa ma ta albarka. kai tsaye parking lot ta nufa in da ta ke hango Turaki a wajen motarsa ya buɗe ya shiga ƙafarsa ɗaya a waje, ya ajiye ledar kayan da ya amsa, ɗaya a ƙasa ɗaya a saman murfin booth, ta ƙarasa wajen motar cikin sanɗa ta durƙusa ta kwashi kayanta, ta yi saurin barin wajen kamar za ta kifa ƙasa, fatanta ɗaya ta isa har ƙofar part ɗin ta bai fito da ga cikin motar ba, abin da ba ta sa ni ba shi ne, tana ɗaukar kayan ta juya shi kuma ya fito da ga cikin motar, mamakin ƙarfin hali irin na ta shi ya tsayar da shi kawai yana bin bayanta da kallo, ya kasa yi ma ta magana balle ya cimmata ya karɓe, shi kallon ma da yake yi ma ta tun jiya kamar da akwai abin da takala. ya jijjiga kansa, koma me take ji da shi zai saitata ne within wani ɗan lokaci. bayan sallar azahar tana zaune kan darduma ta zabga uban tagumi sai taji kamar hayaniya a compound, ta miƙe da azama ta leƙa ta window sai taga su Adda Asma'u ne, ai kuwa babu shiri ta wancakalar da hijab ɗin jikinta ta fice da sassarfa me kama da gudu, saura kaɗan ta zame a steps, ta sauko parlon a san da ta ga ana ta shigo da manyan kuloli na abinci ana wucewa da su kitchen, taji Inna Hajar na cewa da masu shigar da kayan,"kar ku saka su da ga in da babu iska kayan gara ne". ta yi tsallen murna da farin ciki ta faɗa jikin Raudha, duk su ma sauran sai suka maƙalƙaleta anata Allah sarki ƴar marainiya, sai kuma aka ɓige da yi ma ta tsiya ana tsokanarta amaryar ƙamshi, har ta fara kumatu, ta harari Maijidda da ke ta kallonta tana murmushi. ta zame da ga wajensu san da Adda Asma da Dadda ke shigowa, ta tafi da sauri ta faɗa jikin Dadda, sai ga hawaye kamar da ma jiran ganinta su ke. Adda Asma ta ce,"yau naga tsiya, to in dai kuka za ki yi kam sai mu juya". ta yi saurin goge hawayen tana faɗin,"ku yi haƙuri Adda Asma na daina". ƙememe Adda Asma ta hana su Raudha zuwa bedroom ɗin Fillo, kamar ta san gulma ce zata kaisu, ta ce wallah duk wanda ya kuskura yaje ma ta ɗaki sai ta ɓata masa. ita dai Fillo ba ta ce komai ba, daɗi duk ya isheta saboda ganin ƴan uwanta, ji take kamar kar lokacin tafiyarsu ya yi, Dadda tasa su Raudha suka shiga kitchen ɗinta su ka ƙara gyara ma ta shi da cikin store, su kuma suka haura sama zuwa bedroom ɗinta, wasu kayan da aka zazzo ma ta da shi aka ƙara kimtsa ma ta su, da aiken Dada da ta bayar a ƙawo ma ta, sannan su ukun duk suka zauna suka ƙara yi ma ta ƴan nasihohi da ba'a taɓa daina yiwa ƴa mace in har an aurar da ita. a parlo suka zauna akai ta hira har akai sallar magriba tukunna suka yi haramar tafiya, Fillo ta riƙe Maijidda akan lallai ba zata tafi ba, ta rakosu compound tana ta kuka irin na jiya. bata ƙara jin kewarsu ba sai da magriba ta yi, lokacin ne kuma ta fara jin yunwa ta shiga kitchen, ta buɗe freezer taga babban botiki na miya da su ka zo ma ta da shi ɗazu, ta ɗauko flask ɗin da Inna Hajar ta faɗa ma ta akwai ferfesun kifi a ciki, ta zuba kaɗan ba da yawa ba, ta buɗe oven ta ɗauko gasassan biredi, sai dai ko da ta zauna sai taji kasa ci, dole haka tasa hijab ta fita ta kaiwa Baba me gadi. tana zaune a parlo har akayi sallar isha'i, a lokacin tsoro ya fara kamata, tayi azamar barin parlon ta koma upstairs ta kulle ɗaki, ta dunƙule akan gado tare da toshe kunnuwa dan sam ko ƙarar AC bata son ji, kamar dai yanda ta kwana jiya ita ɗaya haka yauma ta kwana ita ɗaya, cike da tsoro fal kamar zuciyarta zata bar ƙirjinta. *Masarauta Kaltungo.* wani mugun ɗoyi ne ke tashi a cikin turakar ta Fulani Azima, tana can da ga kusurwar ɗakin an kwantar da ita akan gado, ba ma lallai ka lura mutum ba ne idan ka shigo, halittarta tayi mugun muni kamar ba wannan macen ƴar gayu da ƙwalisa ba, me ji da mulkinta da kuma girman izzarta. idanuwan da suka firfito waje kamar na ƙwarangwal sai kallon Ilham take yi wacce ke durƙushe da ga can bakin ƙofa, tayi tagumi tayi nisa acikin tunani, taji bala'in tausayin yar tata ya kamata, ta sa ni alhakin mutane da dama da ta ɗauka ba lallai ya bar ɗiyarta taji daɗin zaman gidan aure ba, ko me ya faru da ita ta san ita ta janyo ma ta, ga shi ba ta da bakin maganar da zata nemi yafiyar mutanen da ta cuta su yafe ma ta ko ta samu sauƙin wahalar da take ciki, ƴarta ma ta samu hutu. ta san babban alhakin wanda ke bibiyarta ita ce Hajiya Ramla, domin ita ta yiwa cutarwa mafi munin zalunci, kuma yanzu a cikin tsoro take matuƙa ma kuwa, domin hausawa sun ce ka guji shirun wanda ka zalunta, shirun da Hajiya Ramla tayi har yanzu yana matuƙar ɗaga hankalinta, yana tsoratata, gani take kamar shirun nata shi ke ƙara shigarta wannan matsanancin halin da take ciki, kuma kamar tana shirya ma ta wani abu ne da zai ƙara jefata halin da yafi wannan da take ciki, domin ta san babu wanda zai san kayi masa cutarwa irin wannan ya ƙyaleka, ko da ace ya yafe maka to dole zai tona maka asiri, amma ita babu ɗa
🏠