yasa".
AmaturRahman ta faɗa tana wucewa toilet.
Raudha ta zauna kusa da Fillo tana kamo hannunta ta riƙe, ta ɗau wayarta tana kiran lambar me makeup da zata zo ta yiwa amarya anjima da za su yi Fulani Day, bayan sun gama wayar suka ci gaba da maganarsu ta abubuwan da zasu yi anjima.
ƙarfe uku na rana aka fara shirya amarya, wata cousin ɗin su da ta zo daga benue tana ta complain akan rashin zuwan ango da aka ce ba zai zo ba, har sai da aka ce ma ta ai baida lafiya tukunna ta sarara ta hutar da yawun bakinta daga masifa.
ita dai Fillo duk babu walwala, ƙwayar idonta na manne a cikin mudubi kai kace kanta take kallo, nan kuwa hoton ranar da suka je asibiti ne kawai ke haska mata.
ta tuno sanda suka shiga room ɗin da Turaki ke kwance an saƙala masa oxygen, ga wasu abubuwa da akayi masa connecting, kallo ɗaya dai zaka yi masa idonka ya cika da ƙwalla haka kuma kaji tsoron Allah ya kama ka.
ita da ta gansa ma sai da tayi mugun tsorata saboda kumburar da ya yi kamar an hura shi, a yacca yake ma zaka ce gawa ce, har yanzu ta kasa kwatanta abin da taji a lokacin da ta gansa da kuma abin da take ji zuwa yanzu.
kawai sai ta rufe idonta tana hasko lokacin da ta gyara masa zaman hannunsa akan gadon a sanda ya buƙaci hakan, lokacin da taji ta kasa rabuwa da hannun nasa ta riƙe tayi masa irin riƙon da bata taɓa yiwa hannun wani mahaluƙi ba, har yanzu tana jin sautin muryarta a kunnuwanta da suka dinƙa fita da amo na tsananin tausayi suna jera masa kalmar sannu tamkar yawun bakinta zai ƙare, kuma a sanda take ji a jikinta kamar yana buƙatar wani abu daga gareta sai taji ya riƙo ɗaya hannunta ya zura ma ta farar takarda, wannan farar takardar da ke ɗauke da baƙin rubutu me ɗacin ɗanɗano, rubutun da take ji gwara a soketa da mashi akan abata karatunsa kuma a alaƙantata da shi, rubutun da taji ya tsayar da wani dunƙule abu a maƙoshinta ya hana ko da yawu wucewa, ita dai ta san ko kaɗan bata son Turaki, daidai da bugawar sakan na agogo ba ta taɓa jin wani abu me kama da sonsa a cikin zuciyarta ba, tausayinsa kawai take ji wanda shi ma daga Allah ne, amma ta rasa dalilin da yasa ta damu da sakin da ya yi mata, ta rasa reason ɗin da yasa take jin kamar ta mutu akan wannan sakin.
ƙwayar idonta ta ƙara haska mata san da ta ɗauki tsayin daƙiƙu uku tana kallon takardar kafin ta iya ɗauke idonta daga kai ta sauke su akansa da yake kallonta da wani rauni da zata iya cewa ta gani acikin ƙwayar idonsa, ta san lokacin da idonta ya manne acikin ƙwayar idonsa, amma ba zata ce ga sanda hawaye masu azababben zafi suka shiga sauko ma ta ba, ta san dai ta ɗau tsayin lokaci tana kallonsa har sai da shi ya ɗauke nasa idon akanta ya kauda fuskarsa gefe, kauda fuskar da yasa taji kamar an tsikareta, tayi saurin miƙewa tana sakin hannunsa da ta riƙe ta fita da ga room ɗin tana danne kukan da yake cinta, kukan da har yau kowa ya rasa na menene har da ita kuwa, kuma kukan da har yau yaƙi tsagaita ma ta.
hawaye su ka sauka akan foundation ɗin da me makeup ke blending ma ta, me kwalliyar taja tsakin ƙorafi tana matsawa da baya da cewar,"haba ke kuwa don Allah, haka fa jiya ma kika yi mana ki kasa akai ta westing time. idan ba za ki iya daina kukan ba kice a fasa yi miki mana ki daina wahalar da ni, ni wallah ban taɓa ganin amarya me masifaffan kuka ma irinki ba".
tai maganar da muryar ɓacin rai.
kowa sai ya hayayyaƙowa Fillo akan kukan da take yi sam bai dace ba, ran kowa ya ɓaci aka fara fita daga ɗakin ana barinta, Maijidda da tsananin tausayinta ta kamata suka shiga toilet ta wanke ma ta fuskar sannan suka dawo, me kwalliyar taƙi tasowa, duk da kuɗi za'a biyata masu yawa bata jin za tayi ta yin aikin wahala haka, har sai da Ammi ta shigo tayi magana tukunna ta miƙe tana jaddadawa Fillo akan kar ta ƙara ɓata ma ta aiki.
sharp sharp akayi kwalliyar da tayi bala'in haska Fillo, ta dawo tamkar ba ita ba, aka fito da ita cikin shigar fulani kamar ka saceta ka gudu, Maijidda ta dinga roƙonta akan ta daure tayi murmushi ta kore damuwar fuskarta kar tayi musu irin ta jiya, duk ta yanda ta so ta yi hakan ta kasa, har sai da suka shiga parlon Maudo taji Dada na ba da labarin.
"ehh mana, ai ni ban taɓa ganin ƴar banza mata ba irin wannan tsohuwar, ke ni da naje asibitin ma ban san sanda na tofar da yawu ba da na ganta, kin ganta kuwa a fige kamar figaggiyar kazar da bata kama abinci ba, naji haushin kaina ma da na zauna waje ɗaya ina ta masifa banje munyi ido huɗu da ita ba tun farko ta raina kanta, muna haɗa ido ta zabga ma ta harar da ta fi tata, tana ta maganganunta ni dai na kirawo likita nace masa ga sabuwar patient nan".
ba ta san lokacin da siririyar dariya ta suɓuce ma ta ba, kuma cikin sa'a Nuratu ta ɗauketa hoto a lokacin, hasken camerar yasa ta ɗago ido karaf camera woman ma ta ƙyasta ma ta, sai kawai taji abun ya burgeta hakan ya bayyanar da dukka kyawawan fararen haƙoranta, suka fito cikin wani salo na burgewa da ɗaukar hankali, idanuwanta su ka yi wa