tana kallonsa tace,"Hamma dana ganka sai naji farinciki ya kamani, amma da naga wannan masifar a tare da kai sai naji kamar in haɗiyi zuciya in mutu, saboda na san ba komai ya samin Ummina kukan da ta jima bata yi ba ba sai shi, dan haka gwara mu bar muku nan ɗin dan ba zamu ƙara zama da masifar da zata hanamu farinciki da jin daɗin rayuwa ba".
tana rufe bakinta Hamid ya ɗauketa da mari, kuma bai sauke hannunsa ba Ummi ta zabga masa marin shima.
"ƙarya tayi ba masifar bane shi da har zaka ɗaga hannu ka marar min yarinya, to wallahi ka kiyayeni kar kaja ɓacin rai yasa bakina ya zama silar lalacewarka a duniya, kuma na fasa tafiyar kaje ka gangaro shi kuzo ku fita a gidan nan tunda ba uban wani ya gina mana ba".
maganar Hayyo ta shiga kunnen Fillo a sanda yake cewa,"dan Allah dan Annabi ƴata ki yafe min, ki tausayawa halin da nake ciki, wallahi na san alhakinku ke bibiyata shisa na faɗa cikin wannan mawuyacin halin".
Ummi tace,"ai baka ga komai ba, kaɗan ma ka gani, kuma insha'Allahu nan gaba maganar ma sai ta gagareka, da izinin Allah sai kowa ya gujeka ya barka kai ɗaya a halin da yafi wannan muni".
Hayyo ya kulle idonsa yana ƙara roƙon su Ummi su yafe masa, tasa tazo ƙarshe su taimaka masa kar ya tafi lahira da alhakinsu, Fillo na kallonsa cikin ƙunci tana tuna voice ɗinsa da taji a wayar Turaki tace,"mu yafe maka kake cewa?, ka manta sanda kake saka Ummina a ɗaki ka kulle kayi ta dukanta?, ko kuma ka manta sanda kake bin ta har waje ka duketa a gaban mutane kana zaginta?, ko manta yacca ka azabtar damu da yunwa kayi?, ko kuma ka manta sheganta ni da kayi da har kake kirana da ƴarka?, to idan ka manta duk waɗannan abubuwan mu ba zamu manta ba, kuma tsakaninmu da sai Allah, da yardar Allah ba zaka mutu ba sai kaga shiga matsanancin halin da yafi wannan".
a tsawace Kaka tace da ita,"kul ɗinki Fillo, karki ƙara wani furuci anan, wannan lamarin tsakanin iyayenki ne, duk lalacewar uba uba ne shi, uba ba abin wasa bane ki san da wannan, kamar yanda kike ganin mahaifiyarki da mutunci ya zama dole shima ki gansa a mutumce muddin kina son gamawa da duniya lafiya, ke ba dan shi ba ai da baki zo wannan duniyar ba, ki iya bakinki akansa kafin duniya tayi watangaririya da ke".
Fillo tasa kuka tana faɗawa jikin Ummi tace,"ni wannan ba Babana bane, shi da ya sheganta ni a duniya ta ya za'ai ya zama ubana, mutumin da ya kasa bani ilimi da tarbiyya shi ne zai zama mahaifina?, ni dai ba Babana ba ne kuma ba zan taɓa yafe masa abunda yay mana ba".
tarin da Hayyo ya fara babu qaqaautawa yasa Fillo haɗiye sauran maganganunta tayi kansa da sauri, Kaka tace da Hamid ya tura shi su shiga daga ciki, Ummi na tsaye tana jin zuciyarta nayi mata wani iri tabi bayansu da kallo.
cikin ƙanƙanan lokaci dai Hayyo ya fita a hayyacinsa, tari kawai yake yana a basa ruwa ya sha, Fillo ta ɓare jarkan faro jikinta sai rawa yake yi ta zuba a kofi ta tallafi kansa ta basa ya sha, Kaka ta ɗauka lambar Dr Yusuf ta kirasa a waya yace gashi nan zuwa nan bada jimawa ba.
cikin mintunan da basu wuce biyar ba Hayyo yasha ruwa yafi roba huɗu, da yasha zai kuma cewa a ƙara masa, kuma duk Fillo ce take basa, idan ta kai kofin bakinsa sai ya haɗa harda hannunta ya kama tukunna yake shan ruwan, hawayenta kuwa dake zuba ajikinsa jinsu yake kamar wuta, in ace ya san haka Ƴaƴa suke da tausayi da jin ƙai da bai wulaƙanta ƴaƴan da Allah yabasa ba balle ya wofuntar da su, bai san Ƴaƴa rahama bane sai da ya shiga wannan halin, lokacin da babu macen da zata kula da shi, haka kuma babu ƴaƴan da zasu zauna su basa kulawa, in ace babu Hamid bai san kuma ya zai yi ba, wataƙila da tuni ya mutu ya ruɓe ba tare da kowa ya sani ba.
sai a yanzu da tasa tazo ƙarshe yaji sonsu da ƙaunarsu matuƙa na bin jinin jikinsa, sai yanzu yake jin ina ma ace baya zata dawo da ya kyautatawa iyalinsa, babu abinda yake buƙata a yanzu irin ubangiji ya basa aron lokaci, sannan ya ara masa lafiya ko ta ɗan kaɗan ɗin lokaci ne dan ya faranta ran iyalinsa, ya gyara halinsa, ya gyara lahirarsa, to amma ya san ƙarshensa yazo, ba zai ƙara samun wata dama ba a wannan duniyar balle kuma lokaci.
yana ta kallon Fillo yana kuka sosai yace,"na karɓi sadakin aurenki tuntuni, na san da cewa hakkinki ne, dole na baki hakkinki, amma saboda son zuciya nawa ban nemeki ba balle na baki, sai na gina kaina da kuɗin motar dana siyar, ban ko fara morarsu ba Allah ya jarabceni da shiga wannan mawuyacin halin, dan Allah ki yafe min kar in mutu da hakkinki akaina".
ya faɗa yana kuka sosai. "na san ƙwarai na zalunceku, ba'a taɓa mugun mutum irina ba da ya ƙuntata rayuwar iyalinsa, ban baku ilimi ba balle na baku tarbiya, hasalima duk naƙi karɓarku a matsayin ƴaƴan dana haifa, alhakinku kaɗai ba zai barni in ƙare da duniya lafiya ba, dan Allah ku yafe min ko na sami sassuaci a ƙabarina, kuce kun yafe min ko naga da kyau a ranar gobe".
ya kamo hannun Hamid yace,"haƙiƙa banda tamkarka ɗana, Allah ubangiji yay maka albarka