NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 229 of 323

ar ta buɗe toilet ɗin ta shiga ta fito da ita, ta bi su Maijidda da duk suke kwance kan gado suna ta baccin gajiya, dan ba su tashi a event ba sai 11 na dare, kuma suka dawo gida suka ƙara ɗorawa da wani ba su suka kwanta ba sai 3, shiyasa sallar asuba ma duk da ƙyar suka yi. Ummi ta zaunar da ita akan darduma ta ɗauko Alqur'ani ta bata ta ce,"kiyi ta karantawa za ki ji sauƙin koma me ke damunki. tun da dai ni da nake mahaifiyarki ma ban isa ki faɗa min matsalar da ke damunkin ba, to ga maganin kowacce kalar damuwa nan ki ta karatu, ƙarfe sha ɗaya naji Dada na batun jirginku zai tashi". Fillo dai kallonta kawai take yi, har Ummi zata fita sai kuma ta ƙara cewa da ita,"in ma kina tsoron faruwar wani abu ne a auren naku ki yi ta ambaton innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, Allah zai sanya komai ya zamo mafi alkhairi a gare ki, ni dai har zuciyata bana jin komai a game da tarewar nan taki ba, kullum adu'a nake ina faɗawa ubangiji, kuma na gamsu da son da yaron nan yace yana yi miki". Ummi ta fita ta barta, ita kuma ta buɗe suratul Yusuf ta shiga karantawa, kamar almara sai ta fara jin duk wata damuwa da fargaba da komai yana tafiya yana barinta. ƙarfe takwas Ummi ta dawo ɗakin, hannunta riƙe da tray wanda ke ɗauke da kayan breakfast, ta ajiye a gaban Fillo, ita kuma ta aje alqur'anin hannunta ta miƙe ta shiga toilet ta wanko bakinta ta dawo, tare suka yi breakfast ɗin ita da Ummi, su na ci Ummi na yi ma ta ƴan nasihohi akan sabuwar rayuwar da zata tsinci kanta, da maganganu tausasa da duk suka sanya sauran damuwar da ke tare da ita barinta. ƙarfe tara Ammi ta shigo ɗakin nasu tare da me makeup, ta tarar su Maijidda da Amatullah sun sa Fillo a gaba sai tsokanarta su ke, saboda ta daina kukan da ta ke yi sai su ke cewa ashe dama so take yi akaita gidan miji shiyasa ta ishe su da kuka, yau kuwa ga idonta nan ƙyam sai ƙyallin farin ciki da yake yi, ita dai tana zaune babu wanda ta tankawa. Me makeup ɗin ma sai da ta tsokaneta, Ammi na kallonsu duka ta ce,"to bara ta bar muku ɗakin sai inga wa zaku takurawa". ta kamo hannun Fillo suka bar ɗakin suka wuce sashin Lamiɗo ɗakin matarsa Diyam, anan aka zaunar da Fillo don shiryata, simple makeup aka yi ma ta amma tayi masifar kyau, gyaran jikin da akayi ma ta na 4days sai ka rantse an ɗauki watanni ana yi, sai faman shining take yi kamar fatar kifi, fatarta ta zama kamar madara tsabar kyau. riga da skirt na material me tsada cikin lefen da akayi ma ta na gida, sai aka ɗora ma ta alkyabba me mugun kyau red colour. Dadda ta shigo ɗakin, ta shigo tana faɗin,"kaiii Diyam ɓangarenki ai gaba ɗaya ya karaɗe da ƙamshin amarya". ta ƙarasa tana buɗe fuskar Fillo ta ce,"Masha Allah, Tubarkallah. Lallai Muhammad Turaki ya yi da ce da kyakykyawar ƴar mu, ai da na sa ni na ƙayyade masa sabon sadaki". zuciyar Fillo ta buga, tasa hannu ta dafe takardar sakin da ke maƙale acikin brezier ɗinta. Dadda ta ce da ita,"ungo sha wannan". Fillo tasa hannu ta karɓa tana yatsine fuska, zata yi gardamar da ta saba Dadda ta ce,"ke wannan ba magani ba ne ruwan tofi ne Dottijo ya bayar a kawo miki, ma za yi bismillah ki kafa baki ki sha". tayi bismillah a fili ta kafa baki, ba ta sauke ba sai da ta shanye tass da ma tana jin ƙishirwa. "ko ke fa, adu'armu itace Allah ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka ya albarkaci rayuwar aurenku, Allah ya baku zuri'a ɗayyiba, ya kauda fitina tsakaninku ya haɗa kanku ke da abokiyar zamanki". kowa da ke ɗakin ya amsa da,"ameen". a lokacin Dada ta shigo, itama ta bata wani ruwan tofin adu'ar ta sha, sannan ta ba ta wani magani na su da kuma wani turare da ta fesheta da shi lungu da saƙo, ta kuma bata wata ƙaramar kwalba itama da ke ɗauke da turare aciki ta ce,"karki yarda taje hannun kowa har ki shiga ɗakinki, ki shafa turaren ciki a lokacin da zai shigo ɗakin, karki yi wasa da duk abin da muka faɗa miki da kuma abubuwan da muka ba ki, so muke kiyi zarra, ki zama tauraruwar da ke haska cikin gidan mijinki". Dadda da Adda Asma su ka kamata a tare suka fita da ita, ɗakin Hajjah aka wuce da ita inda nan Ummi ta ke da zama yanzu ita da su Kaka da sauran ƴan'uwanta, ana shigo da ita Ummi kawai sai ta fashe da kuka, aka ƙaraso da Fillo gabanta ta durƙusa. Ummi ta zura hannunta cikin alkyabbar ta kamo hannunta ta riƙe anata, sai a lokacin Fillo ma ta saki nata kuka da bai zo ba tun ɗazu. "Yanzu kin zama matar aure, kin bar ƙarkashinmu kin koma ƙarkashin wani bawan Allah wanda Allah ya zaɓa miki matsayin mijinki, haka zalika aljannarki ta koma ƙarƙashin mijinki, bauta za kiyi, bautar da za ki saka a ranki cewa ba Muhammad Turaki za ki bautawa ba Allahnki za ki bautawa, biyayyar mijinki a yanzu ita ce gaba da komai a gurinki in banda addininki, in dai har za ki yi ma mijinki biyayya to za ki shiga aljannah, faɗar Allah ce ba tamu ba, ki kula da abincin mijinki ki kula da shimfiɗarsa, karki wasa da tsafta, ki zama me haƙuri, karki ko yi rashin juriya da kawar da kai,
🏠