NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 231 of 323

akan ba dan sam bata so yaga weakness ɗinta a yau balle ya alƙanta hakan da zafin sakin da yay ma ta. ta kafe ƙunshin hannunta da kallo tana jin ƙaguwar su tafi aje ayi ayi a gama taron ta daina ganinsa a kusa da ita. da ga Bello dake driving har su kowa zuciyarsa a cunkushe take, Maijidda ce kawai da bata san damuwar komai ba take jin zuciyarta wasai sai kallon titi takeyi, Bello kuwa bini-bini sai ya daki stearing yana jan dogon tsaki. can da tafiya tayi nisa Fillo taji kallon dake jikinta ya yi yawa ta ɗago ido, karaf ƙwayar idonsu ta tsarƙe ata juna, tasha murr fiye da yanda ya haɗe tasa fuskar, kwatakwata ba ta san lokacin da bakinta ya suɓuce da faɗin,"kana da buƙatar ƙara sanin addini da kyau, domin na lura sam baka san yanda shari'ar musulunci ke tafiya ba". tayi maganar a ƙasa yanda su Bello da ke gaba ba zasu ji ba. Turaki ya dinƙa kallonta da mamaki tsantsa, kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce da ita,"kin fini buƙatar komawa makaranta ke da kika kasa ba da takardar sallamar da aka ba ki". ya faɗa daidai da isowar motarsu event center, suka yi parking a bakin ƙofar shiga gurin sannan suka yi zaman su a mota, Bello bai ko waiga ya kalli Turaki ba balle yay masa magana, ya fita ya tsaya jikin motar sai jera uban tsaki yake yi. sai da duk mutane suka gama shiga cikin hall sannan aka zo aka fito da Turaki da Fillo, Bello ya yi gefe abinsa kamar bai da wata alaƙa da Turaki, aka zagayo da Fillo side ɗin da Turaki yake nan da nan sai ruwan camera akansu, ƙememe suka ƙi riƙe hannun juna duk da ɓata ran da Anty Rahinatu(ƙanwar Mum) ta nuna musu, suka jera kamar ƴan ƙauyen ƙayayau. su Amatullah da suka zama ƙawayen Fillo su ne suka fara shiga a layi na hannun dama da ga nan sai iyayen gayyar a tsakiya, sannan abokan ango da Turaki bai sa a inda Bello ya kawoso su ba suka ja nasu layin a gefen hagu, abin dai gwanin burgewa, ba zaka taɓa kallon fuskar Turaki da Fillo ba kayi zaton ransu a ɓace yake, ko damuwa, hakan yasa duk hoton da aka ɗauke su sai sunyi kyau, ita dai tayi ƴar ƙarama a kusa da shi dan ita kanta sai nauyi take ji. su na ɗora ƙafafunsu akan step na shiga hall ɗin MC ya fara sanar da shigowarsu, kowa ya miƙe tsaye kamar an ce wasu masu mulkin nigeria ne za su shigo. ƙafafun Turaki da na Fillo suka shiga hall ɗin a tare, abokai kuma na take musu baya, cameras suka shiga ɗaukan su ta kowanne angle, me video coverage na ɗauka tun da ga kan takalmansu har zuwa kan fuskarsu. taro dai ya tafi a bisa tsari kamar yanda iyayen ango suka so ya kasance, yanda Bello ya zo ya yi baiograph haka AmaturRahman tazo tayi biograph na Fillo, anci an sha an bar abinci, biki dai kamar da ma an jima ana shirya masa dan sosai sisters ɗin Fillo suka dinƙa rawa, tashin kiɗa a wajenan kace bayyanar dujal, su dai waɗanda ake abin dominsu suna tsaye ƙyam kamar gumaka, gwara Fillon ma na ɗan murmusawa mussaman da ta ga cousin sisters ɗin suna ta shan rawa abin su, ruwan kuɗin liƙi kamar ba'a talauci a nigeria. Dada da Hajiya Madina kuwa watsa kuɗi kawai suke yi kamar babu talakan da ke buƙatarsu a duniya, har hannayensu sai da suka fara ciwo, rawa kuwa ba ka ce da jikinsu su ke yi ba, Dada sanda ta suɓuce zata faɗi akai saurin tarota, amma a haka taci gaba, ita kanta Maama har sai da Khalil yaji haushi yazo ya janyeta, tazo tana rawa ta manta gaban ƴaƴa take da abokan ƴaƴa. sai a ƙarshen taro Fillo ta yanka cake ɗin da Turaki ko kallonsa bai yi ba, kuma babu wanda ya lura da hakan banda Bello da ke kallonsa yana jin kamar ya rufe shi da duka, Hajiya Sajida Yayar Hajiya Ramla ita ta rufe taro da adu'a sannan aka tashi. lokacin da aka tashi ƙarfe goma sha biyu, direct daga nan aka wuce da Fillo gidan mijinta. su na zuwa Dadda tasa tayi wanka sharp sharp aka ƙara shiryata cikin wani ɗinkin atamfa na riga da zani, aka ɗora ma ta sabuwar alkyabba ba irin wacca aka zo da ita ba fara ƙal me arnen kyau, a gurguje suka ƙara yi mata nasiha daga bisani kuma suka yi ma ta sallama suka tafi, tare da shaida ma ta zasu zo gobe kafin su wuce in dai Dada bata hana su zuwa ba. Adda Asma ta kalli su Raudha da suka wani maƙale ma ta ta ce,"sai ku tashi mu tafi ko". kusan duk a tare suka miƙe su na rataya jakunkunansu, Fillo ta kamo hannun Maijidda, ta ɗage hular alkyabbar da aka rufeta da ita, ta kallesu duk su biyar ɗin, Amatullah, Amaturrahman, Raudha, Maijidda, Khairat, da kumburarrun idanunta cikin sanyin murya ta ce,"yanzu tafiya za ku yi ku barni ni kaɗai?, ku zauna tare da ni don Allah". Khairat ta ce,"mu barki ke ɗaya ko mu barki ke da angonki?, gulmammiya rabonki da azababben kukanki tun jiya da kika ji za'a kawo ki gidan miji yau". Raudha ta ce,"bar ƴar ƙaniya za ta wani marairaice mana ba". Maijidda ta ce,"rabu da su zanke zuwa ina ganinki kinji Hussainata". Dadda ta sake ƙwala musu kira dan haka suka fice da sauri su na ƙara yi ma ta sallama da yi ma ta tsiya. tana jiyo takun su a sanda suka sauka daga bene,
🏠