NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 207 of 323

n ya kaiwa Dottijo, tun ɗazu ya aiko Manga kuma ba'a samu an kai masa ba, kuma ƙila zai sha tare da baƙi ne, yi maza du Allah". Hadimar ta wuce da sauri tabi dogon soron da zai kai ka wani babban fili kafin ka fita zuwa waje. Dada ta waiga tana kallon masu fitowa daga ɓangaren Hakimi, ta ƙwala kiran,"Munyoɗo". sai da ta kira sau biyu tukunna wata farar dattijuwa ta fito da sauri tana amsawa, tazo gabanta ta rissina tana faɗin,"Dada gani, lafiya kika fito ke ɗaya?, kuma kin tsaya ai a rana, me kike da buƙata?, ina Petel din?". tai maganar tana kamata ta matsar da ita daga cikin ranar. ta kalleta ta cikin glass ɗinta tace,"ina wannan shike, amnn mata na wurin Hayyo?". Munyoɗo tace,"wacce daga ciki Dada?". Dada ta ɗan ɓata fuska da muryar ƙorafi tace,"wannan yaro dai Allah ya jiƙan shi kawai, du yaje ya haɗo mata da yawa in ka tashi neman ɗaya sai kayi ta faman kwatance". tayi tsaki sai kuma tace,"wasu sun ƙara zuwa ne?". Munyoɗo tace,"ai Dada jiya duk sun gama zuwa, su bakwai ne yanzu sauran huɗun ance sun rasu, suna babban parlo yanzu haka". Dada ta girgiza kai alamar Allah ya kyauta sannan tace,"to wannan Balarabiyar za ki kirawo min". Munyoɗo tace,"tom Dada bari na duba". ta faɗa tana juyawa ta nufi ɓangaren da yake nanne na mahaifiyar Hayyo, ta shiga babban parlon da ya tara ƴan zaman makoki, ta dinƙa wuce su har ta ƙetara inda Ammi da Ummi suke zaune tace da Ummi,"Dada tana kiranki". Ummi ta amsa da to tana yunƙurawa ta miƙe, Ammi ma ta miƙe tana faɗin,"kin san Allah na sha'afa gaba ɗaya Dada tana nemana". tare suka fito gaba ɗaya, suka tadda har an ajiyewa Dada kujera ta zauna akai, suna zuwa ta ɗaga sandar hannunta ta bugawa Ammi, Ammi ta kauce tana faɗin,"kiyi haƙuri baƙi ne suka tsayar da ni". Dada ta harareta ta cikin glass bata ce mata komai ba, ta mayar da dubanta ga Ummi dake tsugune a gabanta tace mata,"kije ki sako mayafinki mu wuce asibiti, ance tun shekaranjiya baki koma wurin yarinyar nan ba, ban sani ba ko isashshen hankali ne baki da shi". Ummi ta miƙe cikin sanyi jiki ta wuce, Dada ta kalla Ammi tace,"kije ɓangaren Giɗaɗo kice da matarsa ta bayar da ferfesun kaji da nace ayi, na santa da ɗan banzan cin yajin jaraba, idan ta san yayi yaji da yawa to ta zubar da shi ba mayu ne zasu sha ba, ta ɗora sabo na mara lafiya ne". har Ammi ta wuce sai kuma ta ƙara tsayar da ita,"kice da Belɗo ya fito da mota zai kai ni asibiti, yace da Safara'u taje ta haɗa min kayana a kawo min yau can ina kwana". tana tafiya sai ga wata hadima daga bangaren Modibbo ta fito, tayo wurin Dada da sauri tana zubewa tare da cewa,"Allah juttin balɗe ma, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana Dada, da akwai abunda kike buƙata ne ayi miki cikin gaggawa?". Dada ta dubeta tace,"a'a bana buƙatar komai". Hadimar bata tashi ba ta cire takalmanta ta zauna akai ta shiga matsa ƙafafun Dada. lokacin maƙwabtansu suka shigo, da girmamawa matar ta tsuguna tana gaida Dada tare da ƙara yi mata ta'aziyya, Dadan ta amsa tana yi mata godiya sosai. matar tace mata tare da mijinta suke, Dada tace taje ta shigo da shi,ba jimawa sai gasu tare, suka gaisa da Dada wadda ke ta sanya masa albarka. "Dada wajen kuma da zafin rana da kin koma daga ciki". tace da shi,"zanje dubo yaron Hayyo ne, zafin mutuwar uban ya taɓata tana can asibiti kwance rai hannun Allah, Belɗo nake jira yanzu zai fito". daga nan suka yi mata sallama suka wuce. a ƙofar gida sanda su Ummi suka fito zasu tafi motar su Hajiya Ramla tayi parking, tun ranar ɗaya da suka zo suka koma sai yau suka dawo, Ummi ta ƙarasa wajensu tana yi musu barka da zuwa, su kuma suna ƙara yi mata ta'aziyya, Ummi tayi musu godiya sosai da sosai akan irin kyatatawarsu gare su. Hajiya Madina da damuwa a tare da ita tace da Ummi,"to ya jikin Fillon?". Ummi tace,"Alhamdulillahi da sauƙi, yanzu ma can zamu je, wataƙila ma dai zuwa dare su sallamota". Hajiya Madina ta kalla Hajiya Ramla tace,"to ko ni na bisu ne?". Hajiya Ramla tace,"ah ki dai bari mu shiga muyi gaisuwan, idan muka fito tafiya sai mu biya ta can ɗin ko". Hajiya Madina tace,"to shikenan". sai kuma tace da Ummi,"Me Babban suna yana nan ɗin ko yana can asibitin?". Ummi tace mata,"acan asibitin yake kwana ai, ya hana kansa natsuwa kwata-kwata, jiya ma nai ta fama da shi kan ya dawo gida ya huta yace min to, sai bayan su Lamiɗo sun dawo suke ce min yana can ɗin dai bai tafi ba, dan Allah Hajiya ku wuce da shi yau ɗin ya samu yaje ya huta shima". Hajiya Madina tayi ɗan jimm kamin tace,"to bari dai muga yanda za'ai, sai kun dawo". Ummi ta kira wani cikin jikokin gidan tace yaywa su Hajiya Ramla iso zuwa wajen Dadda wadda itace matar Maudo babban yayan su Hayyo hakimin yanzu kenan. direct Taraba State Specialist Hospital motar su Dada ta nufa, a reception su Ummi suka tadda Kaka ita da ƙannan Hayyo da suke uba ɗaya su biyar, tare suka wuce ward ɗin da aka kwantar da Fillo, suna tafe Dada nata ƙorafin asibitin basu iya aik
🏠