NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 220 of 323

ni ba, kuma saboda gujewa fushin ubangijinsa da kuma taɓewar duniya yasa ya bi wannan umarnin". Boɗejo ta bi Mum da kallo kafin tayi ƙarfin halin ce ma ta,"Ramla kika sa ya saki Ilham?". Mum ta kawar da kanta gefe tana jan yatsunta tace,"kiyi haƙuri, amma abinda nake ganin ya dace shi na sa shi ya aiwatar, hakan shi kaɗai zai sa hankalin kowa ya kwanta, da ga mu har ke har kuma ita yarinyar". mayafin Boɗejo ya zame ya faɗi. "haka kike Ramla?". ta tambaya da tsananin mamakin Mum ɗin, wanda take tantamar da ƙyar idan ita ce tasa Turaki yayi wannan sakin. Mum ta fuskanceta tace,"ba zance haka nake ba ko ba haka nake ba, amma idan hakan bai yi miki daɗi ba Allah ya huci zuciyarki. naga masalaha ake ta nema tuntuni, wanda kuma ta hakanne kaɗai za'a samar da ita. kiyi haƙuri da abinda zan faɗa, ina son farin cikin ɗana, ina so ya sami kwanciyar hankali da nutsuwar da ya rasa tun daga ranar da ya auri Ilham...". "dakata! me kike so ki faɗa min?, so kike kice an aura masa annoba da har kike faɗar ya rasa kwanciyar hankali. to cikin ku biyun kar wadda ta ƙara ambatar min kalmar tashin hankali anan, tashin hankali na can wurin shegiyar yarinyar da yaje ya aura a titi, kuma tunda kika sa ya saki Ilham, to ya zama dole kisa shi ya saki waccan yarinyar da ban yarda da asalinta ba, ba zan taɓa yarda a kawo mana gurɓatacce cikin zuria'armu ba ku san da wannan, dan haka ba shi umarni ya saketa". Mum ta rufe ido ta buɗe sannan tace,"ina son rayuwar ɗana, ban shirya rasa shi a yanzu ba, kamar yanda nake tsananin son farin cikinsa, hakan yasa ba zan taɓa raba shi da abunda yake farin cikinsa ba. idan kika ce lallai sai ya saketa hakan zai zama barazana ga rayuwarsa, domin kuwa uwar gidansa itace rayuwarsa, rabuwa da ita dai-dai yake da rasa ransa, saboda haka ni ba zan sa ya saketa ba, dan Allah kiyi haƙuri a bar min yaro ya huta haka, kamar yanda ɗanki yake so ya rabu da ke lafiya haka shima yake so ya rabu da ni lafiya, sam ba zai iya ƙetare umarnina ba". Boɗejo ta nemi kujera ta zauna tana salati, ta dafe kai tana girgiza shi,"yau naga abinda ban taɓa gani da ji ba a tarihin rayuwata, ni yau ake bijirewa umarnina, ni yau ake ja-inja da ni. Ramla da Madina me ku ka taka?, me Azima tayi muku da ku ka tsani ƴarta haka?, zumuncin da ubangiji yace a yi shi ku ke so ku rushe yau?...babu komai bari Dikkon ya shigo". ta miƙa hannu ta ɗauko jakarta da ta tangarar a ƙasa ta ɗauko wayarta, da ƙyar ta iya lalubo lambar Baffa dan ta san duk wanda tasa ya nemo mata ayanzu ba zai nemo ba. ringing biyu ya ɗaga, ta amsa sallamar tana cewa da shi,"kana ina?". "ina gida". "kana cikin gidan naka ka barni da matanka suke min rashin mutunci suna gaggaya min maganganun da suka ga dama?, Dikko kana so ka gama da duniya lafiya kuwa?, to ka bar duk wani abu da kake kazo ɓangaren Mandina yanzu dan babu lafiya". tana faɗar hakan ta kashe wayarta, idonta akan Turaki da har yanzu yake dafe da kansa, dana sanin aurensa duka biyun fal cikin ransa. mintunan da basu wuce biyar ba Baffa ya shiga parlon Hajiya Madina, tun daga baƙin ƙofa yake kallon Hajiya Madina da Kuma Hajiya Ramla waɗanda ke tsaye sun kasa zama, ya ƙaraso ciki da sauri wajen mahaifiyarsa ya zauna a ƙasa yana cewa,"ranki ya daɗe gani, lafiya dai?". "ina kuwa lafiya Dikko". ta faɗa tana ɗauke ido daga kansa ta mayar kansu Hajiya Madina tace,"waɗannan marasa mutuncin matan naka sun sa yaron nan ya saki Ilham". with shock Baffa ya ɗago yana kallon Maama, Boɗejo tai saurin cewa da shi,"a'a ai ba ita ce tasa yay sakin ba, gata nan ita ta saka shi ya saki matarsa saboda bata tsoron Allah bata gudun girgizar al'arshin ubangiji". ran Baffa a ɓace ya miƙe yana kallon Hajiya Ramla. "kika sa ya saki Ilham?, a bisa wanne dalili Ramla?, wace ke?". Mum tayi murmushin takaici tace,"wace ni kake tambaya Dikko?, har ka manta shekaru 33 baya da na tsuguna na haifa maka yaron cikin tsananin wahala?, tunda ka manta bari na tuna maka, ni ce wannan matar da ta ɗauki cikinsa tsawon wata tara, na raini cikin da wuya bata daɗi ba, na kuma haife shi acikin mawuyacin halin da kai kanka kake tunanin ba lallai na rayu ba, na shayar da shi tsawon shekaru biyu, na ci kashinsa na sha fitsarinsa, ka tuna wacece ni ko kuma dai still na tuna maka?, to ni ce mahaifiyarsa, ni ce wannan uwar da ubangiji ya faɗeta sau uku kafin ya faɗi uba sai ɗaya tal. ka san kuwa da cewar ni ɗin bata wasa ba ce, ina da ikon sawa ina kuma da ikon hanawa ko ana ko ba'a so muddin ana so a gama da duniya lafiya, so banga dalilin da zai sa abi a takura rayuwar yarona ba, yayi biyayyar amma hakan duk bai yi muku ba, ya kuke so yayi da ransa?, so kuke sai ya faɗi ya mutu tukunna?, tunda har yay biyayya ya auri zaɓinku ku barsa ya auri zaɓinsa mana, amma son rai duk ya hanaku kuyi masa adalci, to ni nasa ya saki amaryarsa zai kuma tare da uwar gidansa kamar yanda zuciyarsa take so, kamar yanda hakanne zai zama farin cikinsa da kwanciyar hankalinsa". ta ƙ
🏠