NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 203 of 323

ba. "ya akai kazo nan Hamid?, wa ya faɗa maka inda muke?". tambayoyin da tai masa kenan, kuma kamin ya bata amsa idonta ya sauka akan halittar da duk lalacewar da tayi ba zata kasa ganeta ba a kallo ɗaya, tai saurin ɗauke ƙwayar idonta daga kan mutumin da take jin ta tsane shi tsana mafi muni. Hamid ya buɗe baki zai yi magana tayi saurin ɗaga masa hannu cikin fusata, ta kulle idonta tana huci na tsawon daƙiƙa ɗaya, ta buɗe su a sanda ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jawur, wannan damuwar da take tare da ita na tsawon shekaru ta taso tun daga can ƙuryar zuciyarta ta mamaye saman fuskarta. da tsananin ɓacin rai a muryarta tace da Hamid,"tunanina duk sanda zan ganka zan zama ina me farin ciki ne". ta faɗa tana ƙara ɗaga muryarta da faɗin,"me yasa kazo min da wannan abin cikin gida?, to idan baka sani ba ka sani, bana so kuma bana ƙaunar sake haɗa ido da azzalumin mahaifinka har in bar duniya, dan haka tun ina shaida kai ɗana ne ka fitar da shi daga gidan nan". tai maganar cikin zafin rai tana yi masa nuni da gate, Hamid ya dubi mahaifinsa da tausayi wanda ke ta kokawa da wheelchair yana so ya sauko, ya koma ya kalla Ummi yace,"dan Allah Ummi...". bata barsa ya ƙarasa ba ta doka masa tsawa. "Hamid ka fita da shi na faɗa maka, ka fita da shi tun ina iya kallonka ina shaida kai ɗana ne, Hamid ina me rantse maka in baka fitar da wannan matsiyacin mutumin daga gidan nan ba zan tsine maka". Kaka tayi saurin shiga maganarta da cewa,"kul, kul Halimatu, shi me yayi miki da zaki nemi ki sauke fushinki akansa". Ummi tace,"wallahi tallahi in har don inci gaba da kallon wannan azzalumin mutumin a inda nake ne to gwara in yafe Hamid ko kuma in tsine masa muddin bai fitar da shi daga gidan nan ba, na tsani mutumin nan na tsani ganinsa, inata roƙon Allah kar ya ƙara haɗani ko da ace da inuwarsa ne shine Hamid saboda baya ƙaunarta zai ɗauko shi ya kawo shi inda nake salon zuciyata ta buga". Yami tace,"kiyi haƙuri Ummin Fillo, ki tsaya ki saurare shi har yanzu shi ɗin mijinki ne, kuma karki manta shi uban ƴaƴanki ne, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, to kuma ina laifin wanda ya gane kurensa yazo neman yafiyarka". ta girgiza da kanta cike da takaici da ƙunar rai,"Yami baki san waye wannan mutumin ba, wannan da kike ganinsa azzalumi ne, mugu ne, macuci, dan Allah ku fitar da shi daga gidan nan tun ban faɗi na mutu ba". sai kawai ta fashe da kuka me cin rai, tana jin wani abu me ɗaci na taso mata, tana jin kamar ta shiga ciki ta rarumo duk abinda ta gani tazo taita rotsawa Hayyo. faɗowar Hayyo daga kan wheelchair yasa hankalinsu ya kai kansa, Hamid ya tafi da sauri ya ɗaga kujerar da ta danne shi, jikin Hayyo duk karkarwa yake, yana jan jikinsa a ƙasa yana so ya ƙarasa gaban Ummi, Hamid ya fara hawaye ya ɗagosa ya mayar da shi kan kujerar, sannan ya turasa ya kaisa gaban Ummi. gwanin ban tausayi hawaye ke sauka akan fuskar Hayyo ya haɗe hannayensa alamar roƙo, bala'in nadama da danasani shimfiɗe a fuskarsa, cikin ƙinƙina mesa zuciyar mutum ta tsinke yace,"dan darajan Allah ki yafe min Halima, ki tausayawa halin da nake ji, ke kaɗai kika rage ki yafe min acikin waɗanda suke raye, kuma muddin baki yafe min ba nasan ba zan gama da duniya lafiya ba, domin nasan na aikata miki abubuwan da Allah ba zai barni ba, dan Allah ki yafen ko na samu sassaucin bala'in da nake ji a tare da ni". Ummi na kallonsa da tsantsar tsana tace,"kai yanzu Hayyo har kana da idon da zaka kalleni ka buɗi baki kace in yafe maka?, yaushe kasan Allah da yau kake roƙon wani da shi?, to bari kaji na faɗa maka, banda idon da zan dubi halin da kake ciki in tausaya maka balle na yafe maka, ka cire batun yafiya tsakanina da kai dan ko da ace yafiyata ta rage maka shiga aljannah Hayyo ba zan yafe maka ba". Kaka, Yami da Hamid sukai ta roƙon Ummi akan ta yafe masa, amma sam taƙi, ƙarshe ma sai ciki ta shiga ta ɗauko mayafi ta fito tana kallon kowa tace,"in har ba zaku ɓadda shi daga inda nake ba to ni zan bar muku gidan". sannan ta kalli Hamid tace,"kai kuma ko a mafarki ka ganni karka nuna ni a matsayin mahaifiyarka, tunda kaima baka tausayina". tana zuwa bakin gate Fillo na turo ƙofa ta shigo, niƙab ɗinta a hannu tana yamutsa fuska alamun ta gaji, farat ɗaya hankalinta ya tashi ganin Umminta na kuka, gabanta ya faɗi tana tunanin me zaisa mahaifiyarta kuka a yanzu kuma?, ai tayi zaton zubar hawayenta ya ƙare kuma tunda har ta rabu da Hayyo. sai ta ƙanƙance ido tana bin kowa da kallo, ta tsayar da idonta bayan Hamid da bata ga fuskarsa ba, zuciyarta bata gama tunanin ko waye ba ya juyo, ta ware ido tana faɗin,"Hammah". ta faɗa murmushi na ƙwacewa a fuskarta, harta ɗaga ƙafa zata wuce wurinsa sai kuma idonta ya sauka akan mahaifinta dake kallonta yana murmushi da hawaye, alamun na yaji daɗin ganinta, lokaci ɗaya ta haɗe rai ta ɗauke idonta daga kansa. ta kalla Ummi dake ƙoƙarin raɓata ta wuce, ta kama hannunta zasu fita maganar Hamid ta tsayar da ita. ta juyo
🏠