NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 208 of 323

in komai ba, ace mutum kwanansa biyu yau amma shiru jiki babu sauƙin arziƙi, to ita dai idan jikarta bata sami lafiya yau ba to gobe ƙasar waje za'a fitar da ita ƙwararrun likita su dubata. Belɗo dai sai bata haƙuri yake yana tayi shiru kar likitocin suji, in suka ji ba zasu ji daɗi ba, tayi masa banza bata saurare shi ba har suka iso room ɗin da Fillo ke kwance. Ummi ta dakata daga ƙofar room ɗin bata shiga ba saboda nauyin sirikinta da take ji, tunda taga su Kaka a reception ta san shine zaune a wurinta. Turaki ya miƙe cikin sauri daga gefen gadon a sanda su Dada suka shiga room ɗin, ba shi yake cutar ba amma kallo ɗaya zaka masa ka hango bala'in ramar da yayi, ga damuwa kamar a lakuta a fuskarsa, ya matsa daga gefen gadon yana yi musu sannu da zuwa. Dada ta kallesa ta girgiza kai saboda tausayinsa taje,"sannu namijin ƙwarai, Allah ya baka ladan kulawa da matarka, ka kwantar da hankalinka zata sami lafiya insha'Allahu". ya kalli Fillo da ke ta bacci sannan yay ƙasa da kansa kamar zai yi kuka yace,"Allah ya amince". Kaka na kallonsa tace,"Me Babban suna ko zaka je gida kai wanka ka samu ka ɗan huta, rabonka da abinci ma tunda jiya da rana, dan Allah kaje kaci tunda likitan yace gobe da safe zasu sallame mu". da damuwa tsantsa a muryarsa yace,"Kaka ina so naga ta farka ne tukunna". Kaka ta gyaɗa kanta tace,"to Allah ya farkar da ita cikin ƙoshin lafiya". Dada ta zauna kan kujera tana fuskantar Fillo cike da jin tausayin yarinyar, sai adu'a take tayi mata a sanda ta kama hannunta ta riƙe, ta zaro wani diamond ring daga yatsanta ta saka ma Fillo, kuma sai ya zama kamar dama na Fillon ne, yay cif a yatsan nata. kamar zata yi kuka ta dubi Kaka tace,"se yaushe ne zata farka ni kam?". Kaka ta kalli Turaki shi kuma ya kalli agogon hannunsa sannan yace,"nan da awa ɗaya insha'Allahu". Dada ta dubi Hadimar dake ta shigo da kayan abinci tana ajiyewa tace,"Uwar wannan yarinya shina waje ko?". Hadimar tace,"ehh ranki ya daɗe". ta gyaɗa kai tare da jan tsaki tace,"sam matar Hayyo uwar banza ce, kije kice da ita ta shigo ta yiwa ƴarta adu'a, ni ban sani ba ko ƙaunar ƴar ne bata yi". sai kuma ta hau bambami yi take kamar zata haɗiye kowa, da yake mafaɗaciya ta kata'i, sai da ƙyar Belɗo ya tausheta tayi shiru yace in bata so Fillo ta tashi to taci gaba da ɗaga murya sannan aka samu ta rufe baki. Turaki ya kalla ƙofar ɗakin da Adda Asma ke shigowa, idonsa ya sauka akan gyalen Ummi da ya leƙo ta jikin ƙofar, ya juya ya ɗauki wayarsa dake kan drower ya fita cikin sanyi jiki kamar mara laka, ya sani in har yana cikin ɗakin Ummi ba zata taɓa shigowa ba, tun zuwansu asibitin sau ɗaya ta iya zama a ɗakin shima duk a takure kuma saboda shi, irin iyayen nanne masu bala'in jin kunyar sirikansu. tana ganin fitowarsa ta matsa gefe, ya durƙusa har ƙasa ya gaida ita, sai ta kasa amsawa ta bisa da kallo tana tsananin jin tausayinsa, kwana uku rak amma ya dawo kamar shine mara lafiyar da aka kwantar, idon nan yay jawur ya ƙanƙance tsabar baya samun bacci. ya katse shirun nata da cewa,"Ummi ki shiga daga ciki". tace,"a'a da ka koma kawai, ai ina jin ma yanzu zamu wuce". yace,"a'a Ummi ki shiga". sai ta ƙara kallonsa tace,"ya kamata ka huta haka". yay shiru bai iya cewa komai ba, kowa nata ce masa ya huta ya huta, ta ina zai iya hutawa alhalin Fulaninsa na cikin wannan halin. Ummi tace,"baka ce komai ba". yace,"tom Ummi". ya amsa ba dan yana jin zai iya aiwatar da abinda tace ɗin ba. Ummi na shiga room ɗin likita yazo, Turaki ya tsaya daga jikin window yana sauraron bayanin da Dr ɗin ke yi. "karku damu allurar bacci ce muka yi mata domin ta samu ta huta yanda ya kamata, ta yacca ba za'a samu damuwa ba idan ta farka, saboda gaskiya tana buƙatar hutu shisa ku ka kalla an ɗau tsayin wannan kwanakin bata farka ba, amma insha'Allah in the next 50minutes zata farka kuma lafiya lau da izinin Allah". duk suka amsa da amin, shi kuma ya ƙara da cewa,"sai dai akwai abinda ya kamata a kula da shi, kamar yanda na faɗa muku tunda farko ta samu heart failure, dan haka ya zama dole a kiyaye duk wani abu da zai iya zama damuwa a gareta, ai ƙoƙarin kiyaye ɓacin ranta sosai, ko stressing kanta da yawa kar ake bari tana yi, zan ƙara nanata muku duk wani abu da zai zamar mata damuwa ko ya sanyata ɓacin rai ko ya haifar mata da fushi to ya zama dole a kiyaye shi in har kuna sonta da ranta". da sauri Dada tace,"insha'Allahu za'a kiyaye hakan, baza ma mu bari ranta ya ɓaci ba balle kuma damuwa, ai ƴar gata ce gaba da baya, fatanmu dai Allah ya tashi kafaɗunta lafiya lafiya". Dr ya dubi ƴan dubiyan da ke ta shigowa ɗakin, da kuma hayaniyar waɗanda yake ji daga waje, ya sauke numfashi yace,"amm ya kamata a bata space dan wannan hayaniyar ma zata iya zamar mata matsala, da za'ai haƙuri ma ƴan dubiyan su dakata har zuwa ta farka". Dada ta ama masa"to shikenan yanzu kowa zai wuce kam". ya ɗauko wata takarda acikin file ɗinsa ya miƙawa Bobbo wa
🏠