da yake so ya tafi, so ita taso ta zauna anan nigeria but due to haukar Asuu da ta sani yasa ta fasa cikewa ta-ke bincike akan Uni ɗin da Raudha tace su tafi can kawai, yanzu lissafin karatunta kawai take yi ba lissafin wani aure ba kamar yanda taga an mayar da hankali akai tun bayan adu'ar arba'in.
Dada da ke shan tea ta ɗago kai ta kalla Fillo, ta girgiza kai tana yamutsa fuska kamar wacca taga kashi tace,"tirrrr, tirrr, tirrr da wannan mugun hali naki irin na Hayyo".
Fillo kamar zata yi kuka ta shiga dukan ƙafa a ƙasa tace,"kai dan Allah Dada, Abba nah fa ya mutu ki daina min irin haka, duk in kin ambaci sunansa fa sai ya tashi a ƙabarinsa".
Dada ta watsa mata wani kallo na ki shiga hankalinki da ni sannan tace,"an faɗa ko ba halin nasa ba ne, wani yace kar ya zama mutumin ƙwarai?, to in faɗa miki har duniya ta naɗe Hayyo dai bai da halin kirkin da za'a shaide shi da shi gwara ma ki daina nunawa duniya shi ubanki ne, ko kuma kike bari ana ambatarsa akai-akai ko ake masa adu'ar samun rahamar ubangiji.
banda iskanci ke kenan baki da aiki sai faman ɓata fuska ki yita turowa mutane laɓɓa gaba kamar ganda, to wallahi ki kiyayeni tun ban ɓata miki ba, ana tausaya miki saboda rashin mahaifi amma kina yiwa mutane iya shegen da kika ga dama, to ni ubanki zanci ba kowanne iskanci nake ɗauka ba".
ta gama faɗan tana harar Fillo kamar idanuwanta zasu zazzago, sannan ta juya kan Raudha tace,"ina jinki kin gama lissafin abinda na saka ki?, kuma kin duba shagon da yafi kowanne anan Jeddah ɗin?, ba sanin kan shagunansu nayi ba inda dai Riyadh ne can nafi zama".
gaban Raudha ya faɗi, nan da nan ta shiga zare idanu kafin tace,"kiyi haƙuri Dada wallah na mance, amma zanyi yanzu".
da muryar faɗa Dada tace,"in saka ki aikin tun yammacin jiya kice min ba kiyi ba?, to uban me kike rubutawa yanzu?".
"Dada ai kin san can dangin mijin Fillo sunce za'ai events kafin ta tare, shine dama nake lissafin abubuwan da zamu yi, ƙanwar mijin tana ta yo waya ta tambaya ko mun gama shirya abubuwan da muke so kuma duk banyi ba, ita kuma inata tambayarta taƙi ce min komai kiyi mata magana dan Allah".
ta faɗa duk a ɗarɗarce saboda irin kallon da Dada ke bin ta da shi da makafin idanuwanta.
Dada ta gyaɗa kai ta juyo ta fuskanci Fillo tace,"ke ɗauko min sanda ta".
sanin hali yasa Fillo miƙewa babu shiri ta wuce ɗakin Dada, in few seconds sai gata ta dawo tana miƙawa Dada sandar daga baya-baya. Dada ta karɓa ta saita kafaɗar Raudha ta muƙa mata, tuni zafin dukan ya ratsa Raudha idonta ya ciko da ruwa.
Dada ta fara mata masifa,"uwaki da ubaki ke da lissafin bikin, wato har wani shirin bikinta kuke yi saboda ba kwa ƙaunarta ko?, saboda ubanta ya mutu shikenan sai ace bata da me tsaya mata?, to tana da ni Kakarta, ni ce nan gatanta, dan haka banga wanda zai ɗaukar min jika ya kaita inda ba'a ƙaunarta ba. ko za kice baki da labarin Kakar yaron bata sonta ba?, har tana faɗin wai ya sakar min jika, to dama ko bata sa shi ya saketa ba ai mu zamu buƙaci ya saketa tunda dama jikar tamu ba sonsa take yi ba, ni inama na taɓa jin anyi gantalallen aure irin wannan Allah dai ya gafartawa Hayyo, to in har ba so ake rai ya dinƙa ɓaci ba kar in ƙara ji an tada maganar auren nan".
taja dogon tsakin da duk su Fillo sai da suka toshe kunne, ta doka sandarta akan table ɗin dake gabanta, fuskarta na bayyana tsurar ɓacin rai ta hau ruwan bala'i kamar zata haɗiye gidan.
"wace ita da zata ce jikanta yafi ƙarfin jikata ba zai zauna da ita matsayin matarsa ba?, to me take ji da shi, kuɗi ko mulki ko kuwa sarauta?, idan tana ɗagowar cewa suna da Gombe a hannunsu to muma haka muke da Taraba a tafin hannunmu tun daga sama har ƙasa. ita wai ƴar wofi har wani kashedi take turo min kar in sake jikata ta tare a gidan jikanta saboda yana aurar ƴar sarki, to idan ban sa an ƙwace sarautar tasu ba Allah ya tsine, babu ƙulla ƙullar da ba zan iya yi ba akan a tsigesu a kujerar sarautar nasu sai inga ta tsiya, yo banda ma dai ƙaddara ina jikata ina jikanta?, ai wallah sam babu haɗi, jikata tafi ƙarfin wannan mummunan jikan nata, wani dogon banza ma da shi kamar basamude, ai Fillo matar larabawa ce ba matar mutumin da zuwansa saudia ma bai fi ƙirgen yatsu ba, yaron ma da bai ma san darajar mace ba, tun sadakar uku bai ƙara waiwayanta ba shi ga shi ɗan iska, iya haka ma ai ya shaida maka wannan yaro baida ilimin addini sam, mu kam kaf zuri'ar Barkinɗo babu wanda yake jahili babu kuma wanda ke auran jahili, babu ta inda aka barmu daga addinin har bokon, saboda haka can ta kwaɗa jikan nata ta cinye itace a yunwa ce, mtswww daga jin ma yanda take hayagaga akan sarautar tasu kasan ci akai aka rage musu".
tai shiru tana faman huci sai girgiza ƙafa ɗaya akan ɗaya take yi, ta kuma jan tsaki ta kurɓi tea sai kuma ta zubar da shi acikin wata ƙatunwan silver me kama da sink.
ta kama haɓa tana jijjiga kai na irin takaicin nan ya isheta, ta ɗora manyan idanuwanta akan Fillo tana faɗin,"to ni dai ban yafewa