NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 22 of 323

e, Amir mutumin kirki ne, ki ga fa tunda kika kwanta yake sunturi akanki". Fillo dai bata ce mata komai ba, don ita tunaninta ma na wani waje can na daban. Dogon tsakin da Fillo taja na takaici shi yasa Maijidda saurin kallonta da mamaki. "shi kuma tsakin fa?". Fillo tayi shiru tana jin wani ɗaci acikin ranta, tunda tazo gidan nan bata taɓa shiga ɓangaren masu gida ba, kai hasali ba matar gidan ma bata taɓa ganinta ba balle ƴaƴanta, idan aka cire wadda tazo ranar nan ta kawo musu kwancen kaya, abunda kawai ta san da bakin kowa na faɗa shine Uwar ɗakinmu Hajiya Madina. Amma haka kawai ta ke jin bata son mutanen gidan, dan ta ra'ayinta da tuni sun bar aiki sun koma wani wajen to dan Kaka taƙi ne. To dan me yasa ma ba zata ji zaman gidan nan ya fice akanta ba yanzu?, sanadin fa taimakon ɗansu ta shiga halin da ta shiga. sannan again tana kwance cikin wannan halin sunzo sun ɗauke mata Kaka sun mayar da ita aiki ɓangarensu, aikin da idan ta fita tun safe sai dare zata shigo, ta lura sam bata samun hutu da can ɗin. Akan me ma zuciyarta zata so matar gidan?, tuwo ne a idonta da ta kasa ganin girman tsufan Kaka da har suke loda mata uban aikin da zai gajiyar da ita. Ko da yake in akace baka da shi dama shikenan taka ƙararriya ce, talaka dai na ganin rayuwa. "salamu alaikum". Maijidda ce ta amsa sallamar da aka yi daga ƙofar ɗakin, Fillo kuwa aciki ta amsa, sai bin ƙofar ɗakin da tayi da ido. Wata tsohuwar mata ta leƙo kai cikin ɗakin tana kiran sunan Kaka. Maijidda tace,"ki shigo bata nan". Ta shigo ɗakin tana faɗin,"bata nan?, ina lafiya dai ko?, kwana biyu banga gimlawarta ba acikin ɓangaren nan". "lafiya lau, ta koma cikin gida da aiki ne shiyasa". Maijidda ta bata amsa. Ta ƙara cewa,"Allah sarki shi yasa ashe, ni fa naga kwana biyu bana ganinta a wurin aiki. Kuma da yake ta saba leƙowa a gaisa ko da ba ranar aikinsu ba shi yasa ma nace bari na leƙo naga ko ba lafiya ba". Maijidda ta ƙara cewa,"lafiya lau, idan ta tafi ne bata shigowa sai dare". Matar tace,"to kwa sanar mata na nazo idan ta dawo, kuma kuce ina yi mata barka an samu ci gaba". "to insha'Allahu za'a faɗa mata". Yanzu ma dai Maijidda ce ta amsa, dan Fillo ma babu alamar zata yi magana. Matar har zata fita sai ta dawo tana cewa,"kinga na manta fa ashe Fillo babu lafiya, kusan ni ɗaya ce ban shigo dubata da jiki ba". Ta kalla Fillo dake kumbure ta haɗe gira duka biyu tace,"ya sauƙin jikin naki Fillo?". Ba don taso amsawa ba tace,"naji sauƙi". tace,"to Allah ya ƙara lafiya...sai anjimaku". Da haka ta fice tana fita Fillo taja uban tsaki tace,"har ga Allah haushin komawar Kaka aiki cikin gida nake, gaba ɗaya an riƙeta da aiki ba'a barinta ta huta. su ko tausayinta ma basa ji, ko basu da tsohuwa ne oho?, tun fa da ta fara aikin nan idan ta fita da safe bana ƙara ganinta sai wata safen, dan kamin ta shigo nayi bacci, jiya har kusan goma da rabi bata shigo ba...jiya da ta dawo ina ganinta tana miƙa tsabar gajiya, kawai don bana cikin hayyacina ne amma da sai naje gidan nace su sallamemu". Ta gama ƙorafinta cikin masifa, Maijidda dai bata ce ma ta komai ba, sai ma ƙwaryar furar da ta janyo tana sha. ruwan hawaye ya kawo idon Fillo, muryar in breaking tace,"ni ban san ba ko basu ga yanda Kaka ta tsufa ba ne...amma me suka ɗauki kansu?". Maijidda tace,"masu kuɗi mana. kuma dai ba za ki ce suna sahun masu kuɗi marasa kirki ba. za ki so kanki ta wannan ɓangaren in kika faɗi haka...ke dai ki yiwa Kaka adu'a kawai, banda ke sanin kanki ne ba zata juri wannan bautar ba tunda ta tsufa da yawa". Bata ce komai ba, Maijidda ta ƙara cewa,"ga furar kisha da sanyi". "aina kika samu ƙanƙara?". "Yami ta aike ni ɗazu na ganta shine na sayo, nasan za ki so". Fillo tayi shiru, idonta na kallon yatsun ƙafarta. "ni dai kici abinci kar naci amanar Amir". "ba zan iya ci ba Maijidda sai Kaka ta dawo". "haka za ki yini da yunwa kenan?". "zanci amma idan ta dawo". "Amma dai kin san sai dare ko?". Fillo tai shiru, itama Maijiddan bata ƙara ce ma ta komai ba. For a while Fillo Let out a long sigh of despair, duka tafukan hannunta saman fuskarta tana ƙoƙarin danne kukan dake neman cin ƙarfinta. "Maijidda tsawon yaushe idanuwana zasu ɗauka kamin Dada ta dawo gare su?". tausayin Fillo ya kama Maijidda matuƙa, bata iya cewa komai ba sai hannu da ta saka itama tana goge nata hawayen. **** Sakkowa yake daga stairs a hankali hannunsa riƙe da mug, three quarter ke jikinsa brown colour da white t-shir me coller dark blue. har yanzu ba'a cire masa bandage ɗin dake goshinsa ba. yana sakkowa parlon direct kitchen ya wuce, ya zuba sugar acikin tea ɗin, sannan ya fito ya ƙarasa kujera ya zauna. Kaka wadda ya barota a kitchen ta fito da sauri, ta ƙaraso inda yake, da rissinawa ta ke faɗin. "sannu ya yallaɓai". Turaki ya amsa mata yana ɗan runtse ido saboda zafin ciwon dake kafaɗarsa. Kaka ta saka masa pillo daga bayansa sannan ya jingina da kujer
🏠