, Allah ya saka maka da mafificin alkhairin, ya baka masu kayatata maka fiye da yanda ka kyatata min, fiye da yanda ka dinga kare martabata da mutuncina, na san ba zan ƙara wani lokaci me tsayi ba, idan na mutu ka ɗauki wannan Atm ɗin dana baka ajiya kaje ka ciro miliyan hamsin ka bawa ƴata, hakkinta ne".
ya faɗa yana shafa fuskar Fillo, sannan yace,"ka nemi adalin alƙalin da zai raba maku gadonku babu zalunci, duk wata kadara dana mallaka taka ce Hamid na bar maka, na rubuta hakan a takarda ta nan cikin kayana, abinda kayi min ba zan taɓa iya biyanka ba Hamid, na gode, na gode, na gode Hamid, baka taɓa fushi dani ba, baka taɓa guduna ba saboda mugun halina, matana da ƴaƴana sun guje ni amma kai ɗaya namiji da Allah ya bani kana liƙe da ni, kana faɗa min gaskiya a lokacin da nake da dama amma naƙi saurarenka, Allah yasa ka gama da duniya lafiya, dan Allah yayin da babu ni ka zama uba a wurin ƴan'uwanka, karka bari zumuncinku ya yanke, kayi musu gatan da ni banyi musu ba, ka zama na gari Hamid, ka zama na gari, mutum baya dana sanin zama mutumin ƙwarai har mutuwarsa, amma idan ka zama mutumin da wasu suke kuka da kai zaka yi dana sani a sanda kazo mutuwa har bayan mutuwarka, Allah yasa ka gama da duniya lafiya".
Hamid ya kasa cewa komai yana dai riƙe da hannunsa yana hawaye, Hayyo na shaƙuwa ya kalla Fillo yace,"zan ƙara ruwan me sunana Umminta".
Fillo ta ɗago kansa ta kuma basa ruwan yasha, a lokacin sai da ya shanye jarkan guda, yana kallon Fillo yana murmushin ƙarfin hali yace,"ki tayani roƙon yafiyar mahaifiyarki, ki faɗa mata ina sonta, ina sonta fiye da yadda baki zai furta, dan Allah ta yafe min ko na na samu naga haske a ƙabarina".
yana faɗar hakan kansa ya langwaɓne gefe yana shaƙuwa sosai, ya dafe ƙirjinsa yana jin tsananin azaba na ratsa shi, magana yake so yayi amma shaƙuwa sam ta hana shi, can kuma sai ga jini yana fita daga bakinsa kamar zubar yawu, ya damƙo hannun Fillo da Hamid yace,"tawa tazo ƙarshe, ba zan ƙara ko da minti uku ba, mutuwa zanyi ƴaƴana, bana so na tafi na barku amma ban isa na hana mutuwa ta ɗaukeni ba, ba'a son raina zan rabu daku ba sai don mutuwa ta zama dole a gareni ko ba yanzu ba, idan na mutu ku nema min gafarar Allah, karku gushe face kuna me nemar min gafararsa a ko da yaushe, haƙiƙa ni ɗin me laifi ne a gare shi, mutuwa zanyi babu makawa, iyayena sun rasu tun ina saurayi, baƙin cikina ya zama ajalinsu, ku nemi dagina a ƙauyen Ngurore-Jabu under local government ɗin Karim-Lamiɗo, Wurkum district gidan Hakimin Wurkum, nanne gidanmu, Allah yayi muku albarka, dan Allah kuce da mahaifiyarku ta yafe min, la'ila ha'illahu muhammadurrasulillahi sallahu alaihi wassalam".
ɗif kamar ɗaukewar wuta haka numfashin Hayyo ya ɗauke, hannunsa ya saki ya faɗi daga riƙon da yaywa yaransa, Kaka ta fashe da kuka tace,"shikenan, Hayyo Allah ya jiƙanka yay maka rahama yasa can tafi nan".
Fillo ta ƙwala wata ƙara tana jijjiga shi,"Abba nah, Abba don Allah ka tashi, Abba karka mutu, Abba karka tafi ka barmu muna buƙatarka, wallahi mun yafe maka duk abinda kayi mana, dan Allah ka tashi Abba nah, muna sonka a yanda kake Abba ka tashi please".
Hamid dai kukansa a hankali yake yi, shi ɗaya yasan me yake ji a zuciyarsa, Kaka ta tashi ta fita dan kiran Ummi idan bata yi nisa ba, tana fitowa ƙofar parlo ta tarar da ita a tsaye tana goge hawaye da mayafinta, ta kalleta tace,"ya mutu ai".
wasu sabbin hawaye suka ƙara zubowa a fuskar Ummi, Kaka ma ta goge nata tace,"ki shigo ciki asan abin yi kafin dare yayi, anan za'ai jana'izarsa ko sai mun koma can?, in sai mun koma can dole sai gobe za'a kai shi tunda kinga daren yayi, in kuma nan ɗin ne to na shiga masallacin can na faɗa in yaso ko bayan magriba sai a kaishi".
kukan da Ummi ke ta riƙewa ya kubce mata, ta fashewa da kuka sosai ta shiga parlon da gudu ta tafi kan gawar Hayyo, wanda take kallonsa kamar zata yi masa magana ya amsa mata, ta kifa kanta a ƙirjinsa tana riƙe hannunsa, kukan da bata taɓa yi ba a duniyarta yazo mata, da ƙyar muryarta ta samu ta fito acikin kukan tana cewa,"na yafe maka, Allah ya yafe maka, Allah yasa ka huta, ubangiji ya lulluɓeka da rahamarsa".
lokaci ɗaya parlo ya karaɗe da kukan uwa da ƴaƴanta, zuciyoyin da su kaɗai suka san me suke ji, duk rashin kyan halin mutum yayin da akace babu shi mutuwa ta ɗauke shi sai mutuwarsa ta taɓa zuciya musamman makusantansa, ji suke yi inama zasu iya dawo da shi suci gaba da rayuwa tare da shi a yanda yake.
kukan da Fillo da Hamid ke ya ƙara tsinkar da zuciyar Ummi, kuka sosai babu me iya lallashin wani, lokacin kuma Dr Yusuf ya shigo parlon, da Yami ya fara cin karo, yana kallonta jiki a sanyaye yace,"lafiya Yami?, waye babu lafiya?, ba dai jikin Ummi bane ya tashi?".
tana goge hawaye tace da shi,"a'a ba ita bace, wanda ma aka kira ɗin kazo ka duba shi Allah ya karɓi abinsa".
ya kalla wurin da su Ummi suka kewaye gawar sannan ya kalla Yami yace,"ban gane ba Yami?, waye mutu?".
tac