NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 21 of 323

wai ta gyaɗa masa, ta sani ɗin in har ba'a kira Amir Babban Malami ba to ba za'a kira shi ƙarami ba, Babansa Malami kai kafatanin gidansu ma, kwatancen gidansu ma idan za'ai gidan malamai ake cewa, kuma kusan shi ya gado mahaifinsa 100% cikin yara 28 da Allah ya ba shi. Ya taso ya matso kusa da ita, ya bar tazaran inches tsakaninsu. "me da me kike ji?". Ya tambayeta yana kai hannunsa ya taɓa goshinta. Sai ta rufe ido tana jan numfashi, so ta ke ta tambaye shi abinda Kaka taƙi amsa ma ta, ta tambaye shi makomar wanda ya ƙona asirin da ba nasa ba, kuma so ta ke ta yi musu bayanin ta ƙona asiri, ko ta samu ta waraka daga wannan masifar da ta jawa kanta. to amma ta ya?, ta ina zata fara?, da wanne irin bayani zata faɗa musu?, wacce fahimta zasu yi ma ta?, shin zama su yarda da ita ne?. Bama zata soma wannan katoɓarar ba, saboda idan Kaka ta fahimceta ba lallai Amir ya fahimta ba, kuma wataƙila idan wani yaji ta ɗaure kanta akan cewar ita ke da niyyar masa asirin. Ita dai ta sa ni ko meke damunta a halin da take ciki yanzu yana da nasaba da ƙona asirin da tayi, ba zata iya tantance irin mummunar halittar da ta ke gani cikin mafarkinta ba, ita tayi hakan bisa tausayi da kuma son taimakawa wanda ake son cutarwa, to amma kuma shikenan daga taimako?. Sai kawai ta rumtse idonta sosai, tabbas ba Muhammad Turaki kaɗai ba da akayi asirin saboda shi, tun daga kan wanda tunanin yin asirin yazo kansa, da mai zuwa ya amso asirin, da masu zuwa suyi aikin asirin, duka sun shiga uku, rubuce yake a tafin hannunta sai taci uwar uban duk wanda yay sanadin shigarta wannan mawuyacin halin. "ya kike jin ciwon kan?". Amir ya tambaya with a look of concern and sympathy. Ta haɗiye abunda ba zata kira shi da yawu ba, sannan ta buɗe ido takalle shi. "ina jin kan kamar ba nawa ba, kamar ma ba na mutane ba". Ya sauke numfashi kamin yace,"sannu". ita kuma ta gyaɗa masa kai kawai. Nan Amir ya kama kan nata ya shiga karanto adu'oi yana tofa mata, tsawon mintuna yana yin hakan kamin ya tsaya. Sannan ya miƙe ya ɗauko ruwan faro da yake siyo mata yanzu ya buɗe sabo ya tofa adu'ao aciki ya bata tasha, kana ya rufe ya aje mata sauran a kusa da ita. Fillo ta rufe idonta ta jinginar da kanta ajikin bango, her breathing slows down, abu kamar almara sai taji ciwon kan daya addabeta tsawon sati biyu ya fara tafiya, har ma tana neman ta rasa shi gaba ɗaya. Hatta wannan nauyin da jikinta yay shima ya fara saki, to 10minutes sai taji komai yayi sauƙi kamar ba ita ba. Maijidda tayi sallama cikin ɗakin daidai da buɗe idon Fillo, ta ajiye ƙwaryar furar dake hannunta tana zama kusa da Fillon. "sannu". Tace da ita kamin ta juya gun Amir tace mishi,"sannu da zaman jinya Amir". Yay murmushi kaɗan sannan yace,"yauwa Kuluwa". Ya faɗa da zola dan bata son sunan, tace,"ni dai daga yau idan ka ƙara kirana da wannan sunan sai na rushe gwamnatin da ka kafa a zuciyar ƙawata". "yaushe kika yi wannan isar?". Yay tambayar yana kallon inda Fillo ta ke, wadda ta samu relief a yanzu, dan har idanuwanta sunyi tangarau, tana kallonsu ne kawai bata cewa komai. Maijidda tace,"ka dai bi a hankali kawai, ita masoyiyar taka ai tasan girman isar da nake da ita". "ah lallai ne mai girma Kuluwa". Suka yi gajeriyar dariya su duka. Amir yace da Fillo,"ya kike ji yanzu?". Idonta akan ledar magungunan dake can bayansa tace,"idan ka tashi tafiya ka tafi da waccan ledar ka jefar a bola". ya waro ido waje yace,"haka likitan ya karanta mana dama?". ta ɓata rai tace,"koma me ya karanta ni dai a zubar da su kawai, ai naji sauƙin". Maijidda tace,"ai sai ki bari idan Kaka tazo kyayi mata wannan bayanin". Sai kawai Fillo tayi narai-narai da idanuwa, fuskar nan a marairaice tana duban Amir kaɗan tace,"dan Allah Amir...wallah idan Kaka tazo ba zata bari a zubar ba, ni kuma naji sauƙi". Tana yin shiru ya ɗauki ledar ya saka a aljihunsa yana faɗin,"yanda kika ce ranki ya daɗe". Wayarsa tayi ƙara ya ɗauka, ƙaramar waya ce ba wata babba ba, yayi shiru yana sauraron maganar dake cikin wayar kamin yace,"tom shikenan Bandirawo ina kan hanya insha'Allah". ya ƙara yin shiru for seconds kan yace,"ahh mai jiki da sauƙi, yanzu haka ma ina wurinta". "tom zata ji insha'Allah, mun gode". Ya katse wayar ba tare daya dubi Fillo ba yace,"Bandirawo ne, yana yi miki sannu da jiki". Tace,"ina amsawa". Sannan ya miƙe yana roƙonta akan ta daure taci abinci, gyaɗa kawai tayi, ta yunƙura itama zata miƙe dan yi masa rakiya yace a'a ta koma ta zauna. Zuciyarta na harbawa da soyayyarsa ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, cikin sanyayyan muryarta da ciwo yaywa lahani tace,"na gode". Ƙwayar idonsa akanta da tsananin shauƙinta yace,"da me?". Still idonta kan yatsunta tace,"ni dai kawai na gode, Allah ya bada lada". Ya sauke numfashi yace,"amin". Sannan ya nufi ƙofa, ita kuma tana ce masa ya gaida su Inna. Bayan fitarsa Maijidda tace,"ke kam Fillo kin mo re da miji aur
🏠