NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 225 of 323

nki da ni tun banyi mugun saɓa miki ba, dan tsab sai in baɗawa idona toka nasa Jagarɗo ya kai ki barikinsu ya ƙulleki, ni bana son halin ƴan iska saboda haka ki kiyaye ni". Fillo ta ɗaga idanuwanta da take jin sun ma ta nauyi ta kalla Dada ta ce,"banda lafiya ne". Dada ta zabga ma ta uwar harara ta ce,"da ba ki da lafiya kuma sai aka ce kuka ne zai yi miki magani ko?, mtswww". ta miƙe ta fita ta bar ɗakin tana ta faɗa, a parlon ta sami Ammi cikin mutane tana raba musu Dakkere(abinci ne na fulani), ta kirata tazo tace ma ta. "ɗanki ya wuce ko yana nan?". Ammi ta ce,"wanne a ciki?". ta harare ta ce,"mutanen ƙwarai ake nema ba ƴan wiwi ba, likitan nake tambayarki ba wannan mara kunyar ba". ta ce,"yana nan, amma ina jin kamar shi ya wuce kai Maudo airpot ɗa zu". "to ina waccan yarinyar ƙanwarsa, me aikin asibitin?". "sun je gidan Fatima anjima kaɗan zasu dawo". Dada ta ɗanyi tsaki tace,"ma za kirawota ta dawo ta zo ta duba jikin yarinyar nan, tayi ma ta allura yanda zazzaɓin zai fi saurin sauka kinga ajima akwai taro, ba'a tara jama'a babu amarya ba, ko kuma an gayyota jama'a kuma su zo ace musu ba taro". Ammi tace,"bata da lafiya ne?". "yo gata can dai tana neman kashe kanta ai, ciwo yana cin ta babu wanda ta faɗawa saboda shegen nurƙufanci da miskilanci da baƙin hali irin na Hayyo". Ammi ta ɗauki waya ta shiga kiran lambar Yusrah, tana ɗagawa ta ce da ita ta dawo yanzu sai ta koma. Dada ta sa aka kira ma ta Ummi, tana zuwa Dada ta ɗaga sandarta ta rafka ma ta a ƙafa. Ummi ta ɗan ja da baya tana bata haƙuri tun bata ji laifinta ba. "ki shiga ciki kiji damuwar ƴarki tun da ke dai soluwar uwa ce". ta faɗa tana bin Ummi da harara. Fillo dai na zaune tun da su Dada suka fita, tana riƙe da farar takardar da Turaki ya bata ranar da suka je dubo shi a asibiti bai da lafiya, kallon takardar ta-ke tana juyata gudun hawayenta na ƙaruwa. ta jinginar da kanta jikin bango idanuwanta a rumtse tana ƙoƙarin danne kukan dake neman cin ƙarfinta, babu abin da ke haskawa cikin ƙwayar idanuwanta sai rubutun dake cikin takardar, kawai sai ta kasa riƙe kukan ta sake shi ya fito da ƙarfi a sanda Ummi ke shigowa ɗakin. hankalin Ummi tashe ta yo kan gadon tana tambayarta lafiya, bata ma san ta shigo ba sai a yanzun, da sauri ta cusa takardar a cikin rigarta. Ummi ta kwantota kafaɗarta tana lallashinta da ban haƙuri. zatonta duk kukan ba na komai ba ne sai irin kukan da wasu amare ke yi idan zasu bar gida. Fillo ta samu ta rarrashi zuciyarta da ƙyar saboda bata so Ummi ta san abun da yake faruwa, bata san irin damuwar da zata shiga ba in har taga takardar sakin da ke hannunta, ba lallai ta iya ɗaukar wannan ƙaddarar ba, zata ga kamar itama bata yi dacen samun miji ba ne kamar yanda ita ma bata yi sa'ar miji ba a sanda ta auri mahaifinta, dalilin da yasa ta ɓoye kenan kuma ba ta tunanin za ta faɗa, ai tun da har ana zaman idda a gidan miji zata yarda su kai ta, ranar da ta gama iddarta acan sai ta sanarwa da kowa abun da ya faru, amma ba a yanzu ba da ba ta san wanne irin hali Ummi zata shiga ba akan hakan. Yusrah ta shigo tayi ma ta allura, aka kuma ɗebo uban magunguna a first aid da aka ɗauko a ɗakin Innah aka bata. Ummi ce da kanta ta bata abinci taci, sai da taci da dama sannan ta ƙyaleta. "ki daina kukan haka nan kinji Auta ta, bari naje ana ta baƙi daga ɓangarenmu, idan kika ji daɗin jikinki sai ki zo ku gaisa da su Yaya Murja". tana kallon Ummin ta ce,"wace ita?". "da babarta da Kaka ubansu ɗaya, su na can sun zazzo ma fa da yawansu, sai tambayarki suke yi, nayi zaton kuna can gidan Asma'u shiyasa ai". ta gyaɗa kanta kawai, Ummi ta fita daidai da shigowar su Maijidda, waɗanda suka shigo suna ta masifa akan ɗinkin da tela yayi musu ba daidai ba. AmaturRahman na faɗin,"na rantse da Allah in ace ba yau zamu sa kayan nan ba sai ya biyani zan baro shagonsa, ɗan iska me kama da ɗan daudu". Maijidda tayi watsi da nata akan gado ta ce,"ai ni idan kinga na saka waɗannan kayan to sauya ni aka yi, gwara idan na koma gida na dinƙa saka su idan zanyi aiki amma ba'a bikin Hussaina tah ba, ban da rainin hankali ɗinki sai kace ance masa tsofaffi ne zasu saka". Amatullah ma ta shigo ta jefar da ledar hannunta, Raudha ma haka, duk in ka kalla fuskokinsu ka san ransu babu daɗi. Raudha tayi tsaye jikin wadrobe tana fuskantar Fillo, ta harɗe hannaye tana cewa,"kin ga yanda fuskarki ta kumbura kuwa?". ta rufe idonta kawai ta kwanta tana juya musu baya, Amatullah ta ce,"ai ɗa zu Hammah Hamid ce yay idan ya dawo ya tarar ba ta daina ba sai ya zaneta babu ruwansa da matar aure ce". Raudha ta sauke numfashe ta ce,"i never see such a kind person me shegen kuka ma irinta, da muna saudia zatona ko dan Dada ta ce sai an saketa ne, da muka dawo kuma na kasa fahimtar auren ne bata so ko kuma kukan barin gida ne". "kin taɓa ganin amaryar da take kuka irin haka dan zata bar gida?, ita dai barta dan ta ga ƴar auta ce shagwaɓa tayi mata yawa shi
🏠