NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 212 of 323

a barin wajen yana saurin isa gaban Fillo da hazari ganin tana ƙoƙarin tashi ta bar wajen. ya kama hannunta ya maidota kan kujerar ta zauna, kawai sai ta ƙara fashe masa da kuka ita lallai ya saketa yanzu ba sai anje gida ba, ya dinƙa bata haƙuri da lallashi amma kamar yana tunzurata, ransa ya kai ƙololuwar ɓaci ya sakar mata uwar tsawa da tasa babu shiri ta faɗo jikinsa tana ƙanƙame shi, jikinta banda kyarma babu abinda yake yi. "ban san irin illar da zan yi miki indai kika ƙara ambatar min kalmar saki". sai kuma ya kwantar da murya gwanin ban tausayi yace,"wannan Kukan naki ba komai bane illa damuwa, muyi avoiding duk kalar wani abu da zai saka ki a damuwa muddin muna sonki da rai, haka Dr yace, bana so na rasaki Fulani nah ina so na rayu da ke, ki taimaka min, wannan kukan naki na faɗa miki baida amfani, in har za'a bawa Abba damar magana da yayi yace ki bar yi masa wannan kukan kiyi masa adu'a, so please ba kuka ba just pray for him". tayi ɗif tare da lafewa a jikinsa kamar ba ita ba, shashsheƙar kukan ma a hankali take yi yanda ba zai ji ba, ya kai bakinsa saitin kunnenta a hankali yace,"za ki bi ni mu tafi tare?". ta girgiza kanta da sauri alamar a'a, sai kawai ya rufe idanunsa tare da miƙewa ya kama hannunta itama ta miƙe. tana taka ƙafarta tace da shi,"zafi ƙafata". yace,"to in ɗauke ki?". ta girgiza kanta da sauri. ya riƙe hannunta suka koma office ɗin Dr, sai da Dr ya tabbatar masa ciwon ƙafartata babu damuwa ya kuma gamsu sannan ya kamo hannunta suka fito. su Kaka har sun tafi lokacin, tana wurga idanu a compound ɗin tace masa,"ina su Kaka?". yace,"sun wuce". ya faɗa yana nufar inda motarsa take, ita dai binsa kawai ta-ke yana riƙe da hannunta har lokacin, sai kallon baƙon asibitin ta-ke yi tunda ba nan aka saba kaita ba, suna zuwa bakin motar sai ga wani mutumi nan ya ƙaraso wurin da gudu-gudunsa. ya rissina yana cewa da Turaki,"ance in zo in tafi da ku ne". Turaki na kallonsa yace,"a'a ga motata ai, kaje kawai". mutumin ya ƙara rissinawa yana cewa,"umarnin Dada ne yallaɓai, Dottijo ma ya ƙara da nasa akai". Turaki ya kalla Fillo da ke ta kallon mutumin da rashin sanin sunayen da yake ambata. yace da shi,"kaje kawai babu damuwa". "tom shikenan ranka shi daɗe, A iso lafiya". ya juya ya bar wajen. Turaki ya buɗe front seat Fillo ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ɓangarensa, ya tada motar suka bar asibitin yana driving kamar baya so, ya maƙale hannunta a nasa kamar wanda za'a ƙwaceta ko wadda zata gudu. ita dai kanta na jingine da jikin kujerar, tana ta kallonsa ta gefen ido tana ganin yanda yake cije fuska yana matse goshinsa tare da dafe kai, har stearing ya kusa ƙwace masa, hakan yasa ya gangara gefe yay parking, ya kifa goshinsa akan stearing, Fillo dai sai kallonsa ta-ke yi, bayan wucewar daƙiƙa biyu tace da shi,"baka da lafiya?". yay shiru bai ce mata komai ba, har sai da ya ɗauki minti biyar a haka yaji ya ɗan sami relief tukunna ya ɗago, ɗagowar tasa tayi dai-dai da shigowar kiran Maama, yay picking yana magana da ƙyar. tace da shi,"me Babban suna na rasa yanda zanyi da Baffanku, kayi haƙuri kawai mu koma tare tunda Fillon taji sauƙi kaji, kasan dai yanda lamarin Boɗejo yake sai haƙuri". yace,"tom Maama". tace,"baku taho a asibitin bane?, su Kaka sun dawo tun ɗazu anata tambayar ko lafiya ku baku taho ba, ka san akwai ƴan uwan Babanta daba ƙasar nan suke ba suna so su ganta kafin su koma". yace,"ina kan hanya Maama". tace,"bana son damuwa Me Babban suna, karka zo min da ita ka jefar da ita tun a hanya kaji". ya amsa da,"as you wish". yaci gaba da driving ɗin, Fillo dai tsoro ya cikata duba da kamar ba'a hayyacinsa yake tuƙin ba, can yaji muryarta cikin ƙarfin hali ta ƙara tambayar,"baka da lafiya?". yay mata wani kallo yace,"kina da damuwa da lafiyar tawa ne?". idanuwanta suka yi narai-narai, ta kauda fuska gefe tana kallon titi tana jin zuciyarta nayi mata zafi, ita bata taɓa sonsa ba a rayuwarta, kuma bata taɓa jin zata so shi, abinda tayi masa taimakonsa kawai tayi, so how comes za'a ce shine mijinta?, me yasa ƙaddara zata yi mata haka?, ta ina zata fara zama da shi irin wannan zaman da taji su Ummi na faɗa wai zama na har abada?, taji ƙwalla ta cika idonta, wani dunƙulallan abu ya tsaya a maƙoshinta, in ace shima yana sonta wataƙila ta iya haƙurin zama da shi ɗin, but shima ba sonta yake ba, ya aureta ne saboda ya taimaketa da kuma tausayinta, sannan kuma ya aureta alhalin ya san ba zai iya zama da ita kaɗai ba?, shin ta ina zata fara zama da shi da bata sonsa da kuma kishiyar da bata ƙauna. ta rumtse idonta sosai cikin ranta tana adu'ar Allah ya ɗauki ranta kafin zuwan lokacin da za'ace an kaita gidansa. lokaci ɗaya hawaye ya shiga zubo mata, wataƙila da Abbanta yana raye da ya tsaya mata har sai an raba auren tunda bata so, ta kulle idonta tana jin wani bala'in zafi da ɗaci a ƙasan ranta, kishiya! ita Fillo da kishiya!, kuma kishiyar ma ƴar sarki yacce zata j
🏠