ta lumshewa suka buɗe ta kalli me hoton da irin kallon da ke tsuma zuciyar duk wani lafiyayyan namiji.
tafin da aka fara ana waƙa irin ta su ta fulani sai taji a lokaci ɗaya yana tafiya da damuwar da take ciki, yana tafiya da wannan tarin hawayen da ke cikin ƙwayar idonta yana musanya shi da murmushi me faɗi.
*Gombe.*
"ka yi wankan?".
Bello ƙaraye ya tambayi Turaki lokacin da ya sakko daga upstairs.
Turaki bai ce da shi komai ba ya wuce dining, da ga yacca yake tafiya zaka san bai gama warwarewa ba, har yanzu jikin nasa da saura, duk ya bi ya rame, Bello ya taso shi ma ya isa dining ɗin yaja kujera ya zauna.
"me za ka ci na zuba maka?".
ba tare da Turaki ya kalle shi ba yace,"mene aciki?".
Bello yana nuna masa flask na abincin guda biyu yace,"nan fried suppagetti ce, nan kuma tuwan shinkafa miyan agusi".
Turaki ya sauke numfashi yana kwantar da kansa jikin kujerar dining ɗin ya ce,"couscous na ke so da miyan hanta".
Bello yay ta kallonsa before yace,"akwai data a wayarka?".
Turaki yay masa wani kallo, kallon da ya shaidawa Bello abin da yake nufi, hakan yasa shi cewa,"to ni dai duk da ba'a ji da ni a gidanmu irin yanda ake ji da kai, na rantse da Allah ban taɓa shiga kitchen da sunan girki ba sai dai in shiga in kwasa, to tsakani da Allah ta ina zan san yanda ake dafa wani couscous balle miyar hanta, yunwar dare dai ta taɓa sawa na dafa ƙonanniyar taliya, idan kuma za ka ci irinta yanzu in shiga kitchen ɗin".
Turaki ya harare shi tare da jan tsaki. Bello yace,"to ai shiyasa nace ka ban wayarka sai in yi dowloading vedio, ina ce ai kuna da komai ko?".
jin Turakin bai tanka masa ba yace,"yanzu dai tun da babu wanda kake so ɗin ka daure kaci tuwon shi ma ai ɗan uwan miyar hantar ne, kafin a kira Maama a faɗa ma ta, kaga tun safe baka ƙara cin komai ba kuma Dr ya hanaka zama da yunwa".
Turaki ya ture plate ɗin da ya ajiye masa a gabansa, Bello ya ɗaure fuska yana cewa,"ban da ma dai girma irin na rashin lafiya me zai sa in zauna ina biyewa ƙaton gardi irinka ina yin nan nan da kai kawai saboda baka da lafiya, ehh tou sai kuma girma irin ta ƴan'uwantaka, kuma itama gaskiya na ga zaka cutar da ni sai a koma abota irin ta haɗuwar gate rabuwar bakin gate".
yay tsaki,"haka kawai mutum Allah yay masa gata ya ba shi mace ya ta shi ya korata gidan iyayensu, Allah ma ya rufa maka asiri da wata billahi da ka ɗanɗana kuɗarka, ka bar ganin ina tare da kai ba komai zan iya yi maka ba kamar yanda matarka zata yi maka, banda ma rashin tunani da rashin shawara irin naka, da ka san Baffa yayi maka gate da gidansa ai da ka dawo sai kace ka mayar da ita, da tuni yanzu kana gaban Maama ana tarairayarka kamar ƙwai, abincin ma a baki ake baka ni kuwa duk abinka wallahi sai dai kaci da kanka ko kuma mu koma asibiti aci gaba da zaman jinya".
Turaki ya kalle shi da takaici ya ce,"Bello when za ka zama me cikakken hankali?".
Bello yana kai lomar tuwa ya ce,"ka siyo min kawai maganin jiran lokaci".
Turaki zai yi magana akayi sallama a parlon, Bello ya kai idonsa kan Hamid, yay masa bismilla da ya ƙaraso, ya iso wajen nasu suna ta cewa ya zauna yana ce musu a'a.
yana kallon Turaki ya ce,"akwai room guda ɗaya da babu key ɗin sa".
Turaki ya rufe ido ya shafo wuyansa, kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce,"wanne room ne?".
Hamid yace,"wanda ke downstairs".
Turaki ya sosa girarsa sannan ya ce,"bari na dubo maka".
ya ta shi ya shiga bedroom ɗin Ilham da ke nan ƙasa, ya buɗe drowern madubi ya ɗauko makullayen da suke ciki duka, ya dafe kansa da yaji yana mugun sara masa, kafin ya fito ya bawa Hamid ya ce su gwada dan bai san wanne ba ne aciki.
Hamid ya fita bayan yay musu sallama, Bello ya kalli Turaki da damuwa ke fito masa ɓaro ɓaro me haɗe da tsoro ya ce,"Dr ya kawo maka result ɗin ne?".
Turaki ya ce,"bai kawo ba, ya dawo ranar kuma sai ya tarar mun tafi hospital, but ya kira ni ɗazu ya ce she is not pregnant, ni dama na san zance ne irin na Boɗejo kawai, da na kusanceta ai ban bari sperm ya zuba a ciki ba".
Bello ya tallafe haɓa yana dubansa ya ce,"ɗan ƙara min haske mana MT, kaga ni ma na kusa shiga da ga ciki and bana so na fara tara ƴaƴa da yawa, anyway before kace min ɗan iska, ni dai tsakani da Allah ban ga abin ƙi ba a tare da yarinyar nan Ilham ba da har ka yi kuskuren sakinta MT, Mace irin cikakkun matan da ake so da suka haɗa komai, waccan kam ta zo sai kama sha wahalar raino kamin jikintaya ginu".
Turaki ya cika bakinsa da iska sannan ya ce,"a wurina sakin ta da nayi ba shi ne kuskure ba, babban kuskure a wajena shi ne da bana iya sirrinta abuna dole sai na faɗa maka".
Bello ya ƙyalƙyale da dariya bai ce komai ba, for few seconds sannan ya ce,"yanzu ma ai na san akwai abin da ka ke so ka faɗa min tun ranar nan amma ka kasa, kuma na tabbatar ba dai-dai ka aikata ba shiyasa ka ke shakkar faɗa min, yanzu dai ina jinka me ka ƙara zuwa ka aikata da babu shawara balle zurfin tunani, dan na lura da kai tun da masu jeren kayan nan suka z