NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 23 of 323

ar. "sai me kake da buƙata Yallaɓai?". Ƙafafun Kaka a ƙasa lokacin da ta ke tambayar tasa. ya ɗan rufe ido yana jin tausayin tsohuwar a ransa, tukunna ya buɗe yana kallonta ta wutsiyar ido yace,"babu komai, kije ki huta haka don Allah". tace,"to Allah ubangiji ya ƙara maka lafiya, ina bayan kitchen idan da buƙatar wani abu". Tana faɗin hakan ta miƙe zata bar wajen, har tayi tattaki zata nufa kitchen ta fita ta baya sai ya dakatar da ita, tsawon kwanaki shidan da tayi a wurinsa sai jiya ya san sunanta a bakin Maama. "Kaka". ta juyo idanuwanta a ƙasa, tun ranar daya dawo ta dawo aiki ɓangaren, ita ta ke ta lura da shi da ciwonsa, yana ganin ƙoƙarin tsohuwar sosai, yana jin tausayinta matuƙa a cikin ransa, sai dai bai taɓa jin tausayinta da yawa haka ba sai a yau da yake kallon fuskarta me bayyane da damuwar dake cikin ranta. kullum zuciyarsa na gaya masa tsohuwar kamar wannan bata samun hutun rayuwa, to ina ƴaƴanta?, waye a ƙarƙashin kulawarta da ta kasa samarwa kanta hutu a wannan shekarun nata?. Sai dai tambayar dake zuciyarsa yanzu damuwar dake fuskarta ta mene?, ya ƙara ɗaga ido ya kalleta, tana tsaye har yanzu bata motsa ba, ji yake kamar ya tambayeta menene matsalarta amma sai yaga wannan ba huruminsa ba ne. Saboda haka sai yace,"Kaka tunda yau na sami sauƙi kije kawai ki huta kema". Har yanzu kan Kaka a ƙasa tace,"to yallaɓai". ta faɗa tana sake juyawa ta nufi hanyar kitchen. Kamar bata fahimci me yake son ce mata ba. "Kaka ina nufin ki tafi ki huta sosai". tace,"Yallaɓai ai kar na tafi kuma wata buƙatar ta tashi". Kamin yayi magana sai ga Zaytuna ta shigo, ta wuce inda yake zaune tana kara masa waya a kunnensa, ya maida hankali ga wayar ita kuma tace da Kaka. "ki tafi ɗin kawai babu matsala, zan zauna da shi". da yake taji last conversation ɗinsu kamin shigowanta parlon gaba ɗaya. Kaka tace,"to Zaytuna na gode, Allah ya ƙara masa lafiya. Kya sanar da Hajiyar". "tom shikenan babu matsala". Da hakan Kaka ta bar wajen. daga ɓangaren Bello Ƙaraye dake magana ta cikin wayar Turaki yace,"all this while ina ka bar wayanka, i have been calling tana ta ringing ba kai picking ba". Zaytuna ta sauke cup ɗin tea daga bakinsa, bayan ya haɗiye tea ɗin daya kurɓa ya amsawa Bello da cewan,"Maama ce ta ɗauke wayan wai na samu na huta da kiran da ake mani, i though ma tayi switch off nata ashe kunne ta barta". Bello yace,"anyway, how are you feeling now?". Cikin sanyin jiki yace,"Alhamdulillah". Bello yace,"hope kana iya cin abinci yanzu ko?". Yace,"yanzu haka ma am taking tea". Bello ya ƙara cewa,"Good, batun drugs fa?". Yay tambaya cike da concern. Turaki yay ɗan jim yana tuna yanda Maama tayi ta fama da shi akan shan magani ɗazu da safe. jin shirunsa Bello yace,"i know, ba za'a sami matsala da kai ba a ko'ina sai a ɓangaren shan magani...you should have grow up by now gaskiya". Turaki yace,"ka kira ka gaya min magana ne na kashe wayana?". "yo tsakani da Allah ace ka girma amma kana gudun magani da Allura". "ina ce ciwon jikina yake ko?". "ai kuma da yake mun damu da kai...by the way zan shigo cikin satin nan". "Allah ya kawo ka". Bello yace,"ameen, Allah ya ƙara lafiya...and please ka dinga kulawa kaji" Turaki ya amsa mishi,"toh". Sallama Bello yyi masa ya katse wayar, ba'a ɗau lokaci ba Maama ta shigo parlon. *Kuyi haƙuri da rashin update akan lokaci da kuma typing kaɗan. Rashin nepa ne ke damun ƙauyenmu, amma ku taimako da kuɗin solar kunji ƴan albarka☹️* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *8* Idanuwan Turaki da Zaytuna suka ware akan Maama da ta shigo fuska babu yabo babu fallasa, suka bita da kallo har ta zauna kan kujera ta harɗe ƙafafu tana girgiza su. Dukansu suka sauke numfashi mai nauyi dan sun san tunda suka kalla fuskarta a haka to lallai akwai damuwa. "ɗauki wayar nan ki kira min Bello". Muryan Hajiya Madina ta fito da wani irin amon sauti. Zaytuna ta ɗauki wayar Turaki dake kan cinyarsa, tabi kiran Bello da suka gama waya da Turaki babu jimawa. ta miƙe ta isa ga kujerar da ta ke ta bata wayar, a kiran farko bai picking ba sai ana biyu, shima sai daya kusa katsewa tukunna. Daga ɓangaren Bello yace,"Turaki ya dai?". Hajiya Madina ta numfasa tace,"Bello ba shi ba ne". Jin muryarta yay saurin gyara zama daga inda yake, ya gyara yanayin muryarsa, cike da ladabi ya gaisheta, ta amsa masa tare da tambayarsa ya aiki, yace mata aiki alhamdulillah. Shiru na ƴan sakanni ya biyo baya, Turaki dai kallonta kawai yake, kiran Bello da tayi na menene?, me zata ce da shi?, to me ya faru ma tukunna?, dan yanayin fuskarta kaɗai yana shaida cewar there most be something behind. "kana jina Bello?". ta faɗa a sanda ta ke yiwa Zaytuna nuni da dining area, inda a lokacin Zaytuna ta miƙe ta isa wurin dining ɗin, ta ɗauki cup ta tsiyaya watermelon juice aciki, ta ajiye jug ɗin sannan ta dawo ta miƙawa Maama. "ina jinki Maama". lemun dake hannunta ta
🏠