NOVEL SHARES -
e,"Baban Fillo ne yazo, kuma ashe ajali ne ya kawo shi".
Yusuf ya isa wajen da sauri, sai dai yana zuwa fuskar da ya gani ita ta matuƙar basa mamaki har ya razana yaja da baya, ya kalla Ummi ya kalla su Hamid yace,"waye wannan ɗin?".
babu wanda ya iya basa amsa acikinsu, ya dinƙa kallon Fillo dake aikin girgiza Hayyo tana faɗin dan Allah Abba ka tashi, ka tashi mun yafe maka karka mutu yanzu.
Yusuf ya zube a wajen hoton gawar Hayyo da hoton Kawunsa Muhammad da ya sani na haska masa a ido. a fili ya furta,"Kawu Muhammad".
sai kuma yasa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar Ammi, har ta ƙare ringing bata ɗaga ba sai daya kira lambar Aliyu yace ya kai mata.
murya a daƙile tace da shi,"ya akai?".
yace,"Ammi Kawu Muhammad".
tace,"me ya sami Kawu Muhammad ɗin?, ganinsa kayi?".
kamar yana gabanta yace,"Ammi ya mutu".
a matuƙar razane ta miƙe jiki na kyarma tace,"ya mutu?, aina ka gansa da zaka ce ya mutu?, yaushe rabonka da shi ma har da zaka ce ya mutu?, wa ya san inda yake?".
yace,"to ban sani ba Ammi ko idona ne yake gane min ba dai-dai ba, amma tabbas gani ga gawar Kawu Muhammad, zan tura address kizo yanzu ki gani ko shi ɗinne, amma na tabbata gawar Kawu Muhammad ne a gabana".
Ammi ta jefar da wayar Aliyu tayi cikin ɗaki da sauri ta ɗauko mayafi tace da shi,"muje muje Aliyu, duba wayarka Yusuf zai turo da address".
cikin mintunan da basu haura ashirin ba sai ga su Ammi sun ƙaraso gidan, ta shigo parlon duk a rikice tayi kan gawar da aka lulluɓeta a yanzu, ta kalla Ummi dasu Fillo da babu abinda ke tashi a parlon sai gunjin kukansu, ta kai hannunta na kyarma ta ɗaga zanin da aka rufe shi da shi, tana kallon fuskarsa ta saki zanin ta zabura taja da baya tana ambaton ƙalu innalillahi...
sai kuma ta fashe da kuka sosai tana faɗin,"ashe rabon ba zamu ƙara ganawa ba sai bayan ka mutu zanga gawarka Yaya".
ta kalli Ummi tace,"mijinki ne da gaske?".
Ummi da mamaki take kallonta ta ɗaga mata kai kawai, Ammi tace,"Yayana ne uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya, tunda ya zama ajalin iyayenmu shikenan kuma ya kama gabansa bai ƙara waiwayon kowa ba, rabona da shi tun Yusuf bai fi shekara goma sha ɗaya ba, yazo gidana sau ɗaya lokacin ko sauraronsa banyi ba".
tayi shiru tana bin gawar da kallo tana kuka sosai, "Allah ya jiƙanka Yaya yasa ka huta, Allah ya yafe maka zunubanka, ya haskakaka ƙabarinka, Allah ya sadaka da manzon Allah SAW".
nan da nan kuma sai ta ɗauki waya ta shiga kiran ƴan'uwanta waɗanda suke uba ɗaya, dama su biyu ne a wurin mahaifiyarsu daga shi sai ita, duk da irin fushin da aka ɗauka da Hayyo hasalima wasu sun manta da shi, amma kan kace mene wannan waɗanda ke zaune anan Gombe har sun zazzo.
saboda manyan yayyansa dake can taraba dole aka fasa kaisa a ranar akace a bari sai gobe, a washegari da safe kuwa ƙarfe takwas na safe gida ya cika maƙil da ƴan'uwan Hayyo maza da mata, lokacin har anyi masa wanka jira ake babban wansa yazo ai masa sallah.
lokacin da aka ɗauko gawar Hayyo za'a fita da ita a lokacinne mutane da dama da basu sami damar kuka ba suka saki nasu, saboda bala'in tausayin Fillo wacce ke ta kuka tana kiran a bar mata Abbanta dan Allah, sai da ƙyar Ammi ta iya riƙota Hajiya Madina ta ƙwace hannunta daga kan makarar da ta yiwa mugun riƙo, sannan ne aka samu aka fita da gawar Hayyo daga parlon, kuma lokacinne Fillo ta yanke jiki ta faɗi bayan ta ƙwalla wata razananniyar ƙara da ta masa a gidan gaba ɗaya.
aljanun da ba'a santa da su ba suka tashi....
*Vote, Comment and Share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*43*
*Taraba Satate, Wurkum district, Late Alhaji Aminu Barkinɗo Residence.*
tafkeken gida ne me irin ginin gidan sarauta, sai dai ginin irin na zamanin da ne bana yanzu ba, but an ɗan sabunta shi ba kamar yanda yake ainihinsa ba. ƙofar gidan na marigayi tsohon Hakimin Wurkum danƙare yake da jama'a kace ɗaurin auren wani babban mutum ake ko kuma za'a ƙara yin naɗin sarauta ne.
daga cikin rumfar tempol ɗin da akayi, Maudo ne zaune akan kujera yasha rawani yana amsar ta'aziyya daga bakunan mutane da dama, shine Babban ɗa a wurin marigayi Alhaji Aminu Barkinɗo, kuma shine wanda ya zauna a hannun mahaifiyar Hayyo a lokacin da ta na raye, domin shi tasa mahaifiyar ta rasu, kuma tun bayan rasuwar mahaifin nasu ya maye gurbin kujerar tasa har zuwa wannan ƙarni da muke ciki.
daga cikin gidan, ɗumbin mutane ne ƴan gaisuwa ke ta hada-hadar shige da fice a ƙaton tsarkargidan da yay kusan filoti guda, kana kallon yanda aka kakkasa ɓangare ɓangare zaka san family house ne.
wata farar tsohuwa tukuf ta fito daga wani ɗaki tana dogara sanda, sai da suka ƙaraso tsakiyan tsakargidan sannan ta tsaya tana kallon mai yi mata hidima wadda ke biye da ita a baya tun fitowarta, hannunta riƙe da ƙwaryar fura babba, ita ɗaya ta rage acikin matan Alhaji Aminu Barkinɗo, cikin su uku da ya aura ita ɗaya tayi tsawo rai haka.
cikin yaren fulatanci tace da Hadimar,"ki nemo Gaji ki basa fura