i ta shiga laluben ƙofar kitchen, ƙofofi uku duk sai da ta buɗe, kuma dukansu bedroom ne sai 1 parlo wanda yake shi ne a middle, cikin sanyin jiki ta rufo ƙofar, kenan ita babu kitchen a part ɗin ta?, haɗe musu yay kenan su yi shairing guda ɗaya?, kenan duk wannan uban kayan kitchen ɗin da taga an siya su na can an haɗe su tare da na Ilham?, abun da ake nufi har in zata ci abinci sai taje part ɗin Ilham sannan zata dafa?, ashe kuwa an so yunwa ta kasheta, dan wallahi in har dan sai taje part ɗin Ilham ne zata dafa abin da zata ci, to gwara tayi ta zama a haka har yunwar ta gaji da damƙarta ta kasheta.
bakinta ya suɓuce da tsakin da ba ta san dalilin yinsa ba, ta koma upstairs ta buɗe jakar da Dadda ta ce an ajiye ma ta kuɗi, ta zaro 10k, hijab ta ɗauka ta sa ta fito ta sa mu mai gadi, ta durƙusa har ƙasa ta gaisar da shi yana amsawa da fara'a tare da saka ma ta albarka. sai taji nauyinsa, ba ta jin zata iya aikensa dan ya haifeta, idan bai girmi Abbanta ba tabbas za su yi sa'anni, ta yi shiru tana juya kuɗin a hannunta har sai da ya katse shirun na ta da cewa,"da akwai abunda ki ke buƙata ne?".
ta ce,"Baba don Allah ko za'a sami almajiri a waje?".
ya ce,"aike ne?".
ta ce,"ehh Baba". ta faɗa kanta na ƙasa.
kamar kuwa yanda zuciyarta ke raya ma ta taji ya ce,"ai kin san layin namu babu almajirai, sai dai ki kawo bari naje na siyo".
ta na girgiza kai ta ce,"a'a Baba ka bar shi ba zan iya baka aike ba gaskiya".
yay murmushi yana jin har ransa ta burgesa, da kuma yabawa da tarbiyarta da hankalinta, ya tuno san da Ilham tana nan, a rana ba'a aike shi ba a aike shi sau uku, kuma a gadarance da nuna isar mulki.
"kawo ƴata babu komai ai sai aje a siyo miki, ai ba aikena kika yi ba, a matsayina na uba zan fita siyo miki abun da ƴata take buƙata saboda kare darajar aurenta".
ta ɗago ido tana kallonsa, taji tausayinsa sosai a cikin ranta, ta miƙa masa kuɗin ta ce,"na gode Baba. da ma golden morn za'a siyo min babban ledan, sai madara na gwangwani babba, sai sugar rabin kwano, sai cornflask kwali biyu. za su isa kuɗin ko Baba?".
zai ƙirga kuɗin ta ce,"dubu goma ne ban san yanda kuɗin na su yake ba".
ya ce,"ehh tou nima gaskiya ban san yanda kuɗin yake ba, amma yanda za'a yi, bara idan naje in akwai ciko sai na karɓo miki lambar akawunt ɗinsa sai ki tura masa tunda da ma mun saba da shi, nima na kan yiwa iyali cefane acan".
tayi ɗan jimm kafin ta ce,"bara dai na ƙaro in ya zama da sauran canji ko ma sun kai shikenan".
ta faɗa masa hakan tunawa da tayi bata da waya balle wani account.
5k ta ƙaro, ta ba shi ta ce ya yi har na mota, dan indai ba'a tafiyarta ba tasan layin nan nasu kaf babu wani kanti.
da ga fitowarta ta farko, da komawar da tayi ta ƙara fitowa duk a idon Turaki da ke tsaye a balcony na sama, hannunsa riƙe da mug da alama tea yake sha, ya bita da kallo san da ta koma ciki yana ji zuciyarsa na ƙirga masa girman laifin da ta aikata.
sai bayan ta shiga kuma kawai sai idonta ya sauka acan dining area, adon wurin ya yi bala'in burgeta hakan yasa ta tafi, tana zuwa ta tarar da manyan warmcoolers na abinci guda huɗu da babban tea flask, tana kallonsu ta shaida su, coolers ɗin kitchen ɗin Maama ne da sai Baffa yana nan kawai ake amfani da su.
ta buɗe ƙaramin coolern taga irish ne da miyar hanta da soyayyan ƙwai, ƙamshin ya ziyarci hancinta har sai da ta lumshe ido, ai ko bata jin yunwa sai taci balle kuma uwar yunwa na ƙwazafarta a ciki, mamakinta ɗaya ne da yaushe aka kawo abincin?, zuciyarta ta faɗa mata tana can tana bacci.
ta ɗauko plate ta fara zuba abinci sai taji ana knocking, adu'arta ɗaya ne a lokacin Allah yasa su Dadda ne suka zo, ta miƙe da sauri taje ta buɗe door sannan ta zuge glass, idanuwanta suka sauka akan Bello da ke tsaye hannunsa ɗaya a aljihu ɗaya kuma yana maƙale da waya a kunnensa.
taja da ba ya tana ba shi hanya tare da yi masa sannu da zuwa, ya shigo yayin da yake amsawa, ya wuce ya zauna kan kujera ita kuma ta durƙusa har ƙasa ta gaida shi, ya amsa ya ɗan kallonta da son fahimtar wani abu, sai dai ya gagara fahimtar komai ɗin.
tana tsugune tana jan yatsun hannunta har wucewar daƙiƙa biyu sannan ya kalleta ya girgiza kai ya ce,"MT bai ta shi ba ne?".
tai ɗan jimm tana nazari, kamar ta ce bai tashi ba kamar kuma ta ce masa ya fita, a wannan shirun na ta Bello ya samu amsar tambayarsa, tausayin yarinya ya kama shi, a irin hallacin da tayi masa sam sam ba ta kamaci wani abu wulaƙanci a wurin Turaki ba balle tozarci, dan babu tozararci irin sakin da ya yi mata tana ƙarama da ita, ya miƙe yana cewa da ita,"idan ya dawo kice masa nazo, ina ta kiran wayarsa bata shiga ya yi ƙoƙarin kirana".
ta amsa da,"toh". sannan ta ce,"ba ka sha ruwa ba, ga tea zan kawo maka". bai kalleta ba amma yanda voice ɗin ta ya fito ya tabbatar ruwan hawaye sun cika idanuwanta, kuma so ta ke ta zubar da su, ya sauke numfashi ya koma ya zauna tare da cewa,"oak kawo min tea kawai, kisa nescafe idan ba takurawa"