ara kallon Baffa da kyau tace,"dan Allah ka samawa yaron nan lafiya haka nan, iyakar biyayya yai maka, wadda tun da ka haife shi yake yi maka har kawo yau bai taɓa bijirewa umarninka ba".
Baffa ya ɗaga muryarsa,"shutup Ramla".
ya juya yana kallon Turaki yace,"ban goyi bayan ka rabu da kowacce acikin su ba, amma ka mayar da matarka yanzu anan, idan ba haka ba nayi mugun saɓa maka".
still kan Turaki na ƙasa bai ɗago ba, Mum tace,"wallahi tallahi sai dai idan bana numfashi amma ba zai mayar da ita a yanzu ba, yanda kake bin umarnin mahaifiyarka saboda ka gama da duniya lafiya, shima ka barsa ya bi umarnin tasa mahaifiyar saboda ya gama da duniya lafiya, yanda kake gudun fushin taka mahaifiyar haka shima, yanda kake so ka haɗu da ubangijinka lafiya shima haka yake so, haba Alƙali ka bar yaro ya huta mana ko so kake sai kasa masa ciwon zuciya duk saboda kai baka so ka ɓatawa taka mahaifiyar".
ta mayar da idonta kan Turaki da tsananin tausayinsa tace,"Babana ta shi kaje".
ya miƙe jiki ba ƙwari zai wuce Baffa yace,"daga yau na haramta maka shigowa gidana, kar in sake ganin ƙafarka a ƙofar gidan idan kuma ba haka zaka sha mamakin abinda zan maka, fitaaa a gabana". ya ƙarasa maganar a tsawace wadda har sai da ta tsorata su Maama.
Turaki yay saurin ɗago kai yana dubansa, zai yi magana Mum ta tari numfashinsa da cewa,"je ka Babana, Allah yayi maka albarka".
Turaki ya fice yana jan ƙafafunsa da yake jin kamar ba zasu ɗauke shi ba.
yana fita Hajiya Ramla ta dubi Boejo tace,"ina ƙara baki haƙuri, Allah ya huci zuciyarki". sannan ta kalli Baffa tace da shi,"kayi haƙuri your highness".
bai ko kalleta ba ya durƙusa gaban mahaifiyarsa yana bata haƙuri tare da lallashi.
Hajiya Madina ta ɗauki wayarta ta bar wajen ranta fess, tayi upstairs tana danna kiran lambar Ummi, tana yin picking bayan sun gaisa take shaida mata cewa,"Ummin Fillo insha'Allahu ranar litinin zamu kawo lefe".
Ummi ta amsa da,"Allah ya kaimu".
daga haka suka yi sallama.
ɓangaren Turaki kuwa yana zuwa compound kiran wayar Dada ya shigo wayarsa, kamar ba zai yi picking ba sai kuma ya ɗaga, abinda ya tsammata shi ɗin ne ya faru, dan yana sakawa a dodon kunnensa ya ji ta da masifa tana cewa,"ka sakar min jika ko kuwa?, ka san Allah kar ka bari in muku ɗanyen kai".
muryarsa ta fito kamar ta mara lafiya da cewa,"Dada in tana kusa ki bani ita sai na faɗa mata".
a harzuƙe tace,"ka faɗa mata me?".
yace,"shi abunda kika ce".
tace,"wai sakin?".
yace,"ehh".
tace,"haba yaro aini ba ƴar yau ba ce, kaje ka tambayi tarihina na fi son komai za'ai ayisa da hujja, dan haka furtawa da baki kaɗai ba zai gamsar da ni ba, ba kuma shi tabbatarwa da jama'a kayi ba, saki a rubuce nake so kayi shi cikin farar takarda ka yo min aikensa".
a hankali yace,"shikenan Dada, ina kan hanya yanzu zuwa gida, idan naje zan rubuta insha'Allahu".
tace,"ya dai fi, a sakar min jika dan bazan kawota gidan da za'a ke ma ta kallon banza ba"
ta kashe wayarta tana ta jaraba akan Fillo dake kwance kan gado tana aikin kuka tun ɗazu.
Ilham na kwance a ɗaki hadimanta na matsa mata ƙafa Turaki ya shigo kamar an hankaɗo shi, ɗaya bayan ɗaya hadiman suka miƙe suka fita da azama. yay tsaye bakin ƙofa yana kallon Ilham wacce ganinsa yasa ta ɗauke idonta gefe tamkar bata ga shigowar tasa ba, shiru ya ratsa ɗakin na ƴan sakanni sannan muryarsa na shaida ɓacin rai yace da ita,"ki fito waje ki same ni".
har yay bakin ƙofa zai fita sai yaga kamar bata ji me yace ba, hakan yasa ya maimaita mata amma da mamakinsa sai yaji tace,"in fito in yi maka me?".
yay ƙyam yana ta kallonta from head to toe da son gano wani abu, sai dai hakan ya gagara, ba ya son wata sabuwar damuwar dan haka bai ƙara cewa da ita komai ba ya juya zai fita sai yaji tana cewa,"na faɗa maka zan kuma ƙara nanata maka Turaki, ba damuwata ba ne ka auro duk wacca ka ga dama, but ka san da abu guda ɗaya shine ba zan zauna da kishiya a cikin gida ɗaya ba, in har kuma ka aikata wannan kuskuren to ina mai tabbatar maka da cewa kayi bankwana da zaman lafiya da kwanciyar hankali kenan, sonka da nake ba shi yake nufin ka ɗebo duk yayin da ka ga dama ka watsa min ba, wallahi! wallahi! wallahi! muddin wata tare acikin gidan nan sai dai ko ni ko kuma ita".
sai kuma tayi shiru tana fashewa da kuka tana miƙewa zauna ta kifa kanta da gwiwa, sosai take kuka tana faɗin,"me nayi maka a rayuwa kayi min wannan tsanar, ka rasa da me zaka ƙuntata min sai da kishiya, kishiyar ma aure ko wata biyar ba'ai da yi ba, waɗanna kalar maganganu kake tsammanin kunnuwana zasu dinƙa ji daga bakin mutane, kamata, tsakani da Allah kayi min adalci kenan?, kai ko tausayina ma baka ji, ina cikin tashin hankali na irin mawuyacin halin da mahaifiyata ke ciki, kai baka zauna ka rarrasheni ba kuma kace wai ka auri wata tun kafin ni, wanna kalar rainin hankali ne wannan?, to wallahi duk wacce ta shigo gidan nan sai naga bayanta ka rubuta ka ajiye".
Turaki yay murmushin takaici ya fice ya bar ɗaki