nda ya dawo daga pharmacy siyo magunguna, Bobbo ya karɓa ya karanta sannan ya miƙawa Lamiɗo shi kuma yabi bayan likitan zuwa office ɗinsa.
asibiti dai sai ya zama kamar gidan biki, dan cikin lokaci ɗaya ya ɗinke da ƴan dubiya waɗanda suke zuwa gaisuwa a shaida musu ƴar Hayyo na kwance a asibiti to duk sai suyo asibitin, kace wata ƴar ƙusan ce ke kwance dan manyan mutane ma sai zuwa dubata suke, a shiga a fita a shiga a fita haka aka dinƙa yi.
irin karramammun mutanen da ke wajen in akace maka ƴan'uwan Hayyo ne sai mutum ya ƙaryata, zaka sha mamaki matuƙa in akace mutum me wannan gatan ne ya tsiyatar da rayuwarsa a iska.
ba'a sami sasaucin mutane a asibitin ba sai ƙarfe sha ɗaya da rabi, shima kuma saboda Dada ta koma gida ne, dan tana ta waya tana cewa a bar mutane su daina zuwa haka, Dottijo yace mata ai duk wanda aka hana sai yace a'a sai yazo ya nan asibitin yay mata ta'aziyya, sannan Dada taga tafiyar tata is the solution saboda Dr na ta complain akan hayaniyar da ake samu.
ƙarfe sha biyu dai-dai Fillo ta farka, motsin hannunta dake cikin na Turaki shi ya ankarar da shi, take yaja wani wawan ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin Alhamdulillah.
Fillo ta shiga buɗe idanuwanta a hankali ta sauke su akan Turaki da ya ƙura mata ido yana sakar mata murmushi me haɗe da damuwa.
tana jan numfashi a hankali tace,"ruwa". da ƙyar ya iya sakin hannunta yaje ya ɓare carton ɗin faro ya ɗauko ɗaya ya dawo, ya zuba a cup sannan ya ɗagota ya bata tasha, sai da ta shanye tass sannan ya ajiye cup ɗin.
ya sanya mata pillow daga bayanta ya jinginar da ita, ita kuma ta shiga bin ɗakin da kallo, daki daki kuma abinda ya faru da ita ya dinƙa dawo mata.
abinda zata iya tunawa shine Abbanta ya mutu, kuma har an kwana anyi masa wanka za'a fita da shi ai masa sallah a kaishi, to tunda aka fitar da gawar ba zata ce ta ƙara sanin inda kanta yake ba sai a yanzu da ta farka ta ganta a asibiti.
Turaki ya dinƙa kallonta yana jin kamar zai yi kuka, duk ta zabge tai wani muguwar rama, ƙasusuwanta kamar sayi magana, haka idonta yayo waje ya ƙara ƙwalele kace idon aljanu. ya kama karan hancinsa yana rumtse idonsa, hoton wancan ranar ya dinƙa haska masa, sanda aljanun Fillo suka tashi ta dinƙa bige bige, tun ana iya samu a riƙeta a danneta har ta kai ga hakan ya gagari kowa, sai ƙyaleta akayi tana ta murginawa akan duwatsun compound tana ta ife-ife, ƙarar ihu kuwa har na bakin titi zai iya cewa yaji, kuma sanda aka kira wani malamin ruƙiyya yazo me mamakon a sami sauƙi sai gida ya kacame da masu aljanu, ƙannan Hayyo da Yayyansa da jikoki wancan ta faɗi waccan ta kwasa da gudu waccan ta shaƙe na kusa da ita, haka akaita fama da su, ƙarshe sai da aka tara Malaman Ruƙiyya har biyar a gidan sannan aka sami lafiya, ashe aljanun nasu duk na gado ne na kan Kakarsu wadda ta haifi mahaifin su Hayyo, ita kuma Fillo har da waɗanda ta samu acikin dajin nan sanda da ta ɗauke asirin ɗakin Turaki.
tasha buƙar wuya sosai dan duk jikinta sai da ya farfashe, fuskarta tai ta jini saboda burgimar da tayi akan duwatsu compound ɗinsu. wan mahaifin su Hayyo da suke kira da Dottijo shi ya kira waya yace idan an kaishi to a tattaro a dawo nan gida aci gaba da zaman adu'a kuma, aka shaida masa halin da ake ciki na tashe-tashen aljanun, yace to suyi gaggawar tahowa nan ɗin saboda a samu ai masu magani tunda dama akwai babban malamin da suke da shi acan wanda ke kula da matsalar tasu tunma mahaifiyar tasu na da rai.
aiko dai Fillo tasha baƙar wuya, dan Malamin da yay mata ruƙiyya azababbe ne, bai ƙyale Fillo ba a wannan ranar sai da ya ƙona aljanun da suka shigeta na asirin da ta ɗauke, na gadon ne kawai masu shegen taurin kan bala'i da suka ƙi fita, suka ce su ai suna tare da ita ne saboda bata kariya, yinin ranar curr akanta akai ta fama, kuma sai ya zaman in an samu na waɗancan sun lafa da sun jiyo ihunta sai su ƙara tashi, ƙarshe ita sai ɗauketa akayi aka kaita can gidan Malamin, duk wanda yaga halin da take ciki kuwa sai yayi mata hawaye.
kuma hankula sai suka ƙara tashi a sanda aljanun nata suka lafa, dan tun ana tsammanin baccin wahala take har abin yazo yafi ƙarfin wannan tunanin, cikin gaggawa aka tafi da ita asibiti lokacin Ummi har ta saddaqar itama ta rasu, bama ita ɗaya ba da dama sun zaci ta mutu, sai da likita ya fito yake shaida musu tana raye tayi dogon suma ne sai dai ba'a san ranar farkawarta ba.
sai da Dottijo yayi magana sannan aka ragu a asibitin dan da kowa ya tare acan, yace a bar Kaka da su Adda Asma su zauna tare da ita, sai hadiman ɓangaren Jagarɗo su biyar da suke tare, aka barsu su goma suke kwana a wajenta, sai Turaki da yaƙi tafiya ya kafa ya tsare ko su Kakan baya bari su kwana a ɗakin sai shi, ya kwana da ita ya yini da ita baya ko matsawa daga kusa da ita.
Fillo ta ɗago ido ta kalli Turaki, cikin raunin murya dake ƙoƙarin ɓallewa da kuka tace,"da gaske mutuwa ta rabani da Abbana?".
Turaki bai iya ce mata komai ya ƙara damƙe hannun