.
ba wai yana yin yunwa ba ne, a'a kawai ba zai iya ƙin tayan da tayi masa ba, dan sosai shi dai yake bala'in tausayinta.
ta wuce cikin sauri ta ɗau mug anan kan ƙaton family dining table ɗin, ta cika shi da ruwan tea sannan ta ɗauki plate ɗin da ta zuba irish da miyar hanta taje ta kai masa, shi ya tayata janyo center table gabansa dan yaga kamar mug da plate ɗin da ke hannunta su na neman rinjiyar waɗannan sillan karan hannayen nata, kar yaje ata dalilinsa ƙashin yar mutane ya karye.
ta na kallon carpet ta ce masa,"nescafe ɗin ne dai babu sai na bayar an siyo, kuma mai gadi ya fita bai dawo ba".
da mamaki Bello ya ce,"sai an siyo?".
ta ɗaga masa kai kawai tana sa hannu ta goge hawayenta. yay ta kallonta da mugun tausayinta ya ce,"kuma kin duba ko'ina a kitchen ɗin babu?".
ta yi shiru, sai taji ya ƙara cewa,"tsaya tukunna!, faɗa min gaskiya kar ki ɓoye min komai, ke ɗaya kika kwana a nan ko?".
da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. yay guntun murmushi na takaici ya ce,"karki rufawa MT asiri, ɗan banza ne bai da hankali ko kaɗan, tunaninsa ba irin na mutane ba ne, gwara ma ki fayyace min komai dan ko kin ɓoye min shi ba zai ɓoye min ba. ki faɗan gaskiyar amsar tambayar da nayi miki".
hawaye su ka ƙara zubo ma ta bata ce da shi komai ba, a wannan hawayen ya karanto duk wata amsar tambaya da yake son yi ma ta.
ya sosa girarsa yana tunanin ta yacca zai shawo kan wannan lamarin, tun jiya yake tunanin ta yan da zai yi convincing Turaki akan ya mayar da aurensu, shikenan su zauna lafiya salin alin babu wanda ya san anyi, to amma ya san shegiyar gardama da rashin ɗaukar shawara irin tasa ba lallai ya amince ba, shi abun da yake gudu ma kar silar zaman nata a gidan azo a aikata kwaɓa, yay guntun tsoki ya ƙara trying lambar Turaki amma bai samu ba.
ya ce da ita,"ƙofar tsakiyar nan anan kitchen ya ke, ki kawo min nescafe ɗin".
sai ta juya tana kallon ƙofar da ta buɗe ta shiga ɗa zu har tafi ƙarfin minti uku tsaye aciki, ta ƙara juyo da kanta gare shi ta ce,"babu ai kitchen ɗa zu duk na duba".
yay gajeran murmushi ya ce,"ai na za ki dinƙa girki idan babu kitchen?, ko kin taɓa ganin gida babu kitchen?".
ta ce,"a'a ƙila haɗe mana ya yi da ita, anjima na ke son zuwa part ɗin nata".
Bello ya kaɗa kai,"kina uwar gidan zai tafi bangaren wata ya yi kitchen?, to ba haka ba ne, kowaccenku da nata kitchen ɗin, duba in da na faɗa miki".
ba ta iya jayayya da Babba ba, amma ita ta san babu wani kitchen, ta tashi taje ta buɗe parlon, yana ta kallonta a san da ta shiga ta tsaya da ga bakin ƙofar, yay smiling ya ce ta buɗe ƙofar ciki, ta ƙarasa shiga ciki ta isa wa ta ƙofa da ta gani ta buɗe, jimawa kaɗan sai gata ta dawo riƙe da ƙaton gwangwani na nescafe, ta ajiye masa ta koma dining ta zauna, yana shan ruwan tea ɗin yana ɗan janta da hira sama-sama, har da tsokanarta wai an bata award na amaryar da tafi kowacce amarya kyau tun da aka fara aure a nigeria.
ita dai murmushi kawai take yi, kuma sai taji hirar tasa na yi mata daɗi musamman da yana bata labarin yarintarsu, irin yanda suke faɗa akai akai kamar ƴan tsaki, da yacca Baffa ke cin ƙaniyarsu, har ya ce yana basu purnishment ɗin yin dariya da haƙori ɗaya ko su ciji hancinsu in ba haka ba a dafa su a bawa mage ta cinye, sai suyi ta kuka su na bada haƙori in Baffa yaƙi haƙura sai su ɓuya a lambu, sun sha kwana acan yafi a ƙirga saboda basa son faɗan Baffa da dukansa ko kaɗan.
sai ta sami kanta da yin dariya sosai, sai da ya ɗeba ma ta kewa tukunna yay ma ta sallama ya tafi, bayan tafiyar tasa duk sai taji babu daɗi, ta dawo ta koma upstairs tai kwanta zuciyarta cike da son ganinta a gida, yanzu ta san su Dadda sun ɗau hanya, tana ta so ta yi waya da Umminta taji muryarta, tun da ta tashi take mugun kewarta.
ban da tunane tunane babu abin da takeyi har ƙarfe goma, sai lokacin ta tuna da aiken da ta bawa Baba, hakan yasa tayi saurin saukowa ta fita, tana fitowar kuwa ta tarar da Baba me gadi yana isowa entrance na ɓangarenta, ta tafi da sauri dan karɓar masa kayan, sai dai kamin ta ƙarasa Turaki ya rigata, ta ƙaraso wajen Baban a sanda Turaki ke miƙa masa hannu alama na ya ba shi kayan ba tare da ya ce masa komai ba.
Fillo ta haɗe rai kamar ba ita ba, ko kallon in da inuwarsa take bata yi balle kuma shi kansa, tana yiwa Baba sannu da zuwa ta miƙa hannu za ta karɓi kayan taji saukar muryar Turaki a tsakiyar kanta.
"idan har kayan nan suka je hannunta, to ka nemi wani gidan ka ci gaba da aikinka".
ta dakata da karɓar ledar tana kallon hannun Baba da ke aikin karkarwa, taji mugun tausayinsa ya kamata, tana kallo ya kalleta fuskarsa nayi ma ta nuni da tayi haƙuri ta rufa masa asiri, ta gyaɗa kanta kawai shi kuma ya bawa Turaki ledojin, ya karɓa ya juya ya bar wajen, itama zata bar wajen Baban ya ce,"Hajiya ga canjin ki".
ta waigo tana yi masa murmushi ta ce,"ka riƙe Baba".
ya waro ido waje yana cewa,"dubu biyar ce fa Hajiya". ta ce,"babu komai Baba". ta faɗ