NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 232 of 323

ta jiyo ƙarar rufe ƙofar parlon ƙasa, sai kuma ta dinƙa jiyo hayaniyarsu a compound suna shiga mota an buɗe musu gate sun fita. ƙarar zuge gate ya haɗe da bayyanar wani bala'in tsoro a ƙirjinta, tayi saurin tashi ta isa window ta leƙa, karaf idonta ya sauka akan Turaki da yake fitowa daga mota, tana kallo ya ɗau wata hanyar ta daban ba nata part ɗin ba, sai kawai taji saukar sabbin hawaye a saman kuncinta masu zafi kamar zasu ƙona fatarta, ta ƙara komawa ɗaya windown ta hangesa ya buɗe part ɗin da yake na Ilham ya shige, tana kallo ya zuge glass door na entrance din parlon, sai taji kamar ya haɗa da zuciyarta wajen rufewa ya datse. a hankali ta sulale a wajen tana rushewa da kukan da zata ce bata taɓa yin irinsa ba, yanzu ita ɗaya zata kwana a wannan ƙaton wajen?, tabi tangamemen bedroom ɗin da kallo, tsoro na masifa ya ƙara kamata, me yasa ma tayi wannan haukar na bari a kawota cikin gidan nan alhalin ba zaman aure zata yi ba zaman iddah zata yi?, ta jima zaune tana ta uban kuka har kusan ƙarfe biyu sannan ta miƙe ta shiga toilet tayi alwala tazo tayi sallah, sai bayan ta idar take jin wani irin loneliness da kuma wani irin tsoro na daban, tayi saurin barin kan dardumar ta haye kan gado ta ƙudundune a waje ɗaya, ƙarshe ɓarawon bacci ne ya ɗauketa. *Comment, Share and Vote.* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *47* kirayen sallar asuba ya farkar da Fillo da ga bacci, ta buɗe idanuwanta a hankali, tana miƙewa zaune aka ɗauke wuta, babu shiri ta koma ta ƙara dunƙelewa, har sai da taji masallaci na sallamewa da ga sallah tukunna ta ƙara buɗe fuskarta tana leƙowa, farko duhu ta gani sai kuma ta ga haske ya gauraye ɗakin. da ƙyar ta iya sakkowa kamar me tsoron taka tiles ɗin, alwalar ma kanta ɗaiɗai ta yi saboda tsoron toilet ɗin, ta fito ta isa kan dardumar da ta bari a shimfiɗe tun sallar daren da tayi. zata tayar da sallah taji kamar an buɗe gate, jikin windo ɗin ta isa ta ɗa ga labulen tana hangen bakin gate da mai gadi ke mayar da ƙofa ya rufe, kafin idonta ya manne akan Turaki da yake tafiya zuwa in da taga ya nufa jiya wanda ta tabbatar nan ne part ɗin Ilham ne, dubai jallabiya ce a jikinsa dark blue, sai carbi da yake hannunsa yana ja, a yanzu ma da ya zuge glass door sai taji kamar ya datse da zuciyarta, idonta ya ciko da ruwan hawaye sai dai ba ta basu damar zubowa ba, a hankali ta din ga bin tazarar da ke tsakanin part ɗin na su, cikin kanta tana jin kamar ƙwaƙwalwarta na couting ma ta nisan interval ɗin da ke tsakanin part ɗin na su, tazara ce sosai amma sai take ganin kamar tazarar daidai take da tazarar yatsun hannunta. jikinta taji gaba ɗaya ya saɓule, ta koma kan sallayar ta tayar da sallah, ta jima tana jero adu'oi a san da ta idar, haka kawai taji zuciyarta na raya ma ta kamar Turaki zai mayar da aurensu, ta yi saurin girgiza kanta, it can never be possible ta san da hakan, yanda ya ke da muguwar zuciya ta sa ni ko da wuri ɗaya zasu ke kwana su na tashi ba zai taɓa mai da auren ba, kuma itama ba ta jin ko da ya mayar da auren za ta yar da ta zauna da shi, ai yanzun ma zama kawai take yi da zarar ta gama iddah zata bar masa gidansa, bari kuwa na har gaban abada. ka sa ta shi ta yi ta koma kan gadon, kawai sai ta kwanta nan kan darduma jikinta tana jin duk yana yi ma ta ciwo, hawayen da take ta danne zubarsu taji sun gangaro, muryar Ummi kawai take son ji, ita kawai take son gani. cikin kanta taji na karanta ma ta yanzu ita ɗaya zata yi ta zama haka kamar mayya?, to ai ko wannan bedroom ɗin ya yi ma ta girma da zama ita ɗaya balle wawakeken part ɗin na ta da taji ana ta faɗarsa tun a jiya da su Arɗo su ka dawo daga jere, anya kuwa zata iya ci gaba da wannan zaman da zuciyarta ta tsara ma ta?, ba zata falllasa komai ba kuwa?, kamar fa hauka ne take yi hakan!, ita abin da ba ta so shi ne ƴar ƙaramarta da ita ace wai tana zaman iddah a gidansu, to wanne irin kallo za'a koma yi ma ta?, wanne kalar tunani za su koma yiwa silar rabuwar auren?. sai kawai taji kuka ya taho ma ta sosai, tasa hannu ta toshe bakin kamar akwai wanda ya ke kusa da ita ba ta so ya ji, ita dai ba zata iya wannan zaman ba, gwara ta yi tafiyarta kawai, ko kuma ta kira Ummi ta faɗa ma ta a kawo Sumayya ta tayata zama, Sumayya ƙanwarta ƴar matar Hayyo da har ya mutu da ita ɗaya ce ba su rabu ba, ko kuma ta cewa Maijidda ta dawo nan ɗin?, to ai in har ta faɗawa Maijidda kamar ta kai takardar sakinta ne gaban Dada. da waɗannan lissafin tunanin bacci ya ɗauketa, ƙarfe takwas yunwa ta farkar da ita, hasken ranar da ya ratso ta windon ɗakin yasa hankalinta kwanciya, tsoron ya bar jikinta. tana ta shi ta gyara kan gado, sannan ta shiga toilet tayi wanka, ta daɗe a toilet ɗin kafin ta fito, ɗaya da ga cikin lotions da aka jere ma ta akan dressing mirror ta ɗauka ta shafa, ta shafa farar powder tasa lip balm, sannan ta saka abaya baƙa, ramar da ta yi sai ta ƙara yin kyau sosai acikin kayan. tana sakkowa downstairs sa
🏠