kulle ido tana girgiza kai,"Arɗo akwai ka da shegen taurin kai, ka faɗa musu gudunmawa bama so ta bawa ƴarta, ni jikata bata buƙata".
Arɗo yace,"tom shikenan Dada yanda kika ce".
ta sa ke cewa,"yanzu an kammala kawo kayan gaba ɗaya?".
yace,"a'a da yake bedroom ɗin guda huɗu ne mu kuma order ɗin biyu aka yo, to amma yanzu Saifullahi ya kira wani abokinsa da ke can ƙasar turkey ya taho da su zuwa gobe idan zai dawo".
Dada tace,"to shikenan ya yi, ina fatan kun faɗa masa kaya masu kyau da tsada ake buƙata ko?".
ya ce,"an sanar masa Dada".
"kuyi maganar kuɗi da shi sai ka kira Maudo ka faɗa masa, akwai wasu kayan ƙyale-ƙyale ma da Amatullahi ta nuna min jiya kuma bamu taho da su ba daga can saudia ɗin, zan sa ta turo maka a waya sai ya duba yaga idan akwai acan ƙasar sai a taho ma ta da su".
ya amsa da,"to Dada, sai ta turo yanzu".
tace,"to naji, Giɗaɗo ma sun taho yanzu da sauran kaya. don Allah ku yiwa ƴar nan jere na kece raini, irin jeren da zai hana wannan figaggiyar tsohuwar kwanciyar hankali. ni ban so ma ya haɗe musu gida ba wallahi, na so ya raba su dan sam bana son abin da zai ɗagawa jikata hankali, ina tsoron haɗe su gida ɗayan nan kar suje su ke cutarta tun da ita Allah bai yi ta da baki ba, shashasha ce banda kuka babu uwar abin da ta iya".
Arɗo yana murmushi ya ce,"Dada ai ko hakan ma kamar ya raba musu gidanne, kowacce da part ɗinta kuma da tazara sosai tsakanin part ɗin na su".
ta taɓe baki bata ce da shi komai ba ta kashe wayar tana ajiyewa a gefenta ta dubi Safara'u ta ce,"ke jiya da ku ka je gidan su angon kun gani da gaske bai da lafiyar ko kuwa iskanci ne da rainin hankali kawai za'ayi mana saboda kar yazo bikin?"
Safara'u ta ce,"ƙwarai kuwa Dada, dan har sai da muka je asibitin ma sannan aka sallame shi lokacin, ba shi da lafiya sosai gaskiya ance yana fama da ciwon ƙoda ne".
Dada ta taɓe baki ta ce,"Allah ya kawo sauƙi, rashin lafiyarsa dai ba ita zata hanamu shagulgulan biki ba".
ta waiga ta kalli Amatullahi da ke charting ta ce,"abun jiya da kika nuna min ki turawa Arɗo yanzu".
sannan ta kalla hadimarta da ke matsa ma ta ƙafa tace,"ki leƙa ɓangaren Gaji ki kirawo min Fillo, idan ba'ai wasa ba tana can tana ɗan banzan halin nata, dan yau ko ganinta banyi ba tun safe, ina kyatata zaton ma ko abinci ba ta ci ba".
tana rufe baki Maijidda ta shigo ɗakin, ta wuce tana ajiye kayan hannunta, Dadan ta dubeta tana cewa,"yauwa ke ina wannan ƴa take?".
Maijidda ta turo baki tana ɓata rai tace,"tana can".
tazo wucewa Dada ta rarumi sandarta ta buga ma ta.
"can ina?, dan ubanki ko sheɗan ya san can ne da zan tambayeki kice min wani can... sai yanzu ma na gane mugun halin da Fillo ta kwaso wajenki ta koya, ai Hausawa basu yi ƙarya ba da suka ce abokin ɓarawo ɓarawo ne, haka ma zama da maɗaukin kanwa...sam sam ba kiyi halin ƙwarai irin na kakarki ba, dole na raba ƙawancenku dan ba za'a kaita gidan miji ba kije ki lalata ma ta aure".
Maijidda ta sosa wurin da ta duketa saboda zafi ta ce,"tana sashin Kawu Musbahu ɗakin Adda Amina". zata fita Dada ta dawo da ita,"ke zo nan".
ta dawo tana rakuɓewa wuri ɗaya kamar mara gaskiya, Dada ta kalleta tsab sannan ta ce,"me aka yi miki da ma?".
Maijidda ta fara hawaye tana cewa,"tun jiya take ta kuka kuma duk na tambayeta abin da aka yi ma ta taƙi faɗa min, ina ta rarrashinta ma taƙi yin shiru, zazzaɓi ya rufeta na bata magani ma taƙi tasha".
"wacece da ma?".
tace,"Hussainata mana".
Dada ta miƙe tana dogara sandarta ta fita a fusace, ta shiga parlon Amina mutane na ta gaida ita babu wanda ta amsawa ta wuce kai tsaye cikin ɗakinta.
tana shiga ta sami Fillo kwance akan gado tayi ruff da ciki, ta taƙarƙare ta buga ma ta sandarta a baya, babu shiri Fillo ta miƙe a tsure tana dafe wajen, idonta na fara zubar da hawayen da suka tsagaita ma ta, sosai zafin dukan ya shigeta dan ƙashin bayanta har sai da ya amsa.
Dada ta dinƙa kallon idanuwanta da suka yi jawur, sun kumbura tsabagen uban kukan da take sha a ƴan kwanakin nan, fuskarta kanta tayi jaa ko tausayin kanta bata ji.
ran Dada a matuƙar ɓace ta ce,"ke wai dan uwar ubanki tare da kuka aka haife ku ko kuma an haifeki ne dan ki yi ta kuka a duniya?".
ta nemi wuri ta zauna tana ta faɗa.
"ƴar banzar yarinya mara tawakkali, idan ba za ki iya jurar rashin uban naki ba ki sha fiya-fiya ki bi shi mana, idan kuma auren ne ba kya so ki buɗe baki ki faɗa mana, ko an gaya miki mu muna kai zuri'armu gidan wanda basa so ne. nan na tayar da jijiyoyin wuya akan sai an sake ki saboda ina so na ƙwatar miki ƴancinki, iyayen yaron nan suka zo su kai ta bani haƙuri naƙi na haƙura har sai dai aka kai ƙarata gaban mahaifina tukunna, shi ma ɗin saboda ban iya ƙetarewa maganarsa ne amma da sai na dage akan bakana saboda ko kaɗan ni bana jurar naga za'a wulaƙanta min jinina, da kika san ba za ki iya zama da shi ba tun ranar da suka kawo lefe ba sai ki faɗa ba ace su juya da abinsu, to wallahi tallahi ki shiga hankali