NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 216 of 323

suna Hassana Kakar Fillo ta wurin uba, Fillo uwar gidanka da bata tare ba har yanzu ka shaida?". Turaki ya gyara zamansa yana rissinar da kai kaman a gabanta yake yace,"Allah sarki Dada ina yini". tace,"lafiya". Turaki ya shafo wuyansa yana jin nauyi da rashin dacewar abinda yayi, tun ranar sadakar uku da ya baro Taraba bai ƙara waiwayar garin ba balle ta kan Fillo da ya san ya baro acan, ya sani tana da hakki akansa amma fushin da yayi da ita baya jin zai iya ƙara nemanta sai idan ita ta neme shi, shi ba lusarin namiji bane da zai bari son ƙanƙanuwar yarinya yake walagigi da shi, dalilin da yasa ya banzatar da ita da lamarinta kenan, kuma ya ɗau alwashin indai ba gajiya akai aka kawo masa ita ba shi dai da kansa ba zai nemeta ba, Maama tayi fama da shi har ta haƙura ta zuba masa ido, shi yanzu yaji ma da bala'in Boɗejo na kullum kullum, da fitinar da Ilham ta tsira ba dare babu rana, ta wanni fannin ma sai yaga barin Fillon acan shi yafi akan ya ɗaukota ya kawota nan ɗin, dan bai san abunda Boɗejo da Ilham zasu aikata ba. yace,"Dada dama...". tayi saurin katse shi da cewa,"riƙe dama ɗin ka, zatonka biko na zo?, a'a ko ɗaya wallahi ajinmu da girmanmu ya wuce nan, kiranka nayi dama in sanar maka da cewa Kakarka ta kira waya tayi mana kowanne irin kalar rashin mutunci, tace muddin Fillo bata rabu da kai ba to mu kuka da kanmu da duk abinda zai biyo baya, tace babu batun tarewarta a gidanka in ba haka ba zata cinnawa gida bom, tace ba zai yiwu daga auren ƴar sarki a ɗauko ƴar aiki ace za'a haɗata da ita a matsayin kishiya ba, itama kuma matar taka tace ba zata zauna da kishiya ba Fillo ta nemarwa kanta mafita tun bata yi mata lahani ba, to shiyasa na kiraka in faɗa maka cewa ka sakar min jika saki uku rasss domin tafi ƙarfinka ta kuma fi ƙarfin zaman gidanka ba wai dan muna tsoro ko kuma muna gudun abunda zaije ya dawo ba, a'a wallahi fin ƙarfinka tayi in ma faɗa maka gaskiya, akan me zata zauna a gidan daƙiƙi da daƙiƙiya alhalin ita da iliminta, to dan haka idan da kana tunanin cewa bata da gata shiyasa ka maki giya kaje aka maku kalar wannan watsatstsen auren to yanzu ka sani da gatanta, mutuwar ubanta ta bankaɗo mata daraja da ƙima da mutuncin da take da shi, ita ba salwantacciya bace da za'a kaita gidan da wata figaggiyar tsohuwa can zata ke kallonta banza a wofi, gwarama in saboda matarka ce nace Fillo ta daka shegiya daidai gwargwadon ikonta dan babu matsoraci a zuri'armu. in taƙaita dai, Turaki kake ko waye yanzu da muke wayar nan ka rubuta takardar saki uku rerass ka yo min aikenta, idan kuma kaƙi sakar min jika aradun Allah zan sa a ɗaure kaff zuri'arku, dan bani da kyau, mutunci ba isata yayi ba". Turaki ya rumtse idonsa sosai, farar ɗaya ciwon kai ya kama shi, ya rasa me zaice da Dada, idonsa ya dinƙa haska masa irin jalalar da Boɗejo ta dinƙa yiwa Maama da Mum akan auren nan da zancen tarewar Fillo da akai, cin mutunci babu kalar wanda bata yi musu ba, har da cewa zata sa Baffa ya sakesu su kama gabansu, tana faɗin wai Ilham ba zata zauna da kishiya ba itama ai ita ɗaya ta zauna, in ace dai wata Turaki ya aura to in goma zai yi babu abinda ya dameta, amma akan Ilham zata iya cinnawa kowa wuta a ƙone, sai taga ta inda wata shegiyar ƴar aiki zata raba miji da Ilham, banda ma dai ana so a bar masu abin kunya ace za'a haɗa ƴar sarki da ƴar aiki, to ba'a isa ba, yanzu dai baida sukuni ta hanasa sakat, bini bini ta kira shi tace ya saki ƴar aikin da yaje ya aura a titi babu waliyi. ya furzar da iska daga bakinsa yana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, in da yasan haka auren yake me zai kaishi yin auren duka biyun. Bello nata tambayarsa me ke faruwa bai iya ce masa komai ba, har sai da Dada taji shirun yayi yawa sannan tace da shi,"baka ce komai ba, sai fa ka sakar min jikata, kaima ai ba ƙaunarta kake yi ba munafiki algungumi, kayi zaton gata ne bata da shi kaje ka maki giyarka ka aureta ta yanda zaka wulaƙantata, har da wani cewa tausayinta da taimakonta yasa ka aureta, a gidan uwar wa kake tausayin nata, yaushe rabon da ka waiwayeta?, ai dama duk me hankalin da yaji kalar wannan auren ya san na cin mutunci ne, to aradun Allah ko ka sakar min jikata ko babbar kotun duniya ta rabani da kai". a hankali Turaki yace,"kiyi haƙuri dan Allah Dada...". ta ɗaga murya wajen saurin katse shi da cewa,"kai bafa sulhu na kiraka muyi ba, in sulhun zan nema in kira waccan jarababbar Kakar taka mana, to ka daina bani haƙuri dan babu shi a tsakaninmu kuma ba zanyi ba, ka sakar min jikata kawai, yanda ake jinka ɗan gwal kai da matarka itama haka take ƴar gwal ba daga sama ta faɗo ba". ya ƙara cewa,"Dan Allah Dada...". Dada tayi ɗiff ta kashe wayarta, ta jefar da ita a ƙasa tai ɗakinta, Raudha tabi bayanta da kallo cike da takaici, yaushe aka siya mata wayar amma tana neman ta kashe mata ita. *Gombe, 11:00am.* a sanda suka gama wayar da Dada, Turaki ya baro office ɗinsa yana jin kansa duk ya cunkushe. Bello dake driving ɗin y
🏠