NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 215 of 323

ubanki ba da yasa aka raina mu haka, banda yaja mana raini har ina wannan figaggiyar tsohuwar ta samu zarrar yo min aiken in raba jikata da jikanta dan yafi ƙarfinta, jikarta ƴar sarki ce tafi ƙarfin ta haɗa kishi da jikata ƴar aiki a gidan Alƙali yake ko uban me oho?, har ƙara faɗa take yi mu kuka da kanmu in har muka bari akayi tariyar auren nan". tai shiru tana cizon yatsa kafin ta shiga nuna kanta,"har ni ake yowa wannan baƙin aiken rashin mutumcin ban ɗau matakin komai ba?, ni ƴar sarkin taraba, uwar gwamnan taraba, uwar hakimin wurkum, Kakar soja, uwar macen da tafi kowacce mace kuɗi a nahiyar africa, yo ni kam yaushe nayi wannan saken?, dama har haka tsufan ya lalatar da ni?, ko da yake duk Hayyo ne yaja min ba kowa ba kuma yaje shi da Allah". cikin ɓacin rai ta ƙara buga sandarta akan table har saida glass ɗin ya tsage. "to billahillazi idan ban sa jikan nata yayi fatali da gimbiyar waje ba ya zauna da Fillo kaɗai ba shegiya nake, Hassana sunana na fita fitina da rigima wallahi, taje ta binciki tarihi taji ba'a taɓan ƴaƴa da jikoki a zauna lafiya". tai ƙwafa tare da miƙewa,"na rantse Allah ne ya rufawa Hayyo asiri bamu ƙara gamuwa ba da wallahi tallahi babu abinda zai hanani kai ƙararsa gaban alƙali, haka kawai yaja anai mana kallon ƙanan mutane har ana ci mana mutuncin da kare ba zai shinshina ba, akan jikarmu zata tare a gidan aurenta a kira waya ana mana gargaɗi, kashhh, amma babu komai idona idonta sai ta san tayi min aiken baƙaƙen maganganu, sai ta san tasa shegiyar matar tasa ta kira jikata ta zazzageta, zan nuna mata na fita ɗanyen kai, kowa ai shegen kansa ne, jikan nata da ta-ke ta haƙilo akansa zan nuna mata mune rayuwarsa, ba dai ance yana matuƙar ƙaunar Fillon ba, to aradu sai ya sakar min jika sai dai ya mutu, in ya mutu ita ke da asara bamu ba". zata bar wajen ta kalla Fillo taga tana kuka, ai ko ta ɗaga sandarta ta dinƙa bugun Fillo da ita tana faɗin,"saboda nace sai ya sake ki shine kike kuka, ke ko ace ma Kakar tasa bata kira taci mutuncinmu ba kya yarda ki koma wurinsa ne yanda yay fatali dake ɗin nan ya manta da aurenki dake kansa, to kuwa sai dai ki bi ubanki amma wannan aure sai ya mutu a yau-yau ɗin nan, dan ba zan yarda kije inda za ake miki kallon raini da ƙasƙanci ba duk da cewar ubanki yaja miki, kiyi kukan jini ba na ruwa ba, indai jikan wannan figaggiyar tsohuwar ne na rabaku bake ba shi, ya sakar min ke ki samu mijin aure anan kafin mu koma, babu abinda za kiyi da ɗansu, in ma saboda taimakon da suka yi miki ne gantalallar uwarki ta kasa cewa komai to ai kema kin masa taimakon da yafi nasu, ni na gode Allah ma da bai mayar dake saura ba". tai hanyar ɗakinta sai jaraba take yi, ta buɗe ƙofa zata shiga ta waigo ta kalla Raudha tace,"ɗau waya ki kira min Jagarɗo". sai kuma ta fasa shiga ɗakin ta dawo ta zauna, ranta ɓace take ta kallon Fillo dake kuka, banda tana tausayin karta ɓaɓɓallata da sai ta ƙara mummuƙa mata sandar ko ta shiga hankalinta. Raudha ta miƙo mata wayar tana cewa,"ga shi Dada". ta karɓa ta kara a kunne tare da saka glass ɗinta kamar ganinsa zata yi, bayan sun gaisa tace da shi,"kana jina?". daga ɓangaren Jagarɗo yace,"ina ji Dada". tace,"to ka saka Kakinka na sojoji ku ɗauki hanyar gombe yanzun nan, ka shiga har cikin gidan Alƙali wa yake oho, ka kamo ɗansa da yake auren Fillo kasa masa ankwa sannan ka basa biro da takarda kace ya sakar min jikata, in yaƙi kayi gidan gyara hali da shi da figaggiyar Kakarsa da ta yo min aiken rashin mutunci". Jagarɗo yace,"amma Dada inaga wannan fa sakin nan ba masalaha bane, kar a maida yarinyar nan bazawara tun tana ƙaramarta". ta fusata tace,"a mayar ai bata zama sauran wani ba, ya saketa yau ɗin nan in ba haka ba ai tashin hankalin da ba'a taɓa yi ba". tana faɗin haka ta kashe wayarta, ta kalli Fillo ta doka mata tsawa tace,"ɗago da kanki ki bani lambar mijin naki". Fillo ta ɗago kanta, hawaye duk ya wanke mata fuska, cikin muryar kuka tace,"ban san lambarsa ba". Dada taja tsaki tace da Raudha,"kira min AbdulHamid a waya". ko sallamar Hamid ɗin bata amsa ba sanda ya ɗaga wayar, tace da shi,"ka turo min da lambar mijin Fillo yanzu yanzu". sanin wace Dada yasa ko tambayar ba'asi bai yi ba, haka kuma bai jinkirta ba wajen turawar, dan duka 2 numbers ɗin ya tura mata, gudun ma kar ta ƙara kira ta zazzage shi tace ya tura mata ta ƙarya. Fillo ta miƙe tayi bed room ɗinsu tana jin zuciyarta kamar zata fito, har sau biyu kiran wayar Turaki na shiga bai ɗaga ba sai ana uku, lokacin suna tare da Bello a office, ganin lambar saudia ce yasa bai hanzarin picking ba dan bai san ko waye ke kiran ba. yana ɗagawa yayi sallama Dada ta amsa kamar abin arziƙi, daga can ɓangarensa ya kurɓi ruwa sannan yace,"wake magana?". Dada tana kalla Raudha tace,"munafuka mene ma sunan shi?". baki na rawa Raudha tace,"kamar Turaki naji suna faɗa". Dada tai gyaran murya sannan tace,"Turaki ne?". yace,"ehh ni ne". tace,"yauwa to
🏠