NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 202 of 323

a idanuwa na?, Hamid dama kana raye baka taɓa nemana ba?". Hamid ya sauke numfashi yace,"kiyi haƙuri Kaka Allah ne bai nufa ba, amma wallahi kina raina, ta ya zan manta dake bayan kece silar zuwan mahaifiyata duniya". Kaka ta share hawayen farin ciki tana bin motar da kallo kamin tace,"to ya akai kazo nan Hamid?, kar dai wani abu ne ya faru mara daɗi?, wannan motar kuma ta waye?". Hamid yace,"Kaka ai ban manta da kina aiki a gidan sarki ba, na faɗa miki tsawon shekarun nan Allah ne kawai bai nufa ba sai yanzun". tace,"dan dai kaga bana tare da abu me muhimmanci a wurinka ne shisa ka kasa nemana". yaga tana kallonsa tana ƙara bin motar da kallo yace,"mota ta ce, ba zai yiwu mu shiga daga cikin gidan ba ne?". Kaka na kallonsa tace,"zai yiwu mana Hamid, ai shiga cikin gida ma dole, gidanku fa kazo taho muje". ta faɗa tana juyawa ya dakatar da ita,"Kaka mota ba zata shiga ciki ba ne?". tace,"to sai dai ka duba tunda mu ba mota garemu ba, tun zuwanmu dai ta wannan ƴar ƙofa muke shiga". ya ƙarasa ya duba yaga gate din yaga ba me zugewa ba ne, hakan yasa yace mata,"Kaka to bari na fito da shi". tace,"waye?". yay ɗan jimm damuwa na bayyana a fuskarsa sannan yace,"tare da Abba muke, ba zai iya tafiya ba sai na taimaka masa". idanun Kaka a waje tace,"kana nufin Babanka Hayyo?". ya ɗaga mata kai,"ehh Kaka". da mamaki sosai tace,"to me ya sami ƙafar tasa da ba zai iya takawa ba, ko wani mulkakken ya zama?". ya sauke numfashi yace,"jarabawar ubangiji". Kaka ta taɓe baki tace,"Alhaki dai yake bibiyarsa". bai ce komai ba ya ƙarasa mota ya buɗe booth ya ɗauko wheelchair sannan ya buɗe bayan ya taimakawa Hayyo ya fito ya ɗorasa akan kujerar, tun fito da shi Kaka tayi masa kallo ɗaya taji mugun tsoro ya kamata kamin bala'in tausayinsa ya biyo baya, indai gani take yi da kyau ya rame kamar me cutar ƙanjamau, mutumin da yake jayent son kowa ƙin wanda ya rasa, mutumin da bama a gane girmansa ko ada amma yanzu girma ya bayyana ajikinsa sosai kace me shekaru ɗari. Hamid ya turo shi suka ƙaraso inda Kaka ke tsaye cike da tsoron duniya, hoton abubuwan da suka faru a baya suna ta haska mata a ido, ita dai banda Hamid ya faɗa mata yace Abbansa sai ta rantse tace ƙarya ne ba shi bane, dan gaba ɗaya ya fita daga kamanninsa tsabar wahala, kamar ba wannan ƙaƙƙarfan namijin da ke zage dukkan ƙarfinsa ya zane mata ƴarta ba. ta girgiza kai tana ƙara jin tsoro na al'amarin sakayyar wanda aka zalunta, a hankali tace da shi,"Hayyo". ya ɗago da wuyansa da ƙyar wanda ya laƙwashe. ya kalleta ya buɗe baki yace,"nannnnaaammm Daddddda". ya faɗa cikin ƙinƙinar da sai kayi da gaske zaka gane, kuma cikin murya kamar ta masu koyon magana. kawai sai Kaka ta fashe da kuka sosai tana ambaton,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". ta ƙara kallonsa tace,"Hayyo kai ne ka koma haka?". ta tambayesa tana tuna zaƙin maganarsa ada, wanda daɗin amon muryarsa na ɗaya daga cikin abinda yake jan hankalin mata garesa, dan ƙarya ne Hayyo yayi magana kana wajen baka ce kaji daɗin muryarsa ba. hawaye ya sakko a idonsa yace,"Kakkkkaaa dddddaaa Allllahhhh kikkki yaaafeeee miiiimmmmnn, dddda Allllahhhh kiiii neeemmmooo minnn Haliiimaaaattttuu". sai da aka ɗauki cikakken minti ɗaya da ƴan kai sannan ya iya faɗar kalmar da za'a faɗeta cikin sakanni biyu, yana maganar bakinsa na rawa, haƙoransa na daddatsewa akan harshensa. Hamid yasa handky yana goge masa uban yawun da ya dalala ajikinsa ya ɓata gaban babbar rigarsa kamar an sheƙa masa ruwa. ƙafafunsa suka shiga rawa akan wheelchair ɗin ya kamo hannun Hamid yana faɗa masa,"zaazzzzzannnn saukkkkkaaaa innnneeee miiii yaaaaaffiyyarrrr Dddddaaaada". kaman yanda Kaka ke hawaye haka ma Yami, saboda ƙarya ne ace kaga halin da Hayyo ke ciki baka zubar da hawaye ba. Hamid na kallon Kaka yace,"wai yana so zai sauko ya nemi yafiyarki". tace,"Hayyo ba sai ka sauko ba na yafe maka, ni baka min komai ba dama". ta dubi Hamid tace,"mu shiga". tai gaba suka biyo bayanta, Yami ta tura ƙofar. suna nufar entrance na parlon gidan Ummi ta fito, Kaka ta fara gani wadda ke aikin goge hawaye, bama ta lura da sauran ba, tai saurin ƙarasowa wajenta tana faɗin,"lafiya Dada?, na fito naga ba kya parlon me ya faru?". Kaka bata iya magana ba dan har yanzu a girgiza take, kuma kamin tayi mata nuni dasu Hayyo, Ummi taji hannayen mutum a ƙafafunta da ɗigar ruwan hawaye. ta kai idonta kan Hamid dake zube a gabanta ya riƙe ƙafafunta, ba fuskarsa ta kalla ba, saman kansa kawai ta kalla ta shaida ɗanta, sai taji wani abu ya tsarga mata, ta kulle ido tana jin taruwar ruwan hawaye aciki. "Hamid". ta kira sunansa da amon sautin da ya tafi ya taɓa har zuciyar Hayyo. "me kake nema a ƙafafuna Hamid?, laifin me kayi min?, tashi tsaye na ganka ɗana". Hamid ya miƙe yana hawaye, Ummi ta rungumosa jikinta suna kuka tare, wucewar daƙiƙa biyu Hamid ya zare jikinsa daga nata yana bin mahaifiyar tasa da kallo, wadda yaga ta ƙara kyau da girma kamar ba ita
🏠