i daɗin taka ta!, zata iya ɗaukar bull shits ɗinta kuwa?.
kawai sai ta cije leɓenta na ƙasa, for some seconds ta buɗe ido a sanda motar ke ƙoƙarin dukan bishiya, da ƙarfi tace da shi,"kayi a hankali zaka ka bugi bishiya".
yay saurin juya kan motar yana kaucewa bishiyar da ya kusa daka ba tare da ya sani ba, duk sai yaji dama ya bar wancan mutumin ya tafi da su, dan shi kansa ya san ba'a hayyacinsa yake ba, banda bala'in ciwo da kansa yake masa yana jin ƙirjinsa ma kamar zai bar jikinsa, ga idonsa ma ba sosai yake gani ba saboda azababben baccin dake cikinsu, ya ɗauka wayarsa zai kira Hamid yazo ya tafi da su sai kuma ya fasa, yaci gaba da lallaɓawa yana jan motar a hankali.
sanda suka sauka akan titi ya shiga street ɗin da zai kai su gidan Barkinɗo, daga saman kansa yaji tana tambayar,"wai ina zaka kaini?, dan Allah ka kaini gida, ni ba wurin Maama zanje ba".
bai ko waiga ya kalli inda take ba balle ya amsa mata. ta ɗauke idonta daga kansa taci gaba da kallon hanyar da bata sa ni ba, da irin ginin gidajen da zata ce in ba a tv ba bata taɓa gani ba, hanyar sam bata yi mata kama hanyar da ta taɓa bi ba, tunaninta ɗaya ne ta yanda zata buɗe murfin motar ta faɗa waje.
sunyi tafiya me nisa a street ɗin sannan ya samu wuri yay parking, idonsa na manne da gabansa yace,"fita".
Fillo ta ɗauke idonta daga kan symbol ɗin da take karantawa ta juyo tana kallonsa, kamar ba shine taji yayi maganar ba kuma sai taji ya cire mata tantama da ƙara maimaitawa. "fita".
tace,"ai ban san ina ne nan ɗin ba, ba zan iya gane hanya ba".
shirunta yayi daidai da doka mata tsawa yana ƙara cewa,"i said get out of my car". babu shiri ta buɗe motar jikinta na kyarma, ta fita ta tsaya tana riƙe da murfin motar, "dan Allah kayi haƙuri idan ka saukeni anan wallah ba zan iya zuwa gida ba, ban san ta nan hanyar ba".
yana jinta dai bai tanka mata ba, ya ɗauko wayarsa ya danna kira a lambar Hamid, yana ɗagawa yace da shi,"kaine ka shiga mota yanzu?".
Hamid yace,"ehh".
yace da shi,"ƙaraso ka ɗauki wannan yarinyar, tana wajen symbol ɗin da akai addressing da sunan Hakimi".
Abdulhamid yace,"ok tom gani nan".
sai da ya hango motar Hamid ta taho tukunna ya figi tasa ya bar wajen, Fillo tayi saurin sa hannu ta kare idonta gudunta kar ƙurar da ya baɗeta da ita ta afka mata a ido.
Hamid yazo ya ɗauketa kuma har suka ƙarasa gidan bata iya ce masa komai ba, sai magana yake yi mata tayi shiru bata amsa masa ba, tambayoyi ne fal a bakinta amma jin bakin nata take yayi mata nauyi.
tunda ta fito a mota kuma sai ta zama ƴar kallo, idonta kamar zai faɗo waje saboda kallon gidan da ake nufa da ita da kuma mutanen dake ta tururuwa akanta, suka shiga gidan tana jin muryoyi da dama na faɗin,"ga ƴar gidan Hayyon, masha'Allahu ta sami lafiya".
sai kuma taji wata dattijuwa na cewa,"ɗauko ruwan tofin nan a bata Malam yace tana shigowa ta fara shansa".
idanuwanta suka sauka akan Ummi dake tsaye a bakin ƙofar ɗakin Hajjah mahaifiyar Hayyo, ta ƙwace daga hannun mutanen dake riƙe da ita ta tafi wurinta ta faɗa jikinta, Ummin ta kama hannunta suka wuce ɗakin Dada, kuma zuwan nasu ne ta samu duk amsar tarin tambayoyin dake cikin kanta tun kafin tayi tambayar a bata amsarsu.
mutuwar iyaye bata daɗi, kuma ba'a farin ciki da mutuwarsu duk lalacewarsu, but a ɓangaren Fillo abu ɗaya da zata iya buɗar baki tace shine mutuwar mahaifinta tayi mata rana, domin ta dalilin mutuwarsa yau gasu cikin jin daɗin da basu taɓa hangar cewar zasu ji shi ba har su mutu, gatan da basu san suna da shi ba yau gasu acikinsa.
sai nan da nan ake da ita da Hamid da sauran sisters ɗinta kamar wasu gwala-gwalai, tarairaya kace ƴaƴan wasu shegen ƙusan, motsi kaɗan a tambayesu me suke so.
cikin satin mutuwar kafin ayi adu'ar bakwai haka aka dinƙa ɗaukarsu ana zagawa da su cikin dangi, babu inda ba'a kai su ba adai familyn mahaifinta da suke nan cikin taraba state, waɗanda basa ƙasar ne kawai ba'a kaisu wajensu ba amma suma sunyi vedio call da su.
a hankali ta dinƙa jin damuwar mutuwar na tafiya tana barinta, sai in sun zauna ita da Hamid ne sai suyi ta tambayar junansu wai me yasa Abba ya tsiyatar da kansa haka har yayi irin wannan rayuwar ƙasƙancin bayan yana da gatansa, amsar da basu da ita har kullum kenan.
*After 55days.*
*Saudiyya, Jeddah, Sanabile, House no 08.*
*13:00pm.*
Rauda ta fito daga cikin bedroom ɗin hannunta riƙe da biro da jotter, yayinda Fillo ke biye da ita a baya nata hannun riƙe da laptop. suka ƙaraso parlo Raudha na cewa,"yanzu to ya kika ga lissafin?, tunda dinner ce kawai ai hakan yayi ko? sai dai ban san ba ko after an kaiki akwai abinda za'ayi".
Fillo bata ce da ita komai ba ta zagaya ta side ɗin da Dada take ta zauna kusa da ita, taci gaba da operating laptop ɗin tana duba wata university acan Europe, dan tun bayan sati ɗaya da rasuwan Abbanta ta zana private waec tare da su Raudha da Amatullahi sauran jikokin gidan, aka kuma ce kowanne ya nemo university ɗin